Bala Wunti Media Forum

Bala Wunti Media Forum

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bala Wunti Media Forum, Political organisation, Bauchi.

21/05/2026

*DR. BALA WUNTI NE MAFITAR MATASAN BAUCHI*

Mu zabi Dr. BALA WUNTI

Domin kawo karshen rashin aikin matasa a jihar Bauchi ✅

Domin inganta makarantun mu✅

Domin inganta lafiya✅

Domin inganta tituna✅

Domin inganta ruwan sha✅

Domin Samar da Sana'oi ga Mata✅

Domin inganta Samar da zaman lafiya ✅

Domin inganta tattalin Arziki ✅

Dr.BALA WUNTI mu shine zabin mu 2027 insha Allah!!!

19/05/2026

muyi wunti da alkhairi mutanan Bauchi

19/05/2026

alhamdulillahi
alhamdulillahi
congratulations to the Bala wunti family 🎉

Photos from BWSO Social Media Group's post 11/05/2026

Bala wunti alheri ne🤝

Photos from Bala Wunti Online's post 09/05/2026

indeed 📌

04/05/2026

Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah

25/04/2026

SANARWA ! SANARWA !! SANARWA !!!

Ƙungiyar Dr. Bala Wunti Media Forum, ta na sanar da ɗage gagarumin taron wayar da kai da ta shirya kan muhimmancin mallakar katin zaɓe da aikin yin rigistar katin zaɓe ga wanda basu da shi a ƙaramar hukumar Bauchi.

An ɗage taron ne bayan samun rahoton cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta dakatar da aikin yin rajistar katin zaɓe a faɗin ƙasar nan. Wannan ne ya sa aka ɗauki matakin jinkirta taron, kasancewar rajistar katin ce jigon shirya taron.

Ƙungiyar ta na mai bayyana cewa da zarar hukumar INEC ta ci gaba da aikin rajistar, za a sanar da sabon ranar gudanar da taron.

Hakazalika, ƙungiyar ta jaddada cewa ba za ta ja da baya ba wajen ci gaba da ayyukanta domin tabbatar da nasarar Dr. Bala Wunti a matsayin gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen shekarar 2027.

22/04/2026

Ƙungiyar Dr. Bala Wunti Media Forum za ta gudanar da gagarumin taron wayar da kai kan muhimmancin mallakar katin zaɓe tare da yin rijistar ga wadanda basu da shi a ƙaramar hukumar Bauchi.

An shirya wannan taro ne domin ƙarfafa gwiwar al’umma su mallaki katin zaɓe, kasancewar shi ne mabuɗin damar zaɓar shugabanni nagari da kuma tabbatar da an yi zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Ƙungiyar Dr. Bala Wunti Media Forum, wadda ta dade tana gudanar da ayyukan wayar da kai ga jama’a, na ci gaba da tsara wasu muhimman shirye-shirye da za su amfani al’umma.

Daga cikin waɗannan shirye-shirye akwai ƙoƙarin ƙara wayar da kan jama’a domin su fahimci muhimmancin zaɓar ɗan takara nagari mai kishin al’umma.

Kungiyar ta jaddada aniyarta na ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an gina al’umma mai wayewa da sanin haƙƙoƙinta na dimokuraɗiyya.

Photos from Bala Wunti Support Organisation's post 08/04/2026
07/04/2026

Innaa lillahi wa innaa ilaihir raji'un😭

​Fitaccen mai taimakon al’umma kuma jigo a jam’iyyar APC, Dr. Bala Maijama’a Wunti, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Comrade Abdullahi Koli, inda ya yi tsokaci kan rayuwa da kuma ayyukan taba-kaka na marigayin, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai tsananin kishin hidima, jagoranci, da ci gaban al’umma.

​Yayin da yake jawabi a ziyarar ta’aziyya da ya kai, Dr. Wunti ya bayyana alhininsa kan wannan rashi, inda ya bayyana cewa tasirin marigayi Koli ya wuce iyakacin yankinsa, domin ya taba rayuwar mutane da dama a fadin Jihar Bauchi ta hanyar jajircewarsa wajen harkokin jama'a na tsawon shekaru.

​“Ina alhinin rashin Abdullahi Koli a matsayin mutumin da ya rayu wajen yi wa bil’adama hidima — a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati, dan siyasa, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, wanda muryarsa da gudunmawarsa za su ci gaba da faduwa a zukatanmu,” in ji shi.

​Dr. Wunti ya karfafa gwiwar iyalan da aka bari da su kasance masu hadin kai da kuma ba juna kwarin gwiwa, yana mai jaddada cewa lokutan rashi na bukatar hakuri, imani, da kuma juriya ta bai-daya.

​Sannan ya yi kira ga iyalan da su yi alfahari da kyawawan dabi'u da marigayin ya bari, yana mai kara da cewa dabi’unsa na gaskiya, jajircewa, da sadaukarwa ba tare da son kai ba, ya kamata su ci gaba da zama jagora a gare su.
​Yayin da yake jawabi ga matasan gidan, Wunti ya ba su shawarar su kare mutuncin sunan mahaifinsu kuma su dora daga harsashin da ya aza, yana mai jaddada cewa ayyukan rayuwarsa za su ci gaba da zama madubin koyi ga tsararraki masu zuwa.

​Haka zalika, ya tabbatar wa iyalan cewa zai ci gaba da ba su goyon baya, yana mai cewa alakarsa da su za ta dore ko bayan kammala kwanakin makoki. ​Da yake mayar da martani a madadin iyalan marigayin, Alhaji Adamu Mai Fada ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyara da kuma kalaman karfafa gwiwa. Ya bayyana kasancewar Bala Wunti a tare da su a matsayin abin da ya faranta musu rai, inda ya kara da cewa hakan ya kara karfafa wa iyalan gwiwa wajen zama tsayin daka da kuma hadin kai.

​Ya kara tabbatar da cewa iyalan za su kiyaye tare da daukaka martabar Comrade Abdullahi Koli, ta hanyar girmama manufofin da ya tsaya kai da fata a kansu a lokacin rayuwarsa.

​Daga karshe, Dr. Bala Wunti ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya jikan marigayin da rahama, ya ba shi masaukai na kwarai, sannan ya ba iyalan hakuri da jure wannan babban rashi.

​Abubakar Al-Sadique, Babban Jami’in Sadarwa, Kungiyar Tallafawa Bala Wunti (Bala Wunti Support Organisation), 06/04/2026

Want your business to be the top-listed Government Service in Bauchi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Bauchi