16/09/2026
15th September, 2026
OFFICE OF THE RENEWED HOPE AMBASSADOR
GOMBE STATE
Hon. (Dr.) Aishatu Jibril Dukku (Gimbiyar Dukku), Former Minister of Education and Ambassador, Renewed Hope Initiatives Gombe State, ta raka Gwamnan Jihar Gombe, His Excellency Muhammadu Inuwa Yahaya CON, zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, Aso Rock Villa, Abuja, domin gabatar wa Mai Girma Uwar Gidan Shugaban Ƙasa, Senator Oluremi Tinubu, da Maryam Ibrahim Dan’azumi, wadda ta yi fice a gasar karatun Al-Qur’ani ta ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Makkah, Saudi Arabia.
A yayin taron, Mai Girma Uwar Gidan Shugaban Ƙasa, Senator Oluremi Tinubu, ta yaba matuƙa da hazaka da ƙwazon Maryam Ibrahim Dan’azumi, tana mai bayyana nasarar da ta samu a matsayin abin alfahari da ƙarin ɗaukaka ga Najeriya.
Ta kuma shawarci Maryam da ta yi koyi da manyan mata ‘yan Najeriya da s**a yi fice a duniya, ciki har da Haj. Amina J. Mohammed, UN Deputy Secretary-General, da Hon. (Dr.) Aishatu Jibril Dukku, tsohuwar Ministar Ilimi kuma tsohuwar ‘yar Majalisar Tarayya.
A madadin Shirin Renewed Hope Initiatives na Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu GCFR, Senator Oluremi Tinubu ta ba Maryam Ibrahim Dan’azumi kyautar tallafin kuɗi na Naira Miliyan Ashirin (₦20,000,000.00), domin ƙarfafa mata gwiwa da ci gaba da jajircewa wajen neman ilimi da kare martabar Najeriya.
A wannan ziyarar, Gwamnan Jihar Gombe, His Excellency Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya samu rakiyar matarsa, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya; Uwargidan ɗan takarar Gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar APC, Dr. Zainab Jamil Gwamna; Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dr. Aishatu Umar Maigari; Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, Dr. Bertha Danja; Mai Baiwa Gwamnan Shawara kan Harkokin Tsangayu, Sayyada Amina Shaikh Dahiru Bauchi; iyayen Maryam; da kuma shugabannin gudanarwar makarantar.
KABIRU ABIDOKA HASHIDU
(Dan Lawan Hashidu)