Jakadiya Hausa

Jakadiya Hausa

Share

Ku Kasance Da Jaridar "JAKADIYA HAUSA" Domin Samun Ingantattun Labarai.

29/05/2026

DR YAKUBU ADAMU A TAKAICHE

Dan asalin Giade, an haife shi a Gwabba, ya tashi a Ilelah da Karofin Madaki

An tabbatar da Yakubu Adamu, PhD, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM) mai mulki a Jihar Bauchi domin zaɓen shekarar 2027.

Dr. Yakubu bai samu wannan matsayi cikin kuskure ko sa’a kawai ba. Cikin tawali’u da nutsuwa ya gina kansa har ya kai wannan matsayi mai daraja, duk da kasancewarsa matashi daga gida mai sauƙin rayuwa.

Yana da ƙwarewa sosai wajen shugabanci da gudanarwa, kasancewar ya yi aiki a harkar banki na tsawon lokaci. Ya fara aikin banki ne daga ƙaramin matsayi, amma cikin ƙanƙanin lokaci ya riƙa hawa matakai daban-daban har ya kai matsayin jagoran sashen kula da gwamnati a yankin Arewa maso Gabas da kuma Manajan Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na Polaris Bank a Bauchi.

Yakubu Adamu, PhD, shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki na Jihar Bauchi da ya gabata nan kusa. Ya yi murabus daga muƙaminsa a watan Afrilun 2026 domin mayar da hankali kan burinsa na neman kujerar gwamna.

Shi ɗan asalin ƙauyen Gulbun ne da ke Gundumar Doguwa a Ƙaramar Hukumar Giade ta Jihar Bauchi. An haife shi a unguwar Gwabba da ke cikin garin Bauchi a ranar 12 ga Agustan shekarar 1980. Ya taso tsakanin Gwabba inda aka haife shi, Ilelah inda ya fara karatun firamare, da kuma Karofin Madaki inda ya ci gaba da rayuwarsa.

Ya fara karatunsa a Makarantar Firamare ta Kofar Fada daga shekarar 1986 zuwa 1992.

Bayan kammala makarantar firamare, ya halarci Pilot Junior Secondary School daga 1992 zuwa 1995 domin karatun sakandare na ƙasa, sannan ya wuce Government Science Secondary School Toro daga 1995 zuwa 1998 domin karatun sakandare na gaba da ƙasa.

Ƙishirwar neman ilimi da faɗaɗa tunaninsa bai tsaya a nan ba, domin ya samu gurbin karatu a Kwalejin Fasaha ta Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi, inda ya yi shirin Advanced Level tsakanin shekarar 1999 zuwa 2001.

A shekarar 2001, ya samu gurbin karatu a babbar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) Bauchi, inda ya samu digirin farko na B.Tech a fannin Gudanar da Kasuwanci a shekarar 2006. Daga bisani ya koma wannan jami’a a shekarar 2008, inda ya samu digirin MBA a shekarar 2013.

Neman iliminsa bai tsaya nan ba. Dr. Adamu ya kai kololuwar tafiyarsa ta ilimi bayan ya samu wani digirin Masters a fannin Finance, Investment and Banking daga International University of Bamenda da ke Jamhuriyar Kamaru tsakanin 2014 zuwa 2016. Daga baya ya koma jami’ar inda ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Bincikensa da rubuce-rubucensa a fannin kuɗi da bunƙasa tattalin arziki sun ƙara tabbatar da shi a matsayin mutum mai ilimi da ƙwarewa sosai da kuma mutunci a idon jama’a.

AIKINSA NA ƘWARARRU

Aikinsa ya fara ne a First City Monument Bank (FCMB) a shekarar 2008, inda ya yi aiki har zuwa 2013 yana ƙara gogewa a harkar banki. Ƙwarewarsa da kwarewa wajen tafiyar da harkokin kuɗi ne s**a kai shi wani muhimmin matsayi a Polaris Bank, inda ya yi aiki daga 2013 zuwa 2023 har ya kai matsayin Regional Manager.

