03/10/2026
TIRKASHI: “Rayuwata Na Cikin Hatsari A Gidan Yarin Da Nake Tsare, Alkalin Alkalan Najeriya Ka Kawo Min Dauki” — Sheikh Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, wanda ke tsare a Maximum Security Custodial Centre da ke Janguza, Kano, ya roki Babban Alkalin Najeriya (CJN) da ya kawo masa daukin gaggawa, yana mai cewa rayuwarsa na cikin hatsari a gidan yarin da yake tsare.
Kabara ya bayyana hakan ne cikin wata takarda mai kwanan wata 30 ga Satumba, 2026, wadda ya aikewa Babban Alkalin Najeriya dangane da karar Appeal No. CA/KN/01/2025, Suit No. K/93CA/2022, tsakanin shi da Gwamnatin Jihar Kano.
A cikin takardar, Kabara ya ce yana fuskantar abin da ya bayyana a matsayin “mugun hadari”, yana mai cewa akwai yunkurin aikata wasu abubuwa da ka iya jefa rayuwarsa cikin hadari.
Ya kuma yi ikirarin cewa ana kokarin “kagamin sabon laifi” wanda ya ce zai fi laifin da aka same shi da shi a baya, inda ya ambaci batun Blasphemy.
Kabara ya kuma ja hankalin CJN kan shari’ar tasa, yana mai cewa lauyoyi sun yi adoption na karar a ranar 29 ga Yuni, 2026, kuma tun daga wannan lokaci yake jiran hukuncin kotun.
A wani bangare na takardar, ya ce wasu muhimman takardu da ya gabatar a lokacin shari’ar a Upper Sharia Court, Kofar Kudu, ciki har da Exhibits “M”, “N”, “O”, “P”, “R” da “S”, ba sa cikin takardun da aka yi adoption a ranar 29 ga Yuni, 2026.
Haka kuma, Kabara ya bayyana wasu abubuwan da ya ce sun faru a kwanakin baya, ciki har da abin da ya kira wani shiri na shigar da shi cikin rikicin Niger Delta, da kuma wani yunkuri da ya ce an yi na mayar da shari’arsa hannun Majalisar Dinkin Duniya (United Nations) maimakon a yanke hukuncin da yake jira.
A karshe, Sheikh Abduljabbar Kabara ya roki Babban Alkalin Najeriya da ya duba korafinsa tare da daukar matakin da ya dace, yana mai cewa: “Allah ya taimaki Shari’a, ya yi jagora ga Chief Justice of Nigeria wajen sauke wannan nauyi da na gabatar mata.”
Rahoton ya dogara ne kan abin da ke cikin takardar da Sheikh Abduljabbar Kabara ya aikewa CJN; zarge-zargen da ke cikinta ba a tabbatar da su a cikin takardar da aka gabatar ba