Dominku Ma'abota Soyayyah

Dominku Ma'abota Soyayyah

Share

wannan pejin antanadeshine domin wa'yanda s**a samu sabani asoyyarsu dabada shawar wari masu kyau domin adedeta juna.

12/06/2022

Idan namiji baya iya kai zuciya nesa idan ya fusata kuma yana yawan yin nadama daga bisani akan abubuwan daya aikata cikin fushi, to akwai yuwuwar zai fi son macen data ƙware gurin shawo kan mazajen da s**a fusata. Koda kuwa sauran mutane basu ga kyan wannan macen shi zai ga cewa kyakkyawa ce a idon shi

Dominku Ma'abota Soyayyah Send a message to learn more

18/03/2022

ABINDA WANI UBA YA FADAWA 'YARSA ANA GOBE ZA'AYI AUREN TA

'Yata, gobe zaki daina amsa sunarki na 'yata. Zakiyi auren farin ciki zaki auri muradin ranki wanda k**e kauna.

Kada kiyi kewata domin na cika burina na aurar dake ga wanda k**e kauna, yanzu kuma ya rage naki ki cika naki burin.

Daga yarintarki, na samu nabaki tarbiya cikin ikon Allah ko? Kafin ki amsa mini da cewa eh, akwai wani abinda nakeso na fada miki dangane da zama da mijin aure na kasancewarki matar aure.

Kina tuna lokacin da kika rubuta jarabawar WAEC da JAMB? Kinzo kinsameni na baki #20,000 na registration? Duk da cewa na baki, toh kudin ba nawa bane. Nasan kin dauka cewa ni na biya miki kudin. Maganar gaskiya shine lokacin bani da sisi, Mahaifiyarki ita tabani. Tanada damar da zata baki kudin da hannunta, amma sai ta bani ni na baki.

Ki zamto mai tallafawa mijinki. Wani lokacin rayuwa takan tsananta, mijinki zai iya zamowa a fusace, domin rayuwa tayimar daurin tamtam, zai iya jin tsoron kada ya rasaki domin abin hannunshi ya kare a wannan lokacin, toh a wannan yanayi ne yake bukatar tallafinki, ki zamto mai bashi karfin guiwa sosai.

Babban hanyar da zaki bi wajen nunawa mijinki kina kaunar shi shine kina girmamashi da kuma kuma girmama ra'ayinshi!.

Ta yiyu kuyi jayayya tsakaninku, ko kuma kiki aminta da ra'ayinshi, amma a karshen ranar ki nunamar cewa ya cancanci ki girmamashi. Kina tuna lokacin da nayiwa Mahaifiyarki tsawa? meye tayi lokacin? Shiru tayi.

Kina kuma iya tuna wani lokaci data mini tsawa? Meye nayi? Shiru nayi nima lokacin.

Yake 'yata, ki zamto mai shiru ga mijinki lokacin da yayi fushi. Lokacin da dayanku zuciyarsa ke tafasa, dayanku ya tabbata zuciyarsa tana sanyaye. Idan ma'aurata biyu dukkansu suna tsawa wa juna a tare, ananne babbar matsalar aure ke somawa.

Farkon abinda yak**ata kisani dangane da mijinki shine abincin dayafi so! Idan sunada yawa, ki tabbata kin rikesu a ranki. Kada kibari sai ya roka kimar, ki zamto kinayi ba sai ya nema ba.

Akwai wani lokacin da Mahaifiyarki ta k**ani ina wasa da hannun wata mata, tabbass matar ta janye hankalina amma bawai ina cheating din mahaifiyarki bane. Lokacin data ganmu, batayi fada da matar ba, kawai k**a hanyar ta tayi ta wuce batace uffanba. A ranar naji tsoron komawa gida domin ina tsoron abinda zan tarar a gidan idan na koma. Ammana sai nayi ta mazan na koma gida. Kuma wallahi batace uffan ba. Ta hadamin abinci k**ar yadda ta saba. A hakan a tsorace nake domin nasan abinda na aikata. Sai na fara bata hakuri ta kuma ce babu komai ya wuce. Daga wannan rana ban sakewa yiwa wata mace kallo na biyu ba.

Waye yasan meye zai faru da ta yimin masifa ta balbaleni? Watakila dana fita na bar mata gidan na koma wajen waccan matar data k**ani da ita.

Wani lokacin shiru kan zamo silar sulhu maimakon fada da masifa da balbalin bala'i.

Ki manta da wadancan littattafan na soyayya da k**e karantawa lokacin kina budurwarki. Kin tuna wadannan finafinai na soyayya na India da American? Wasu Nollywood Movies dinnan? Ki manta dasu, kada ki tsammanin rayuwar aurenki ya zamto irin wadancan.

Rayuwa a zahiri ba k**ar wacce wasu Directors da marubuta, su Artist da Producers s**a rubuta bane, rayuwar aure Allahu Jalla Wa Azza ne ya ke Directing kuma shine Producer, shine Artist.

