Usman Ahmad Musa

Usman Ahmad Musa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Usman Ahmad Musa, Public Service, Abuja.

Civil engineer|| Home designer||Cyber security|| Bug bounty hunter|| Ethical hacker || Web developer|| Blogger|| Financial trader||Travel content Creator|| Business spokesman|| Digital content creator ||Influencer|| Freelancer |||

24/11/2025

Duk wanda yake baka kyauta, zai kasance kana jin nauyinsa. Duk wani abu da zai ɓata masa rai, zaka ƙaurace masa don gudun kar kayi masa laifi

Yana dagacikin hanyoyin da yan siyasar najeriya ke bi wurin rufe bakin malamman addini da sarakunan gargajiya

Sai a baka kyautar mota "Toyota Land Cruiser Prado"

A gina maka babban masallacin jumu'a tare da albashi mai tsoka

Daga lokacin shikenan an rufe bakin malami ko sarki, bazai taɓa iya fitowa yace gwamnati tayi kuskure ba domin a gyara 🥲😭

Sai dai kullum idan anje gidan ɗan siyasa sai ayi masa addu'a da jinjina masa
---------------------

Idan ɗan social media ne kai, daga lokacin da aka baka kyautar waya, roba-roba, kujerar umrah, ko ƙaramar mota 206

Shikenan daga wannan ranar an saye ka, dakai da gaskiya kunyi opposite directions

Idan an kashe mutane ko an sace ɗalibbai, ba zaka iya rubutawa ba a shafinka sai dai kayi shiru kana scrolling kamar wanda aka yiwa asiri 🥲😭
---------------------

Yau an waye gari kaf Nigeria babu malami ko sarkin dake iya faɗawa gwamnati gaskiya domin a gyara saboda tsoro

To ku jira zuwan musiba da bala'i da fitina inji manzon Allah Saw.

Alhassan Mai Lafia

15/06/2025

Saura kiris Iran ta mayar da Isra'ila kufai – Mejo Amir.

Sabon kwamandan rundunar sojin, Janar Mejo Amir Hatami, ya bayyana shirye-shiryen sojojin Iran na kai mummunan hari ga gwamnatin Isra'ila.

A cikin saƙon da ya aikawa Jagoran Juyin Juya Hali na Musulunci, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ranar Lahadi, Janar Hatami ya gode masa bisa amincewa da naɗa shi a matsayin sabon shugaban sojojin ƙasa.

Yayin da yake sabunta mubaya’a ga manufofin juyin juya halin Musulunci, sabon kwamandan ya ce sojojin Iran daga sassa daban-daban — Rundunar ƙasa, Rundunar Sama, Rundunar Ruwa da Rundunar Kariya ta Iska — za su kare 'yancin kai da mutuncin iyakokin ƙasar Iran da kafa gwamnatin Jamhuriyar Musulunci da gaskiya da ƙwazo da rikon Amana..

Janar Hatami ya jaddada rawar da rundunar soji ta taka wajen kare ƙasar nan take bayan harin da gwamnatin Isra’ila ta kai a farkon safiyar ranar Juma’a, yana mai cewa rundunonin sojin za su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin rusa gwamnatin Isra'ila da yaudarar duniya wacce ke kashe yara.

Gwamnatin Isra’ila ta kai hari a wasu unguwannin zama a Tehran da kuma wuraren soja da makamashi na nukiliya a wasu sassan ƙasar Iran a safiyar ranar 13 ga Yuni.

A cikin harin, an kashe manyan hafsoshin soja da masana nukiliya akalla shida, tare da fararen hula da dama.

Rundunar Sojin Iran ta mayar da martani da gagarumin luguden makamai masu linzami a wasu birane da ke yankunan da Isra’ila ta mamaye.

15/06/2025

Kamfanin jiragen saman Isra’ila ya soke tafiye-tafiye zuwa wasu sassan biranen kasar har zuwa ranar 23 ga Yuni.

15/06/2025

Yadda makamin Iran ya lalata ginin Bat Yam dake birnin Tel Aviv na kasar Isra'ila.

15/06/2025

YANZU-YANZU: Iran ta harba Jirgin Shahed mai Sarrafa kansa guda 135 a birnin Tel Aviv na kasar Isra'ila, a Yammacin Yau Lahadi. Abdul Journalist 1

15/06/2025

Mansoureh Alikhani, a painter and visual artist, was killed in a Saturday night attack by the Israeli regime on residential areas in Tehran.

15/06/2025

Isra’ilawa masu son tserewa daga Isra'ila sun shiga ruɗani a filin jirgin Ben Gurion a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da kai hare-hare cikin Isra’ilar.
Isra’ilawan sun gudu sun bar kayayyakinsu sakamakon yadda s**a kiɗime

08/05/2025

RIKICIN INDIYA DA PAKISTAN....

Bayan da kasar Pakistan ta samu nasarar kakkabo jiragen yakin indiya wadanda ta siyo daga kasar France, wanda hakan ya janyo hannayen jarin kamfanin Dassault Rafale s**a faɗi a kasuwa...

A daren jiya Indiya ta harba Jirage marasa Matuki DRONES wadanda ta siyo daga kasar Isra'ila sai dai kasar Pakistan ta samu nasarar kakkabo DRONES sama da 25 da aka harba mata...

DRONES din da ake kira da HAROP DRONES sun kasance daga cikin drones mafiya haɗari da kasar Isra'ila take kerawa...

Indiya ta kai farmakin ne zuwa garuruwan Rawalpind, Gujranwala, Attock, Chakwal, Lahore, Bahawalpur, Miano, Chhor, Karachi sai dai kusan dukkan drones din an samu nasarar kakkabo su sakamakon kwarewa da sojojin Pakistan s**a nuna...

Har zuwa yau alhamis Pakistan bata mayar da martanin hari ga kasar Indiya ba, amma ana kyautata zaton zata kai mummunan hari da zai girgiza kasar Indiya....

To Madallah....

06/05/2025

"Heartfelt thanks to each and every one of my amazing followers! Your support, encouragement, and engagement mean the world to me. I'm grateful for the opportunity to share my thoughts and experiences with you all. Let's keep growing and learning together! "

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Address

Abuja