Ya yi aiki a matsayin Team Lead, Public Sector (Northeast) a Polaris Bank Limited daga 2019 zuwa 2021; Business Development Manager a Skye Bank Plc Bauchi daga 2015 zuwa 2019; Head of Branch Retail a Skye Bank Plc Bauchi daga 2012 zuwa 2015; sannan Marketing Officer a First City Monument Bank daga 2008 zuwa 2012.

Dr. Yakubu Adamu mamba ne na Nigerian Institute of Management (Chartered), da Chartered Institute of Economics, da Chartered Institute of Bankers of Nigeria, da kuma Chartered Institute of Loan and Risk Management.

SHIGOWARSA SIYASA

Shigowar Yakubu Adamu, PhD cikin siyasa ya fara ne lokacin da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya naɗa shi a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki a shekarar 2023. Duk da cewa wannan naɗi ne ya fito da shi fili a siyasa, tun kafin hakan Yakubu ya taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zaɓen karo na biyu na gwamnan.

Doguwar gogewarsa a harkar banki ta ba shi cikakken tushe wajen tafiyar da harkokin kuɗi, aiwatar da manufofi da bunƙasa tattalin arziki a matakin yanki. Matsayansa daban-daban a harkar banki sun ƙara ba shi fahimta sosai kan tsarin kuɗi, ƙwarewar da ya yi amfani da ita yadda ya k**ata lokacin da yake Kwamishinan Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki.

Dr. Yakubu Adamu ya kasance daya daga cikin ginshiƙan gwamnatin Gwamna Bala Mohammed, musamman wajen aiwatar da shirye-shiryen My Project 1 da My Project 2 da aka ƙaddamar domin bunƙasa Jihar Bauchi. Ya nuna nagarta, hangen nesa da jajircewa wajen kawo sauyi mai amfani ga al’umma.

Yana da aure tare da ’ya’ya. Daga cikin abubuwan sha’awarsa akwai wasan ƙwallon ƙafa, karatu da bincike. Haka kuma Dr. Yakubu yana riƙe da manyan sarautun gargajiya na Wazirin Giade da kuma Sardaunan Gulbun.

Rubutawa: Abdul Ahmad Burra

Fassarawa: BAUCHI YOUTH COALITION FOR GOOD GOVERNANCE

28/05/2026

Yau a hukumance an tabbatar dani a matsayin ɗan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APM.

Na karɓi wannan amana da kuka bani cikin ƙan-ƙan da kai da kuma sanin nauyin amanar da kuka ɗora min. Ina kuma ƙara jaddada muku shirina na aiki tuƙuru domin na cigaba da bautawa jiharmu ta Bauchi.

Bayan miƙa godiya ga Allah maɗaukakin Sarki bisa ga rahmarsa da ni'imominsa garemu daya tabbatar da wannan al'amari, na miƙa godiya da girmamawa ta musamman ga jagoranmu kuma abun koyi a garemu, jan gwarzon da baya ja da baya, Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Senator Bala Mohammed CON Ƙauran Daular Usmaniyya, bisa amanna damu da goyon bayan daya bani da sauran jama'a. Shine ya zaƙulo mu bayan ya fahimci irin baiwar da Allah Ya mana, ya jawo mu a jikinsa, bayan ya mana karatun tsaf, ya kuma bamu muƙaman da bamu taɓa mafarkin samu ba. Sannan ya horar damu domin gogewa a shugabanci domin shirya gobenmu da tunkarar duk wani ƙalubale.

Irin tarihinsa, da tsoron Allahnsa, da nasarorin da ya cimma a cikin shekaru bakwai da s**a gabata, da shugabancinsa na ƙishin ƙasa, su s**a bamu ƙwarin gwiwar fitowa mu nemi wannan takara domin ɗorawa daga inda ya tsaya a aikinsa na gina Jihar Bauchi abar alfaharinmu.

Na kuma miƙa godiya ta ga shugabannin jami'yyarmu ta APM, masu ruwa da tsaki, ƴan jam'iyya maza da mata da dukkannin al'ummar Jihar Bauchi bisa wannan aminci da aka nuna mana.

Abokan takarata sun cancanci yabo. Kowanne a cikinsu ya nuna sanin ya k**ata, sadaukarwa, ƙwarewa da ƙaunar Jihar Bauchi. Yanzu takara ta ƙare. Yanzu za a fara asalin gwagwarmayar. Ina miƙa ƙoƙon bara garesu su zo mu haɗa kanmu a manufa guda wadda itace gina Jihar Bauchi da samun nasara a babban zaɓe idan Allah Ya kai mu shekara ta 2027.

