29/09/2026
Tijjani Grassroots Mobilization and Empowerment Initiative of Nigeria Zamfara State chapter
Ta Bayyana Shirye-shiryenta Na Tallafa Wa Al’umma
Gusau, Zamfara State —
Ƙungiyar Tijjani Grassroots Mobilization and Empowerment Initiative of Nigeria ta bayyana aniyarta na ƙarfafa matasa, mata da sauran masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar shirye-shiryen tallafi da bunƙasa rayuwar al’umma.
A wata tattaunawa ta Hard Talk, ƙungiyar ta fuskanci tambayoyi kan manufar kafuwarta, ayyukan da take gudanarwa da kuma irin tasirin da take son samarwa a matakin ƙasa.
Daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna akwai yadda ƙungiyar ke zaɓar waɗanda za su amfana da shirye-shiryen empowerment, da kuma matakan da take ɗauka domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen rarraba tallafi.
Haka kuma, an tambayi ƙungiyar kan dangantakarta da harkokin siyasa, musamman yadda za ta tabbatar da cewa ayyukan tallafawa al’umma ba su zama hanyar neman kuri’u ko amfani da buƙatun jama'a wajen siyasa ba.
Ƙungiyar ta kuma fuskanci tambayoyi kan tushen kuɗaɗen gudanar da ayyukanta, yadda take tantance nasarar shirye-shiryenta da kuma irin matakan da take da su wajen faɗaɗa ayyukan zuwa ƙarin al’ummomi.
Masu gudanar da shirin sun jaddada muhimmancin ƙarfafa matasa da mata, samar da damar dogaro da kai da kuma kai ayyukan ci gaba zuwa matakin grassroots, inda s**a bayyana cewa burinsu shi ne ganin an samu sauyi mai dorewa a rayuwar al’umma.
YUSAN TV — Labarai Masu Inganci, Sahihai kuma Amintattu.