28/04/2026
DA DUMI-DUMI: Hon. Muhammad Sani Lawal Ya Bayyana Niyyar Tsayawa Takarar Majalisar Jihar Katsina a Funtua
A yau ne,Hon.Muhammad Sani Lawal ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Katsina, domin wakiltar Ƙaramar Hukumar Funtua, a hukumance karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Hon. Muhammad Sani Lawal, wanda matashi ne jajirtacce, ya shahara wajen tsayuwa kan al’amuran jama’a, musamman ta fuskar tallafawa marasa galihu, marayu da marasa lafiya.
Hakazalika, yana da burin ganin matasa sun samu ingantacciyar rayuwa ta hanyar samar musu da ayyukan yi da kuma gina makomarsu domin ci gaban Ƙaramar Hukumar Funtua.
Wasu daga cikin matasa sun bayyana goyon bayansu ga takararsa, tare da kira ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Funtua da su fito su mara masa baya domin samun nagartaccen wakilci da ingantaccen shugabanci.
Sun kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, idan aka ba shi dama, zai kawo ci gaba mai ma’ana ga yankin.
Sponsored..

14/06/2025
13/06/2025