Jiharmu ta Bauchi ta jima da hawa turbar cigaba. Tubalin da aka gina domin cigaban Jihar nan mai ingantacce ne mai kuma kyakkyawar manufa. Dole ne mu kare wannan nasara da matsayi da Jiharmu ta ginu a kai. Dole ne mu ɗora daga inda aka tsaya. Dole ne mu kai Jiharmu zuwa mataki na gaba. Yaƙin neman zaɓe da za muyi ba zai kasance ba na rarrabuwar kai ba. Kamfen din mu zai maida hankali ne kan ɗorawa daga inda aka tsaya da kuma maganar cigaba da haɓakar tattalin arziƙi.

Kamfen dinmu zai kasance akan muhimman abubuwan da s**a shafi al'umma k**ar su: samar da aiyukan yi da damarmakin samun arziƙi, bunkasa ilimi, samar da ingantaccen kiwon lafiya, aiyukan raya ƙasa, raya karkara, tallafawa matasa da tafiya dasu a al'amaran gwamnati, samar da mak**ashin lantarki da sauransu.

Magoya bayanmu, wannan nasara da na samu ba tawa bace ni kaɗai, tamu ce gaba ɗaya. Ku ma magoya bayan abokan takarata ina miƙa muku goron gayyata. Ku zo mu haɗa kai a tafi tare. Kowa yana da matsayi a wannan tafiya. Tafiya ce ta ƴan gida ɗaya. Ku zo mu tafi tare a matsayin ƴan uwan juna. Aikin dake gabanmu na bukatar sanin ya k**ata, haɗin kai da jajircewa. Idan muka haɗa kai za mu yi nasara.

Nagode. Allah Ya albarkaci Jihar Bauchi. Allah Ya bamu nasara.

Naku,
Yakubu Adamu PhD
(Wazirin Giade)
Dantakarar Gwamnan Jihar Bauchi a tutar jam'iyyar APM

26/05/2026

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP ta tabbatar da Farfesa ISA ALI PANTAMI a matsayin dan takarar Gwamnan jihar GOMBE a zaben 2027

26/05/2026

DA DUMI-DUMI :
Zan mayar da mafi karanci albashin ma aikata zuwa dubu tamanin (80,000) in na zama gwamnan jahar Bauchi inji.Sen. Shehu Buba Umar

Ya kuke ganin wannan Magana?

25/05/2026

MANUFAR DR YAKUBU ADAMU AKAN TATTALIN ARZIKIN JIHAR BAUCHI

Jihar Bauchi jiha ce mai tarin matasa, amma tana fama da ƙarancin ayyukan yi, ƙarancin kudaden shiga da kuma bukatar tsayayyen tsarin tattalin arziki. A irin wannan lokaci, jihar na buƙatar jagora mai ilimi, gogewa da tsantsar kwarewa.

Dr. Yakubu Adamu tsohon Commissioner of Finance and Economic Development matashi ne kwararren technocrat da ya fafata wajen kawo gyara a gudanarwar kuɗi ta jihar.
A matsayinsa na masanin tattalin arziki kuma tsohon banker, ya taka rawar gani wajen:

1. ƙarfafa tara kudaden cikin gida
2. Rufe ɓatattun hanyoyin kashe kudi (leakages)
3. kawo tsarin kuɗi na zamani (tech-driven financial system)
4. habbaka gaskiya da tsari a duk harkokin kuɗin gwamnati

TO, MENENE MANUFAR DR YAKUBU ADAMU A BANGAREN TATTALIN ARZIKI IN AN ZABE SHI GWAMNAN JIHAR BAUCHI?

1. Ƙirƙirar Ayyukan Yi Ga Matasa
Zai kafa (Youth Employment Acceleration Programme) da zai bawa matasa sana’o’i, horo, da tallafin jari.
Zai buɗe cibiyoyin Skill & Innovation Hubs a kowace karamar hukuma.
Zai jawo kamfanoni da masana’antu ta hanyar samar da yanayin kasuwanci mai sauƙi domin su ɗauki matasa aiki.

