30/03/2026
Allah Ya Yiwa Alaramma Malam Ibrahim Dan Jariri Rasuwa A Daran Jiya.
Tuni Aka Yi Jana'izarsa Yau Litinin Karfe 9:30 Nasafe 30 - 3 - 2026 Zuwa Makabartar Kofar Mazugal.
Malam Ya Rayu Cikin Karantar Da Alqur'ani Da Hidima Ga Sharifai.
Allah Ya Jikansa Da Rahma.
20/03/2026
Hotunan Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero A Wajen Sallar Idin Ƙaramar Sallar Bana.
03/03/2026
DA DUMI-DUMI: Majalisar dokokin jihar Kano ta rantsar da sabbin mambobinta biyu
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranci rantsar da sabbin ’yan majalisa biyu a ranar Talata.
Sabbin mambobin su ne Sa’adu Aminu Sa’adu mai wakiltar Ungogo da Nabil Aliyu Sarki Daneji mai wakiltar Kano Municipal, wadanda s**a yi nasara a zabukan cike gurbi da Hukumar ta gudanar.
Dukkansu sun yi nasara a karkashin jam’iyyar APC, inda s**a maye gurbin iyayensu da s**a rasu a watan Disambar bara.
21/02/2026
Yanzu Haka Wata Babbar Mota Ta Buge Wani Dan Sanda A Gaban Kurna Babban Layi Daidai Division Din Dragon Dake Kurna Kafin Aje Gidan Man Aliko.
Dan Sandan Yana Tafiya A Mashin Kirar Jincheng.
Motar Tabi Takansa Ko Motsaya Baiyi Ba.
Yanzu Haka Gawarsa Tana Division Din Na Dragon.
Mai Motar Ya Kawo Kansa Bayan Ya Faka Motar.
21/02/2026
Wasu Daga Cikin Jami'an Zabe Na Jihar Kano Lokacin Da Suke Yin Barci Saboda Rashin Ma Su Jefa Kuri'a.
11/01/2026
Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un 🥲😥
Al'ummar Musulmi na alhinin rasuwar babban malamin Muslunci a unguwar Arzai da ke Kofar Mazugal a birnin Kano Malam Mansur Manzo Arzai.
Malam Mansur ya rasu ne a wannan dare na Lahadi, Allah ya jiƙansa, ya yi masa rahama.
26/09/2025
SHUGABAN DARIKAR KADIRIYYA NIGERIA KHALIFA SHEIKH IBRAHIM ISA ABDULLAHI MAKWARARI DA TAWAGAR MAHAMMADAWA SUNMIKA TAKARDAR KORAFI GA MAIGIRMA GWAMNAN JAHAR KANO TA HANNUN SAKATAREN GWAMNATIN JAHAR KANO M. UMAR FAROUK INDA S**A NUNA RASHIN AMINCE WARSU DA TABARGAZAR DA LAWAN TRAMOL YAKEYI SAKATAREN GWAMNATIN YA ALKAWARTA CEWAR BAZASUYI KASA A GWIWABA WAJEN DAUKAR MATAKIN SHARIA.
25/09/2025
Buɗe mana duk littafin da kake takama da shi, nuna mana inda aka kawo kalmar Tunkiya ko Arne lokacin da ake maganar haihuwar Annabi Sallallahu alaihi wasallama.
Buɗe mana duk littafin da kake taƙama da shi nuna inda aka ce yana da Kwarkwata.
Buɗe duk littafin da ka yarda da shi ka nuna mana inda aka ce yana kwanciya akan cinyar wata mata.
-Muhammad Inuwa Muhammad-
24/09/2025
Matasa sun fara zanga_zangar lumana da Yin Zaman Dabaro a Kofar God and Gwamatin Kano Domin Nuna fushinSu Gami da Kalaman Batancin da Cin-Kashin da Lawan Trump Yakeyi ga Shugaban Halitta.
19/09/2025
IDAN DA ANSAMI WANDA ZAI IYA ZAUNAR DANI A GIDA YA BANI ABUNCI ME ZE SAKA IN FITO TALLACE TALLACE KAN HANYA.
Wata dattijuwa da muka taba kawo hoton ta a nan kafar sama da shekara guda tace har yanzu tana nan tana tallan ashana da biro wanda ake bata su bashi idan ta sayar ta sami abunda zata ci. Bayan tambaya da mukai mata cewa shin idan aka sami wanda zai ajiye miki abuncin safe, rana da dare zaki fito talla sai tace a'a don me zan fito bayan abuncin nake saya da kudin idan na samu kuma sai na wuni ban sami N300 ba ina fatan Allah zai sa wani yaji kaina kamar yadda kake kula dani idan kazo wucewa shikuma ya zaunar dani a gida a ajiye mun kwanon abunci uku sai na hakura da fita, kwana nawa ne ya rage mun a duniyar.
Inji Dattijuya dake tallan ashana da biro a Junction na Lagos Street, Kano kusa da Glo office.
~Bluelens Multimedia.