13/03/2026
Ramadan Day 24.
Welcome to the Office of the Vice Chairman, Danja LGA. Under the dynamic leadership of Hon.
Ashiru Wada Nahuce, this office is dedicated to local development, accountability, and unity.
29th April 2025 - To date
13/03/2026
Ramadan Day 24.
18/02/2026
🌙✨ RAMADAN MUBARAK ✨🌙
Ina taya daukacin al’ummar Musulmi musamman ma al’ummar Danja Local Government Area murnar shigowar watan Ramadan mai alfarma.
Ramadan wata ne na ibada, hakuri, taimakon juna da neman kusanci ga Allah (SWT). Mu yi anfani da wannan wata wajen ƙara ibada, sada zumunci da taimakon marasa galihu.
Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sa mu gama lafiya tare da samun lada mai yawa. 🤲
Ramadan Kareem 🌙
Hon Ashiru Nahuce
Vice Chairman,
Danja Local Government Area
28/11/2025
28/11/2025
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
On behalf of myself, my family, and the entire people of Danja Local Government, I extend our deepest condolences over the passing of our revered scholar, the great leader of knowledge and spirituality, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
The loss of Sheikh Dahiru is a heavy one, not only to Bauchi or Northern Nigeria, but to the entire Muslim Ummah. He was a father to all—an embodiment of humility, piety, deep knowledge, and unwavering commitment to the teachings of Islam.
His lifelong dedication to Tafsir, Qur’anic education, peacebuilding, and moral guidance has shaped generations and left a legacy that will remain forever in our hearts.
We pray that Allah (SWT) forgives his shortcomings, fills his grave with light, and grants him the highest rank in Aljannatul Firdaus.
May Allah comfort his family, his students, and the millions who looked up to him for guidance.
Nigeria has lost a pillar, but his legacy will continue to guide us.
May Allah have mercy on him. Ameen.
Signed:
Hon. Ashiru Wada Nahuce
Vice Chairman, Danja Local Government
On this blessed day of Jumu’ah, I extend my warmest greetings and heartfelt prayers to all the good people of Danja Local Government.
May Allah (SWT) accept our prayers, forgive our shortcomings, and bless our homes, families, and community with peace, unity, and progress.
As we welcome our amiable Governor on his visit to Danja today, we pray:
Ya Allah, grant His Excellency a safe arrival and a safe return.
Bless his mission, guide his decisions, and make his visit a source of development and goodness for our people.
Protect him, strengthen him, and surround him with Your divine mercy and wisdom.
May Allah continue to uplift Danja, bless our leaders, empower our youths, and open doors of prosperity for all.
Jumu’at Mubarak!
Signed:
Hon. Ashiru Wada Nahuce
Vice Chairman, Danja Local Government
28/11/2025
SPECIAL ANNOUNCEMENT
DANJA LOCAL GOVERNMENT AREA
Muna farin cikin sanar da al’ummar Danja cewa yau Jumma’a, 28 ga Nuwamba 2025, za mu karɓi BAKON MU NA MUSAMMAN — Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda wanda zai kawo ziyarar aiki (working visit) zuwa Danja Local Government Area.
Za a gudanar da taron maraba a Danja Local Government Secretariat da misalin karfe 5:00 na yamma.
Ziyarar ta ƙunshi muhimman al’amura na cigaba, walwalar jama’a, da inganta rayuwar al’umma. Muna kira ga kowa da kowa da ya fito cikin kwanciyar hankali domin tarbar wannan babban bako.
Allah Ya sanya albarka cikin wannan ziyara, Ya kuma tabbatar da ci gaban yankin Danja.
Hon Ashiru Nahuce
Vice Chairman, Danja Local Government Area
12/11/2025
Safe Journey The Workalic ALGON and the Executive Chairman Danja Local Government Area Hon. Rabo Tambaya Danja.
Long Live Danja Local Government Area.
Long Live Katsina State.
Long Live Federal Republic of Nigeria.
🕌 JUMU’AT MUBARAK
Alhamdulillah! Ina mika sakon fatan alheri da Jumu’at Mubarak ga daukacin jama’ar Karamar Hukumar Danja da kewayenta.
A wannan rana mai albarka, ina roƙon Allah (SWT) Ya karɓi ibadunmu, Ya yafe mana kura-kuranmu, Ya kuma ci gaba da azurta mu da zaman lafiya, hadin kai da cigaba a Danja da Jihar Katsina baki ɗaya.
Ina godiya ga jama’armu bisa hadin kai da goyon bayan da kuke bani wajen aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma.
Ku ci gaba da kasancewa ‘yan uwa na gari, masu kishin kasa da kishin addini.
Jumu’at Mubarak!
Allah Ya albarkace mu duka.
Hon Ashiru Nahuce
Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Danja
7 ga watan Nuwamba 2025
31/10/2025
Happy Birthday.
A matsayina na Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja, ina taya Sanata Abu Ibrahim murnar cika shekaru 80 da haihuwa.