2. Gagarumin Inganta Tattalin Arziki
Zai ci gaba da tsarin da ya fara: tsaurara bin doka a kuɗi, kawar da almundahana, da ninka kudaden shiga na jihar.
Zai mayar da hankali kan noma — musamman rice value chain, irrigational farming, and agro-processing centres.
Zai ƙarfafa harkar kasuwanci ta hanyar sauƙaƙe biyan haraji da kawo tsarin dijital.

3. Tallafi da ci gaban ƙananan kasuwanci (SMEs)
Zai samar da Bauchi Youth Enterprise Fund, wanda zai bai wa sana’o’in matasa jari marar (kudin ruwa) riba.
Zai tallafa wa ’yan kasuwa da kayan aiki, horo, da haɗa su da kasuwanni na kasashen waje.

4. Tsabtace Gwamnati da Gaskiya
Zai zurfafa tsarin open government da ya kafa a ma’aikatar kuɗi.
Duk wasu kudade da ayyuka za su kasance a fili don jama’a su gani, su bibiyi.

5. Ci gaban Kauyuka da Kananan Hukumomi
Zai zuba jari a hanyoyi, ruwa, makarantu, da cibiyoyin lafiya.
Zai mayar da hankali kan yankunan da s**a dade suna fama da rashin ci gaba.

Dr. Yakubu Adamu mutum ne da ilimi, kwarewa, da sahihiyar niyya s**a hade waje guda — wanda zai iya sauya Jihar Bauchi daga jiha mai dogaro da gwamnati zuwa jiha mai ingantaccen tattalin arziki da ayyukan yi ga matasa.

Daga BAUCHI YOUTH COALITION FOR GOOD GOVERNANCE

25/05/2026

Gwamnati ba zata iya shawo kan rikicin dake shirin faruwa ba idan Nasir El-Rufai Ya mutu a hannun Hukumar ICPC — Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a siyasar Najeriya, Chibuike Rotimi Amaechi, ya bayyana damuwarsa kan halin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ke ciki a tsare.

Amaechi ya ce:
“Ina fatan El-Rufai ba zai mutu a tsare ba. Idan hakan ta faru, zai tayar da abin da gwamnati ba za ta iya shawo kansa ba.”

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce da muhawara kan tsare El-Rufai da kuma zargin hana wasu manyan jagororin ADC ganinsa.

Wannan furuci na Amaechi ya kara ɗaga hankalin jama’a tare da jawo sabuwar muhawara a fagen siyasar Najeriya.

25/05/2026

Comr Sabo Muhammad YA FICE DAGA JAM'IYYAR APC BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU 27 YANA TSAGIN ADAWA .

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gundumar Hardo/Dan’Iya da ke karamar hukumar Bauchi, Comrade Sabo Muhammad, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Hakan na kunshe ne cikin wata takardar murabus da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na gundumar Hardo/Dan’Iya mai dauke da kwanan wata 20 ga watan Mayun na shekarar 2026.

A cikin takardar, Comrade Sabo Muhammad ya bayyana cewa ya ajiye katin zamansa mamba daga jam’iyyar APC ne daga ranar Laraba 20 ga watan Mayun 2026.

Ya ce ya dauki matakin ne cikin girmamawa da tawali’u, inda ya kuma gode wa jam’iyyar bisa irin goyon baya da hadin kan da aka ba shi tun lokacin da ya shiga jam’iyyar.

“Ina mika godiyata bisa dukkan goyon baya da karramawar da aka yi min a lokacin da na ke cikin jam’iyyar tun daga kafuwarta,” in ji shi.

Sai dai Comrade Sabo Muhammad bai bayyana dalilan da s**a sanya ya fice daga jam’iyyar APC ba a cikin takardar murabus din tasa.

23/05/2026

SAKO GA MUTANEN JIHAR BAUCHI: SHAWARA TA RAGE GA MAI SHIGA RIJIYA…!

Tun daga shekarar 2019 zuwa yau, an samu gagarumin sauyi a siyasar Jihar Bauchi an sauya yanayin siyasa daga tsoro zuwa kwanciyar hankali, daga rudani zuwa ci gaba mai anfani ga al’umma.

