01/10/2026
SAKON RANAR ’YANCIN KAI TA NIGERIA 🇳🇬
A wannan rana ta musamman, ina miƙa saƙon gaisuwa da fatan alheri ga daukacin al’ummar Najeriya, musamman al’ummar Masarautar Dass.
A matsayinmu na al’umma mai ɗimbin ƙabilu, addinai da al’adu, abin da ya kamata ya haɗa mu ya fi abin da zai raba mu muhimmanci. Bambancinmu ba rauni ba ne; dama ce da za mu yi amfani da ita wajen gina ƙasa mai ƙarfi, adalci da ci gaba.
Ina kira ga Alumma da mu sanya haɗin kan Najeriya a gaba, mu guji duk wani abu da zai rura ƙiyayya ko rarrabuwar kai, mu mutunta juna, mu zauna lafiya, kuma mu taimaki juna ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko yanki ba.
Najeriya tamu ce baki ɗaya. Makomarta kuma tana hannunmu baki ɗaya. Idan muka tsaya tare, muka fahimci juna, muka girmama bambance-bambancenmu, za mu iya gina kyakkyawar makoma ga yaranmu da waɗanda za su zo bayanmu.
Ina addu’ar Allah Ya ƙara haɗa kan al’ummar Najeriya, Ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa, Ya azurta shugabanninmu da hikima da adalci, sannan Ya albarkaci ƙasarmu da ci gaba da wadata.
Allah Ya ƙara wa Najeriya zaman lafiya, haɗin kai da ɗaukaka.
Ran Sarki Ya Dade.
— Mai Martaba Sarkin Dass
Alh Usman Bilyaminu Othman II
(Mai Dutsen Mbula)