Abu na karshe dana bukata kisani shine....... Kina tuna lokacin da aka haifeki?

Bayan aure na da Mahaifiyarki, rayuwa ta tsananta garemu. Mamarki ayyuka biyu takeyi domin ta tallafa mana, bawai bana aiki bane, nima ma'aikaci ne. Ina dawowa gida karfe 6 na yamma, ita kuma karfe 8 na yamma kuma a gajiye. A hakan bata ta6a hanani abincin dare ba ko kuma kin kulawa da wajen kwanciyar mu. A hakan aka samu aka haifeki cikin ikon Allah.

Kada ki kuskura ki hana mijinki kanki ko abinci komai gajiyanki, ki zamto mace tagari.

Har abada kinanan a 'yar Daddy.

03/12/2019

*Mama Mai Yasa K**e Kuka?
*Mama Kidaina Mun Kuka??
>Ni Ina Cikin Neman ALLAH
>Nida Bana Zina
>Nida Bana Karya
>Nida Bana Cin Amana
>Nida Ba'a Bina Bashi
>Nida Nake Zikirin ALLAH Koda Yaushe
>Nida Nake Karatun Al'Qur'ani Kuma Ina Aiki
Dashi
>Nida Bana Zalunci
>Nida Bana Wasa Da SALLAH
>Nida Bani Da Abokan Banza
>Nida Bana Gulma Da Mutane
>Nida Bana Raina IYAYENA
>Nida Bana Tare Da Mugayen Shuwagabanni
>Nida Na Yarda Da Kaddara Mai Kyau Da Mara
Kyau
>Nida Na Ware Lokaci Dan Ganin Talakawa
>Nida Nake Azumin Watan Ramadan
>Nida Naka Zakka
>Nida Nake Ziyaran Asibiti Na Taimak**a
Marasa Hali..!
*Mama Kidaina Mun Kuka? Kice Suzo Suyi Saurin
Kaine Makwancina Duniyan Nan Tana Mun
Zafi........!
*Babu Mai Jin Maganan Wanda Ya Mutu Sai
ALLAH Madaukakin Sarki..!
YAA ALLAH KASA MU FADI IRIN WADANNAN
KALMOMIN NAN RANA DAKA DAUKI RANMU..!

18/08/2019

MABIYA ADDININ KIRISTANCI NA DUNIYA NA FUSKANTAR BARAZANA
Hankalin Fafaroma Ya Tashi Sak**akon Gano Wani Bible Da 'Jesus'
Ke Wasiyyan Zuwan Annabi Muhammadu (S.A.W)
'Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible
wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S
(Jesus) ya yi wa mabiyansa albishir da zuwan Annabin karshe mai
suna Muhammad (Annabi Muhammadu S.A.W).
An yi ittifakin cewa Littafin ya kai shekara 1,500 da rubutawa. Kuma
an rubuta shi ne da ruwan zinari a cikin harshen "Aramaic" (Larabci).
Jaridar Daily Mail ta Amerika ta ruwaito cewa, gano littafin wanda
aka yi hasashen duk falle daya a cikinsa zai kai kimanin Yuro milyan
£14 ya jawo muhawara mai tsanani a tsakanin mabiya darikar Vatican
da musulmi inda har Fafaroma Pope Benedict XVI ya nemi a kawo
masa bibile din ya gani.
Idan dai aka tabbatar da zargin da ake yi akan Bible din kuma ta
tabbata haka din ne. To akwai chakwakiya ganin cewa littafin zai
karyata mabiya addinin kirista dake Allantar da Isah (AS) da kuma
masu cewa Jesus din dan Allah ne. Bible din zai tabbatar da cewa
addinin Islama shine gaskiya kuma Musulmai sune ke kan addini na
gaskiya wanda (Almasihu/Jesus) ya umurci mabiyansa akai.
Majiyar ta mu ta kuma ruwaito cewa an gano littafin ne tun a
shekara ta 2000 amma hukumomin kasar Turkiyya s**a cigaba da
tsaron shi har zuwa shekara ta 2012 inda s**a kaishi gidan tarihi na
Ankara Ethnography Museum. Kuma ana sa ran nan bada jimawa ba
za'a rika nunawa mutane Bible din a gidan tarihin kasar.
Ministan raya Al'adu da yawon bude ido na kasar Turkiyya, Ertugrul
Gunay ya ce suna kyautata zaton Bible din na gaskiya ne shi yasa
wasu s**a boye shi saboda yadda littafin ya yi bayani akan ainihin
matsyin Almasihu (Jesus) sabanin tunaninsu.
Jaridar ta daily mail ta kara da cewa hankalin fafaroma da sauran
manyan limaman kiristoci ya tashi sak**akon gano wannan littafi na
Bible.
Don Allah idan ka karanta ka tura a other groups.

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address

Dan Mom Teloring Fashion Design Bababa Plaza Bauchi
Abuja