12/06/2026
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane su mika wuya ko kuma su fuskanci karfin gwamnati.
Arewa Updates ta rawaito cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne cikin sakonsa na Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yunin 2026.
Ya ce gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen yaki da ta’addanci, inda ta lalata wani babban sansanin ISWAP a yankin Arege da ke Jihar Borno.
Ya kara da cewa yawan mutanen da ake kashewa sakamakon ta’addanci ya ragu da kashi 81 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2015, yayin da aka kawar da sama da ’yan ta’adda 13,000 a cikin shekara guda da ta gabata.
Tinubu ya kuma bayyana cewa sama da mutane 124,000 daga cikin mayaƙa da iyalansu sun ajiye makamansu ta hanyar shirin Operation Safe Corridor tun daga shekarar 2023.
Kazalika ya gargadi masu ci gaba da aikata laifuka cewa damar mika wuya ba za ta kasance
12/06/2026
A Jawabin shugaba Bola Ahmad Tunubu shima ya yarda cewa ana ta’addanci kuma babu ingantaccen tsaro a kasar.
Inda a jawabinsa yake cewa “Suna Gargadin yan ta’adda Kodai su tuba, su Mika wuya (Surrender) ko kuma sun fuskanci fushin hukumomin tsaron kasar!
Ni abinda nake cewa, har tsawon wane lokaci ne zaa jira wannan yan ta’addan suyi surrender Kafin a dauki mataki akansu Idan sunqi surrender. Yanzu duk tsawon shekarun nan da s**a Kwashe suna ta’addanci, suna sace mutane, suna Kashe mutane Amma jira ake har yanzu suyi surrender?
To tsawon wane lokaci ne Wanda Idan basu yi surrender sun mika wuya ba gwamnati zatayi Amfani da Karfinta wajen Kawar da wannan yan ta’addan?
12/06/2026
Idan an isa ace ba 'yan Kano bane
12/06/2026
Dandalin sada zumunta na Facebook ya samu tangarda da ta shafi wasu masu amfani a sassa daban-daban na duniya, lamarin da ya hana su yin posting da kuma ganin sabbin bayanai.
Arewa Updates ta rawaito cewa, masu amfani da dama sun bayyana cewa duk da wasu suna iya shiga asusunsu, amma sun kasa wallafa bayanai ko amfani da wasu sassan dandalin yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa wasu masu amfani sun rika samun sakon "Error performing query. Give feedback." yayin kokarin yin posting, yayin da wasu kuma s**a samu sakon "Session Expired" wanda ya sa aka fitar da su daga asusunsu.
Tangardar ta shafi wasu daga cikin ayyukan Facebook, Instagram da Messenger, lamarin da ya janyo rudani a tsakanin masu amfani, musamman masu gudanar da kasuwanci da sadarwa ta kafafen Meta.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kamfanin Meta bai fitar da wani bayani kan musabbabin matsalar ko lokacin da za a warware ta gaba daya ba.
Arewa Updates ta rubuta muku wannan labari da taimakon fasahar AI.
12/06/2026
Gwamnan Kano ya naɗa Buhari Kura a matsayin Mai bada Shawara kan Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu.
12/06/2026
What a great honor, Ibrahim Umar Balla. Good luck to the team because a new change will come soon.