CMC TV Hausa

CMC TV Hausa

Share

🟢 BARKA DA ZUWA CMC TV HAUSA! CMC TV Hausa — Muryar Gaskiya

Muna maraba da zuwanka zuwa tashar CMC TV Hausa — gida ne na labarai na gaskiya, shirye-shirye masu ilmantarwa da nishadantarwa, da rahotanni masu zurfin bincike a harshen Hausa.

25/05/2026

Tuna Baya: Lokaci da Tsohon Gwamnan Kaduna Mal. Nasir Ahmad El rufa'i yake Jawabin ban kwana akan mulkin Jihar Kaduna da Kuma yadda s**a marawa Tinubu baya yayi nasara a zaben 2023.

24/05/2026

Jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Wasila Isma'il ta rasu, k**ar yadda makusantanta s**a tabbatar.

Makusantan marigayiyar sun ce ta rasu ne a jihar Kaduna da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya, inda ta bar ƴaƴa hudu - mata uku da namiji ɗaya.

01/05/2026

Barka da ranar Jumu'a...

Ku aika da sunayen mutanen da kuke so a gaisar muku da su cikin shirin Ranar Jumu'a na CMC TV.

Mu hadu a sashin comment

05/04/2026

GOOD MORNING AL'UMMAN KARAMAR HUKUMAR LERE

DA WANE DAN SIYASA KUKE SO MU FARA TATTAUNAWA CIKIN SABON SHIRINMU NA SIYASA RIGAR YANCI ?

Photos from KHM TV Hausa's post 23/03/2026
11/11/2025

CMC HAUSA NA NEMAN MA’AIKATA

Hukumar CMC HAUSA tana sanar da bude guraben aiki a wadannan muk**ai:

1. Managing Director (Shugaban Masu Gudanarwa)
2. Editor Director (Daraktan Tace Rubutu da Hotuna/Editing)
3. Director Reporter (Daraktan Rahoto / Mai Kawo Labarai)

Masu sha’awar wannan aiki su tura aikace-aikacensu zuwa:

Email: [[email protected]](mailto:[email protected])

Ana maraba da mutanen da ke da kwarewa, jajircewa da kwazo.

04/10/2025

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ba zai taɓa mantawa da ranar da aka sace ɗaliban makarantar sakandaren mata ta Chibok a jihar Borno ba.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taro da aka shirya a Abuja, inda ya ce har yanzu lamarin na daga cikin abubuwan da s**a fi girgiza shi a lokacin da yake mulki.

29/09/2025

Na yafe wa duk wadanda s**a ci amanar miji na - Oluremi Tinubu

CMC TV HAUSA

Photos from CMC TV HAUSA's post 29/09/2025

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya sauke kwamishiniyar mata ta jihar Zainab Baban Takko

Sanawar da gwamnatin Jihar ta fitar ba ta bayyana dalilin daukar mataki ba, amma ta kira matakin a matsayin wani dan gyara da aka yi a majalisar zartaswar jihar kuma ta ce mataki ne da ya fara aiki nan take.

Photos from CMC TV HAUSA's post 27/09/2025

Jahar Kano da mutanen jahar Matsalar Yan Daba da Rashin Tsaro ne Babbar Matsalar mu ba Maganan Triump ya Zagi Annabi ba — Sheikh Gadon Ƙaya

Shehin Addinin Musulunci, Sheikh Gado Kaya ya bayyana bacin ransa ganin yadda gwamnatin jihar Kano ta dage sai ta k**a Sheikh Lawan Triumph wanda ake zargi da cin mutuncin Annabi Muhammad.

“Son a k**a Malam Lawan Triumph da wasu ke yi ba abu ne mai kyau ba, wannan sa'insar tsakanin mu da yan Darika da yan Bidia ba yau muka fara.

“Abu ne wanda dama can ana yi dan haka muke fadawa Gwamnati datai kokari ta cire hannun ta kan wannan magana idan abu yazo na Addini a bari hujja tai aiki.

“Bama so Gwamnati ta janyo wata fitinar bayan wacce muke ciki, shi isa muke rokon Gwamnatin Kano ta janye hannun ta kan lamarin Malam Lawan Triumph.” ~ inji Sheikh Abdallah Gadon Kaya

Want your business to be the top-listed Government Service in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kaduna
24