An kai ayyukan ci gaba zuwa sassa daban-daban na jihar.
An gina makarantu tare da karin ajujuwa domin ‘ya’yan talakawa su samu ingantaccen ilimi.
An bayar da guraben karatu ga dubban dalibai domin tallafawa makomar matasanmu.
An gina hanyoyi, gadoji da sauran ayyukan more rayuwa da s**a taba rayuwar jama’a kai tsaye.
Haka kuma, an gina masallatai tare da karfafa harkokin addini, zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’umma.

Abu mafi jan hankali shi ne yadda matasan Bauchi s**a samu daraja da matsayi a wannan lokaci.
A baya, matashi baya iya kusantar gwamnati…
Yau kuwa, matashi yana cikin gwamnati.
Yana bayar da shawara.
Yana jagoranci.
Yana da cikakkiyar damar bayyana ra’ayinsa a bainar jama’a.

Sai dai abin mamaki shi ne yadda wasu suke son al’umma su manta da abubuwan da s**a faru a baya, tamkar tarihin nan da bai taba faruwa ba.

Shin mun manta da shekarun 2015 zuwa 2019 ne?
Lokacin da siyasa ta koma abin tsoro.
Lokacin da k**a da daure matasa ya zama tamkar ruwan dare.
Lokacin da wasu daga wajen jihar nan s**a mamaye dukiyar Bauchi suna anfani da ita k**ar gadon iyayensu.
Lokacin da jama’a s**a rasa manyan ayyukan da zasu nuna a matsayin abin alfahari na gwamnati.

Mu fa mun gani.
Mun dandana wahala.
Mun san bambanci tsakanin mulkin da yake amfanar mutanen Jihar Bauchi da mulkin Yan kashe mu raba.

Saboda haka, lokaci ya yi da za mu tsaya tsayin daka wajen kare mutunci da makomar Jihar Bauchi.

Lokaci ne na hada kai domin gina sabuwar Bauchi mai cike da daraja, ci gaba da walwalar al’umma.

A saboda haka ne muke kira ga daukacin al’umma da su mara wa Dr. Yakubu Adamu baya domin tabbatar da dorewar ci gaba a jiharmu.

Jihar Bauchi tamu ce…
Kuma makomarta tana hannunmu.

EMAG
BAUCHI YOUTH COALITION FOR GOOD GOVERNANCE

22/05/2026

Shugaba Bola Tinubu ya yabawa NDLEA kan babban kamen miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa

...........

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya taya Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa wato NDLEA murna bisa nasarar da ta samu wajen cafke wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ta haɗin gwiwar Najeriya da Mexico, tare da rusa wata babbar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi da kuɗinta ya kai miliyoyin daloli.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

22/05/2026

JAMB ta saki sak**akon jarrabawar UTME na ɗalibai 279 da ta riƙe

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa, wato JAMB, ta sanar da sakin sak**akon jarabawar UTME guda 279 da ta riƙe bisa zargin aikata maguɗin jarabawa.

JAMB ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan gudanar da cikakken bincike kan wasu sak**akon da aka sanya wa ido tun lokacin gudanar da jarabawar da kuma bayan kammalawarta.

A cikin wata sanarwa da mai ba hukumar shawara kan hulɗa da jama’a, Dokta Fabian Benjamin, ya sanya wa hannu, an ce an saki wasu daga cikin sak**akon ne bayan bincike ya nuna babu hujjar da ke nuna ɗaliban sun yi maguɗi.

Sai dai hukumar ta ce ta soke sak**akon wasu ɗaliban da aka tabbatar sun aikata maguɗin jarabawa, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu cibiyoyin jarabawa da aka samu rahotannin ayyukan da ake zargi.

JAMB ta yi gargaɗin cewa duk ɗalibin da aka samu da laifi bayan kammala binciken, za a soke sak**akonsa.

Hukumar ta kuma buƙaci ɗaliban da har yanzu ba su ga sak**akonsu ba su duba matsayinsu ta hanyar aika saƙon “UTMERESULT” zuwa 55019 ko 66019 da lambar wayar da s**a yi rajista da ita.

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address

Maitama
Abuja
005