22/10/2026
HUKUMAR HISBAH TA ƘARAMAR HUKUMAR BADE, JIHAR YOBE, TA KAI ZIYARAR AIKI ZUWA HURA, ƊAYA DAGA CIKIN WURAREN DA AKE TA’AMULI DA KAYAN MAYE, A BAYAN GADA, GASHUA
A yau Alhamis, 11-Jumada Al-Ula-1448H, wanda ya yi daidai da 22-October-2026M, Hukumar Hisbah ta Ƙaramar Hukumar Bade, Jihar Yobe, ƙarƙashin jagorancin Ass. Prof. Yahuza Hamza Abubakar, Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Yobe, da Dr. Muhammad Yawudi Kaleh, Kwamandan Hisbah na Jihar Yobe, ta kai ziyarar aiki zuwa Hura, da ke bayan Gada a garin Gashua, domin yi wa masu dandalin nasiha da jan hankalinsu kan illolin ta’amuli da kayan maye da kuma muhimmancin komawa ga kyawawan ɗabi’u.
Tawagar ta samu wakilcin Sheikh Isa Ibrahim Gashua, Mataimakin Kwamandan Hisbah na Zone C, tare da Imam Hammad Muhammad Jinjiri Gashua, Kwamandan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Bade, da Mal. Audu Jawi Kachallah (Kaigama), Shugaban Tsaro na Hisbah a Ƙaramar Hukumar Jakusko, tare da sauran jami’an hukumar.
A yayin ziyarar, Imam Hammad Muhammad Jinjiri Gashua ya yi nasiha mai ratsa zuciya ga mazauna wajen, maza da mata, inda ya yi kira gare su da su ji tsoron Allah Maɗaukakin Sarki, su guji shaye-shaye da ta’amuli da kayan maye, tare da kiyaye lokutan salloli da gudanar da su a kan lokaci.
Haka kuma, ya jaddada cewa ƙofar hukumar a buɗe take domin taimaka wa masu buƙatar sana’a ko aikin yi. Ya kuma bayyana aniyar taimakawa wajen sasanta waɗanda s**a samu matsala da iyayensu, domin su samu damar gyara rayuwarsu da komawa cikin al’umma cikin kyakkyawan hali.
Daga bisani, Sheikh Isa Ibrahim Gashua ya ƙara jan hankalin mazauna wajen da su taimaki kansu ta hanyar barin shaye-shaye da sauran munanan halaye, tare da komawa ga Allah da kyautata ayyukansu. Haka kuma, ya yi kira ga shugabannin yankin da su bayar da cikakken haɗin kai wajen ƙoƙarin gyara rayuwar al’ummar wajen. Ya kuma tunatar da kowa muhimmancin tsoron Allah da ranar da kowa zai tsaya a gabansa domin hisabi kan ayyukan da ya aikata a duniya.
A nasa jawabin, ɗaya daga cikin shugabannin mazauna wajen ya nuna godiya a madadin sauran jama’arsa bisa wannan ziyara da nasiha da aka yi musu. Ya bayyana cewa rashin aikin yi da ƙarancin hanyoyin samun abin dogaro da kai na daga cikin matsalolin da s**a taimaka wajen jefa wasu cikin irin wannan rayuwa. Ya kuma bayyana fatansu na ganin Gwamnati da Hukumar Hisbah sun taimaka wajen samar musu da sana’o’i da hanyoyin samun abin dogaro da kai, domin su samu damar inganta rayuwarsu.
Wannan ziyara na daga cikin muhimman ayyukan Hukumar Hisbah na umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, domin wayar da kan al’umma, gyara halaye, yaɗa kyawawan ɗabi’u da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kyakkyawar rayuwa a cikin al’umma.
A ƙarshe, muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya shiryar da al’ummarmu baki ɗaya, Ya kawar da munanan halaye, Ya sauƙaƙa wa masu buƙata, Ya kuma ba kowa ikon komawa gare Shi da kyakkyawar niyya da aikata ayyukan alheri. Amin.
Sibawaihi Ukasha Gashua
Hisbah Media Team, Bade Command