Muryar Matasan Yobe

Muryar Matasan Yobe

Share

Tafiyace ta Mai dauke da muryar Al ummar yobe musamman Matasa da masu Kana nan karfi

21/10/2025

Duk yadda za kayi da jaki sai ya ci kara !!!

Malam Bahaushe yayi gaskia da yace: Gwano ba ya jin warin jikinsa!

Yanzu kai tsabar rashin kunya irin ta ɗan IZALA, duk makauniyar soyayya da biyayya da kuke yiwa Ibnu Tamiyyah da Ɗan Abdulwahhabi, Bin Baz, Ibn Uthaimeen, Albany Bature, ba muce kunyi wa Annabi صلى الله عليه وسلم kishiya ba, sai mu zaku tuhuma da haka!??

Toh Bari in ɗan gutsuro maka wasu maganganun Shirka (kamar yadda kuke faɗa) da Taƙiyyuddini Addaƙuƙy yayi cikin wasu baitocin ta’aziyya da ya rubuta wa ma’asumin ku Ahmad ibn Taimiyyah randa ya mutu:

Ka duba (العقود الدرية في مناقب شيخ الاسلام ابن تيمية)

Yana cewa akan ibnu Taimiyyah:

يا ‎واحد الدنيا الذي بعلومه ** يمتاز في الإسلام كل موحد

“ Ya kai tilo makaɗaicin duniya wanda da ilimominshi ne kowani mai kaɗaita ALLAH yake banbantuwa a Musulunci”

‎يا حامل الأعباء عن مستنصر ** يا كاشف الغماء عن مستنجد

“ Ya mai ɗauke nauyoyi ga mai neman taimako, Ya mai yaye baƙin ciki ga duk mai neman ɗauki”

Har yazo inda yake cewa:

‎يا خاتم العلماء صح بموتك ال ** خبر الذي يرويه كل مجود

Ya kai cika makin Malamai: Lallai akan mutuwar ka ne hadisin ɗauke ilimin da ko wani mahaddacin Hadisi yake rawaita, ya tabbata”

‎اليوم قبض العلم قولا واحدا ** من غير ما منع وغير تردد

“A Yau ranar mutuwar ka, tabbas ɗauke Ilimi a doron ƙasa ya tabbata, babu makawa babu shakka”

‎لو لم يكن ختم الأئمة أحمد ** بشرت أهل الخافقين بأحمد

“ ba dan Ahmad (Annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم ???) ya kasance cika makin limamai ba, da na yiwa mutanen gabas da yamna albishir da Ahmad (ibn Taimiyya)

يا من يروم له عديلا في الوري * قد رمت كالعنقاء مالم يوجد

“ Ya kai mai neman na biyun Ibnu Taimiyya a halitta, ka sani kamar kana neman tsuntsun (Anƙa’u) ne, dan ba’a halicci tsuntsun bama tukunna” !!

Kai yanzu da ace waɗannan naganganun sufaye ne s**a yabi Annabi صلى الله عليه وسلم dasu, da tuni kun fidda su daga musulunci, b***e kuma ace Shehu Ahmadu Tijjani ko Shehu Ibrahim inyass ko Sidi Abdulƙadir Jailani s**a yaba dasu !!!

Ga kashi a gindinku baku ji warin shi ba, sai na sufaye saboda tsabar ƙiyayyar bayin ALLAH da ta cika zukatan ku !!!

Imam Hassan Sheikh Dahiru Bauchi

30/09/2025

Dan Allah Anemomin Wanda Yayi Wannan Wakar Inada Tukuici Mekarfi Nide Agurina Yafi Limaman Yan Izala irinsu Lawan Turamol

29/09/2025

Kaji Masoya Annabi Na Gaske 💪💪

29/09/2025

idan Kun Zabeshi Allah Yatsinemuku Kaji Ana Maganar Annabi Suna Maganar zabe Mara Kunya

