26/02/2026
Tausayi Sadaukarwa Jinkan Alumma Taimakon Alumma kyautatawa Alumma Domin su samu Farin ciki Da Annashuwa
A zukatan Su Ba dare ba Rana Duk
Wannan Aikin Al-khairi Duk Halin Dr Bala Maijama,a Wunti ne Bashi da wani Buri koh wata Bukata samada Bukatar Alumma Marasa Karfi da marasa Galihu Harda masu Galihun ma Dr Bala Maijama,a Wunti
Allah ka tabbatar mana da Nasara 227
26/02/2026
Big shout out to my newest top fans! Ali Babangida Giade, Alh Ibrahim Isah
12/10/2025
"Dr Bala Wunti Ka Amsa Kiran Mu Kayi Takarar Gwamnan Bauchi" - Sako Daga Karamar Hukumar Ningi
An gudanar da gagarumin taro a garin Ningi domin kiran Dr. Bala Wunti, da ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Taron, wanda Ko’odinetan Bala Wunti na ƙaramar hukumar Alhaji Bala Somebody, ya shirya ya gudana ne a M.U.K dake Ningi ranar Juma’a.
Alh Bala ya bayyana cewa manufar taron shine haɗa kai da jawo hankalin al’umma domin su mara baya ga Dr. Bala Wunti wajen samun nasarar tsayawa takarar gwamna a 2027.
A jawabinsa, Sa’in Tiffi, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar Bala Wunti a ƙaramar hukumar Ningi, ya yi karin bayani kan dalilan da suka sa suka kuduri aniyar ganin an samu shugaba nagari da kwarewa a tafiyar da al’amuran jihar.
Haka zalika, wakilan Dr. Bala Wunti daga fadar jiha sun halarci taron, inda Alhaji Abba M. Inuwa ya gabatar da jawabi a madadin tawagar, yana mai yabawa da yadda jama’ar Ningi ke nuna cikakken goyon baya da kauna ga Dr. Bala Wunti.
Taron ya sami halartar bangarori daban-daban na al’umma, ciki har da kungiyoyin matasa da na mata.
Abubakar M. Abubakar ya gabatar da jawabi a madadin matasa, inda ya jaddada cewa matasa na da rawar gani wajen tabbatar da nasarar wannan tafiya.
Haka kuma, Hajiya Zulai Mamuda daga bangaren mata ta yi jawabi, tana mai cewa mata za su kasance a sahun gaba wajen tallafawa wannan tafiya mai albarka.
Manufar taron gaba ɗaya ita ce tabbatar da cewa ƙaramar hukumar Ningi ta tsaya tsayin daka wajen bayar da gudunmawa ga jam’iyyar APC, tare da tabbatar da turbar shugabanci mai inganci da dorewa a jihar Bauchi.
Oga Habu Umar Umb Bauchi Bala Wunti Youths Movement Bauchi
02/10/2025
*Happy Birthday to our Esteemed DG, Bala Wunti of Focus Media! 🎉🥳*
On this special day, we celebrate a visionary leader and a man of great honor. May Almighty Allah continue to bless you with good health, wisdom, and countless years filled with success and happiness.
We pray that Allah (SWT) increases your years with abundant barakah, guides your steps, and grants you greater achievements in both your personal and professional journey.
May Allah also support and uplift *Abba Bala Wunti,* granting him the opportunity and success to become the Governor of Bauchi State, so he can serve our people with justice, wisdom, and progress.
Wishing you many more fruitful years ahead, Sir. *Happy Birthday once again! 🎂✨*
02/10/2025
Happy Birthday Message Dedicated to My Mentor and Father, Dr. Bala Maijama’a Wunti
Alhamdulillah! Yau rana ce ta musamman a cikin rayuwata, ranar da nake tunawa da zagayowar haihuwata. Amma ban ɗauki wannan rana a matsayin ta kaina kawai ba, saboda na sadaukar da ita gaba ɗaya ga mutumin da ya zamo silar canji da nasara a cikin rayuwata — Ubangiji ya kaddara ya taimakeni da shi a lokacin da babu kowa a bangarena, lokacin da rayuwa ta yi min kunci, kuma nake bukatar agajin gaggawa. Allah ya azurta ni da wannan kyauta ta musamman, wato Dr. Bala Maijama’a Wunti.
Shi ne limamin canji da nasara a rayuwata, kuma a yau shi ne abin alfahari ga al’ummar Jihar Bauchi, wadanda suke yi masa addu’a da fatan ganin ya zamo Gwamnan Jihar Bauchi a shekarar 2027, in sha Allah.
Yau kuma shine karo na farko a rayuwata da na taɓa yiwa kaina fatan Happy Birthday, kuma ban yi hakan ba saboda kaina, sai don in nuna girmamawa da karramawa ta musamman ga Abbana, Jagora na, kuma kwarin gwiwa na, Dr. Bala Maijama’a Wunti.
Ya Allah, Ka tsawaita rayuwar Abbana Dr. Bala Wunti cikin lafiya da albarka, Ka ba shi ikon ci gaba da jagorantar al’umma zuwa ga cigaba, haɗin kai da nasara. Ka cika masa burinsa na alheri, Ka kare shi daga dukkan sharri, Ka ba shi ikon zama abin alfahari ga Bauchi da Najeriya baki ɗaya.
Allah Ka amsa addu’armu.
Happy Birthday to me – dedicated to my Father and Mentor, Dr. Bala Maijama’a Wunti.