03/10/2026
MAULIDIN ANNABI MUHAMMADU ﷺ
An gudanar da Maulidin Annabi Muhammadu ﷺ a garin Badara, Kirfi LGA, Jihar Bauchi, a Zawiyar Sheikh Muhammad Bello Arabi Badara.
An gudanar da taron ne cikin yanayi na tunawa da rayuwa da koyarwar Manzon Allah Muhammadu ﷺ, tare da gabatar da wa'azi da nasihohi na addini.
Malamai Masu Wa'azi
Taron ya samu halartar malamai mata da s**a gabatar da wa'azi, daga cikinsu akwai:
Sayyada Mubaraka
Sayyada Hajara
Sayyada Zakiya
Sayyada Aisha
An yi addu'o'i da fatan Allah Ya karɓi ibadu, Ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah Muhammadu ﷺ, Ya kuma sa albarkar wannan Maulidi ta tabbata ga al'ummar Musulmi baki ɗaya.
Allah ka barmu da Manzon Allah ﷺ.