28/09/2025

“Rijiyar lemo”! ya faɗi babu nauyi wajen ganin sai ya kare “triumph”! ya juyawa Annabi baya‚ dana saurari jawabinsa sai na fahimci bema fahimci inda aka nausa ba‚ mufa abinda muke tuhumar “triumph“! shine ya munana ladabi ga Annabi (SalLalLahu ALaiHi wasalLam) kai kuma ka ɗauki mas’alar kaciya da kwalli kace babu wani hadithi daya inganta kan wannan mas'alar‚ haba prof! bari mu ɗan tsakura maku kaɗan, acikin ɗabaƙatul~kubra na Ibnu Sa'ad yana ruwaitowa wanda isnadinsa ya dangana ga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib yace

ﻭﻟﺪ ﺍﻟﻨﺒﻲ صلى الله عليه وسلم ﻣﺨﺘﻮﻧﺎ ﻣﺴﺮﻭﺭﺍ

An haifi Annabi ((SalLalLaHu ALaiHi wasalLam)) mai kaciya kuma mai yankakkiyar cibiya.

Ɗabaƙatul~kubra 1/212

Shi kansa ibnu Sa'ad da ya zo bayyana matsayin hadithin sai da yace (بإسناد صحيح) saboda ingancin hadithin sannan shima kwallin da shi aka haife shi kamar yadda riwaya ta tabbatar cikin jãmi'uttirmidhy daga jãbir ɗan samura:

ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﻨﻴﻊ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﺎﺩ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﻮﺍﻡ
ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﺍﻟﺤﺠﺎﺝ ﻋﻦ ﺳﻤﺎﻙ ﺑﻦ ﺣﺮﺏ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﺳﻤﺮﺓ
ﻗﺎﻝ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺳﺎﻗﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ خموﺷﺔ ﻭﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﻀﺤﻚ ﺇﻻ ﺗﺒﺴﻤﺎ ﻭﻛﻨﺖ ﺇﺫﺍ ﻧﻈﺮﺕ ﺇﻟﻴﻪ
ﻗﻠﺖ ﺃﻛﺤﻞ ﺍﻟﻌﻴﻨﻴﻦ ﻭﻟﻴﺲ ﺑﺄﻛﺤﻞ

Jãbir ɗan samuratu yace a ƙwabrin Manzon Allah SalLalLahu ALaiHi wasalLam akwai wani shãfi, yakasance baya dariya saidai murmushi‚ na kasance idan zan kalle shi zance mai kwalli a idanuwa ba tare da ya saka kwalli ba.

Jãmi'uttirmidhy: 3645

tirmidhy kansa da yazo bayyana hadithin sai yace هذا حديث حسن صحيح غريب tare da cewa isɗilãhin malaman musɗalahal Hadith mafi rinjaye idan tirmidhy ya ambaci haka a hadithi to abinda yake nufi hadithine ingattacce amma ba'a ruwaito shi ta fuska mabanbanta ba.

Abdullahi Malam Adamu

25/09/2025

Duk Wanda Ya Shuka Alkairi, Tabbas Zai ga Alkairi.

Alhaji Tonga Betara Ya Samu Kyakkyawan Shaida agun Al'ummar Jihar Yobe bayan Kammala aikin sa a Matsayin Shugaban Ma'aikatar Jihar Yobe (Head Of Service).

hakan Yana nuni da Cewa Yayi amfani bisa damar da Allah ya bashi a cikin kankanin lokacin don ganin cewa Ya'yan Talakawa Sun Samu aikin Gwamnati a dukkanin Fadin Jihar Yobe. Hakika ya Shiga tarihin Ma'aikatar Jihar Yobe Wanda baza'a Manta dashi ba.

Ire-irensu Allah baya barinsu a Kasa, Muna rokon Allah ya kawo masa Wani Matsayin da baiyi Tsammani ba. Wanda kuma ya gajeshi a Matsayin Shugaban Ma'aikatar Jihar Yobe Mai Suna Alhaji Abdullahi Musa Shehu, Allah Yabashi ikon Kawo Cigaba Wajen Samar da aiki Fiye da na Alhaji Tonga Betara.

Want your business to be the top-listed Government Service in Damaturu?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Nasarawa Bututu
Damaturu