Sanata Abu Ibrahim mutum ne mai kishin ƙasa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare dimokuraɗiyya da cigaban Najeriya, musamman jihar mu ta Katsina.
Mun yaba da irin goyon baya, hikima da shawarwarin da yake bayarwa ga shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma irin rawar da ya taka wajen haɗa kan ‘yan siyasa don cigaban ƙasa.
A wannan lokaci mai albarka, muna roƙon Allah Ya ƙara masa lafiya, nisan kwana da ƙarfin guiwa domin ci gaba da hidimar al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Allah Ya ja masa shekaru cikin alheri.
Hon Ashiru Nahuce
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja
31 Oktoba, 2025
JUMU’AT KAREEM
Alhamdulillah, mun sake kai ga wannan babbar rana mai albarka ta Jumu’a, rana da take cike da rahama, gafara da albarkar Allah (SWT). Rana ce da ake amsar addu’a, da ake neman kusanci da Ubangiji, da kuma nazari kan kyawawan ayyukan da ke gina rayuwa da al’umma.
A wannan rana mai muhimmanci, ina kira ga ‘yan uwana maza da mata, matasa da dattawa na Ƙaramar Hukumar Danja, mu ƙara daidaita zukatanmu, mu rungumi zaman lafiya da juna, mu ƙarfafa haɗin kai da gaskiya a tsakaninmu.
Allah Ya sanya soyayya, fahimta da zumunci su mamaye zukatanmu, Ya kuma ba mu ikon yin abubuwan da za su kawo ci gaba da ɗaukaka ga al’ummarmu.
Ina roƙon Allah (SWT) Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kurakuranmu, Ya azurta mu da lafiya, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a cikin Danja Local Government da ma jihar Katsina baki ɗaya.
Ya sa Danja ta ci gaba da kasancewa gari na kwanciyar hankali, natsuwa, da haÉ—in kai.
A matsayina na Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja, ina mika sakon fatan alheri da albarka ga kowane ɗan asalin Danja — ko kana gida, kasuwa, gonaki, makaranta, ko wajen aiki — Allah Ya sa albarkar wannan Jumu’a ta zame maka hanyar samun rahama, nasara, da ɗaukaka a rayuwa.
Mu ci gaba da yi wa juna addu’a, mu taimaki marasa ƙarfi, mu yi hakuri da juna, mu kasance al’umma ta gaskiya da tsoron Allah.
Jumu’a Mubarak!
Da fatan alheri daga gare ni,
Hon Ashiru Nahuce
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja
31 ga watan Oktoba, 2025
Jumu’at Kareem
A yau Jumma’a, rana ce ta albarka, rana ce da ake amsa addu’o’i. Ina mika sakon fatan alheri ga jama’ar Karamar Hukumar Danja baki ɗaya. Allah Ya sa wannan Jumu’a ta zama ta rahama, lafiya, da albarka a gare mu duka.
Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya karɓi ibadunmu, Ya yafe mana kura-kuranmu, Ya ba mu zaman lafiya, ɗorewar haɗin kai, da ci gaban yankinmu.
Mu ci gaba da yin addu’a domin ƙasarmu Najeriya da Jihar Katsina, tare da nuna ƙauna, zumunci, da taimakon juna.
Allah Ya albarkaci Jumu’armu.
Allah Ya albarkaci Karamar Hukumar Danja.
Allah Ya albarkaci Jihar Katsina da Najeriya baki É—aya.
Hon Ashiru Nahuce
Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Danja
17 ga watan Oktoba, 2025
15/10/2025
KATSINA STATE PRIMARY HEALTH CARE AGENCY (KSPHCA)
Ina sanar da daukacin jama’ar Karamar Hukumar Danja cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta bude damar daukar ma’aikata a karkashin Katsina State Primary Health Care Agency (KSPHCA) domin cike guraben aiki a cibiyoyin lafiya na matakin farko a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Ayyukan da ake bukata:
Midwives / Community Midwives
Community Health Extension Workers (CHEWs / JCHEWs)
Sharuddan cancanta:
Dole ne mai nema ya kasance É—an asalin Jihar Katsina
Dole ne ya mallaki takardar shaidar sana’a ko Diploma (Midwifery, CHEW, ko JCHEW)
Dole ne ya kasance mai rajista kuma da niyyar yin aiki a yankunan karkara
Yadda ake nema:
Cika fom É—in a wannan adireshin
🔗 https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSfdB81Z1eNjV3UKX9ESGB3XLS3pQySlLNecoe7qnOOFSKrcog/viewform?usp=sharing
Ranar ƙarshe: 28 ga Oktoba, 2025
Kada ku bari wannan damar ta wuce ku — dama ce ta bauta wa al’umma da inganta harkar lafiya a Jihar Katsina.
Sa hannu:
Hon Ashiru Nahuce
Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Danja
Katsina State Primary Health Care Agency CBHW & SBA Application Form (For CHEWS, JCHEWS, Midwives & Community Midwives ONLY) Dear Applicant, read carefully and respond to all questions before you submit your application.