05/12/2023
Nigerian Youths Development And Awareness Forum
Haɗaɗɗiyar Majalisar Matasan Arewacin Najeriya Zalla, Waɗanda Ke Ƙaunar Ɗaukakar Matasan Mu Na Arewa.
05/12/2023
10/10/2023
Dole Matasan mu na Arewa Su Farka, Musamman a wannan lokacin da a kullum maƙiyanmu ke ƙara samun goyon bayan Yahudawa wajen halakar damu.
Manufofin wannan ƙungiya zai zama mai tasiri ga mutanen arewa ne, waɗanda har yanzu wutar ƙyamar da yankin ke cigaba da ruruwa a zukatan su. La'akari da yadda muka zama koma baya a kowane mataki.
Wannan ƙungiya ta shirya tafiya ka faɗa guda da ƴan jaridar mu dake da sarai kan wannan jarabta da Allah yai mana, Jami'an tsaro da dukkannin waɗanda zasu bada gudunmawa wajen farfado da ƙimar wannan yanki namu.
A ƙarshen wannan watan zamu Ƙaddamar da shiri na musamman, wanda zai taɓa dukkan wani matashi dake raye a wannan yanki da Allah ya azurta da albarkatun ƙasa, wanda hakan ne dalilin da turawa ke amfani da sakar karu daga cikin wadanda Allah ya basu ikon zama shugabanni daga cikin mu gwara kanmu.
Allah ya bamu nasara amin.
(N. Y. D. A. F)
10/10/2023.
09/10/2023
Shi adalci agun masu mulki wajibi ne. Hakanan duk wanda aka bashi wata amana ko shugabanci, to wajibi ne ya zama mai adalci da gaskiya wajen kiyaye amanar da aka bashi.
Idan mai mulki ya zamto adali to saboda albarkar adalcinsa Allah yakan kiyaye garinsa ko jiharsa ko ƙasarsa daga wasu bala'o'i da chututtuka da yawa. Kuma Allah yakan sanya albarka acikin jama'ar da yake jagoranta. Kasuwancinsu da nomansu da sana'o'insu duk zasuyi albarka.
Idan aka samu albarka acikin waɗannan abubuwan da na lissafa to in sha Allahu tarbiyyar al'ummar zata gyaru, yanayin zamantakewar aure za'a samu sauyi, ilimi zai bunkasa, zaman lafiya zai wanzu, kuma tattalin arzikin al'ummar zai bunƙasa.
Mu dubi irin ɗaukakar da daular musulunci ta samu a zamanin Khalifancin Sarkin Muminai Umar bn Khattab (Allah ya yarda dashi) wanda a lokacin sa sai da musulunci ya mamaye dukkan yankunan larabawa har da yankunan sauran ƙabilun nahiyar Asia, kai har daular turawan rum (Roman Empire) hantarsu takan kaɗa da zarar an ambaci sunan "UMAR" ko "ISLAM".
Saboda irin waɗannan nasarorin ne bayahuden Amurkan nan mai suna Micheal Hart bisa nazarinsa ya sanya sunan Sayyiduna Umar akan gaba-gaba acikin jerin manyan shugabannin da rayuwarsu tayi babban tasiri aduniya baki ɗaya.
A zamanin Sayyiduna Umar saboda tsantsar adalcinsa arziki ya mamaye ko ina acikin daula, har albashi yake biyan sauran sahabbai musamman Ahlu Badrin da Muhajirai, sannan gwamnatin musulunci a lokacin sa tana taimaka wa marayu da zaurawa da marassa galiho.
Adalcin Sayyiduna Umar (rta) yakai har watarana ya bugi wani daga cikin gwamnoninsa saboda laifin danne hakkin wani Kirista talakansa. Kunga tsantsar adalci kenan babu wariya, babu zalunci.
Saboda tsantsar adalcin da ya watsu a daularsa, sai gashi arziki ya yawaita a hannun jama'a, Kuma ayyukan laifi sun ƙaranta. Sai ayi shekara da shekaru ba'a samu wani yayi zina ko sata ba.
Ko a wannan zamanin namu, rashin adalcin da Shugabanninmu ke yi shine babban tushen lalata tarbiyyar al'ummah.
Yayin da Shugabanni basu damu da tsaron lafiyar kowa ba sai tasu, basu damu da kiwon lafiyan kowa ba sai nasu da iyalansu, basu damu da jin dadin kowa ba sai nasu, za'a take dokokin Allah basu damu ba, to ku saurari watsuwar bala'in cututtuka da kashe kashen rayuka da manyan laifuka a cikin al'umma.
Ya Allah ka gyara halayen Shugabanninmu, ka haɗa su da mashawarta na kirki, ka kyautata tattalin arzikinmu, ka yaye matsalolinmu, Muna kamun Qafa da soyayyar Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
(NYDAF-TEAM)
09/October/23.
09/12/2021
Duk Wani Abu Da Talaka Zayyi Tinkahon Ya Mallaka Sun Kwace, Damar Dayace Dake Hannunsa, Itama Yanzu Tazama Mara Tabbas.
Ubangiji ka tallafi Al'ummar kasata Nigeria mazauna arewa, dama dukkan Musulmi dake Rayuwa a kaikaikaccen yanayi irin namu, ubangiji ka rahamtawa wadannan bayi naka.
Amman gallazawar da akewa 'yan arewa abun yayi yawa, zalincin ankure malejinsa.
30/10/2021
NASARAR IRINSU KWANKWASO A SIYASA NASARAR MILIYOYIN AL'UMMACE, 2023 Ubangiji Ga Oga.
Ayau asabar 30 ga watan October din 2021, babbar jam'iyar adawa ta kasa PDP, ta gabatar da zaben Cikin gida na shugabancin jam'iyar a duka sassan fadin kasar, taron wanda ya sami halartar tsohon gwamnan kano, bayan haka tsohon sanata daya sami wakilcin shiyar Kano ta tsakiya, a zauren majalisar dattijai ta kasa, Engr Dr Rabi'u Musa Kwankwaso.
Manyan jagororin jam'iyar PDP matakin Jahohi da kasa, sun razana da bayyanar tsohon gwamnan na Kano, bayan haka jagoran kungiyar Siyasa mafi rinjayen karfi a Africa kwankwasiyya.
Dubban magoya bayan madugun na darikar kwankwasiyya daga duka fadin sassan jahohi 37 dake fadin tarayyar kasar nanne s**a cika garin na Abuja sanye da hulana jajaye da manyan alamomi dake bayyana zahirin mubaya'arsu ga salon jagoranci na tsohon gwamnan na Kano. yayin da zaben shugabancin jam'iyar ya gudana, a Babban filin taro na eagles square dake Abuja.
Ya ubangijin Musulunci ka tallafi mai burin temakawa bayinka a Ko'ina yake. Allah idan wannan bawa zaizama Al'khairi ga talakan kasarmu Nigeria, ka danka masa ragamar, inka bashi kayi ruko da hannayensa.
Allah in hakan fitina zaizame masa duniyarsa da lahirarsa, muna rokon kadorar da tunaninsa kan tubalin Gina Musulunci da Al'ummar musulmi ameen.
T.K.O Reporter's
30/October/2021.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Contact the business
Telephone
Address
Abuja
12610
