Al,azkar FIL kitabullahi wassunnah

Al,azkar FIL kitabullahi wassunnah

Share

FORTRESS OF THE MUSLIM
Invocations from the Qur'an and Sunnah

12/04/2018

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
"
Shugaban Kungiyar Reshen Karamar Hukumar Sabuwa,
. Abdullahi Ya'u Aska Sabuwa
"
Shugaban Majalisar Malamai,
. Bello Uthman Sabuwa.
"
Shugaban Rundunar Agaji,
. Musa Dugun-Mu'azu
"
Amadadin kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'ikamatis-Sunnah Reshen Karamar Hukumar
Sabuwa ta Jihar Katsina.
-
Suke farin cikin gayyatar 'Yan uwa Musulmai zuwa gaggarumin 'AZI wanda KUNGIYAR tashirya Zata gudanar kamar haka:-
"
Gari:- Maichaki, Maichaki Detachment
'
Rana:- Jumu'a 2
26/07/1439AH _Friday 13/04/2018CE
'
Lokaci:- 2:30pm-Zuwa 5:30pm
"
MALAMAI MASU WA'AZI
1) Mal. Hamza Sa'eed Daga kwamitin Matasa
2) Mal. Imam Yusuf Abdullahi U/Madugu
3) Mal. Abdulkarim M/Maigora.
4) Mal. Abdurrashid Abdullahi.
"
ALARAMMOMI
1) Alaramma Ibrahim Isma'il M/Bakko
2) Alaramma Anas Shu'aybu.
3) Alaramma Abubakar Haruna Machika.
4) Alaramma Musa D/Muazu.
"
Muna roko Ayi sallar Jumu'a acan
"
ALLAH (T) YA BADA IKON HALARTA AMIN
"
Sanarwa:- Daga Sakataren Kungiya
Alh. Faruoq Hayatu.
"
© Copyright
JIBWIS SOCIAL MEDIA COMMITTEE
SABUWA
25/Rajab/1439
12/April/2018

10/03/2016

(( INVOCATION IN TIMES OF WORRY AND GRIEF ))
"

اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ، ابْنُ عَبْدِكَ، ابْنُ أَمَتِكَ، نَاصِيَتِي بِيَدِكَ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاءُكَ، أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ، سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ، أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَداً مِنْ خَلْقِكَ، أَوِ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ، أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي، وَنُورَ صَدْرِي، وَجَلاءَ حُزْنِي، وَذَهَابَ هَمِّي

120. Allaahumma 'innee 'abduka, ibnu 'abdika, ibnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'awista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa thahaaba hammee .

O Allaah, I am Your slave and the son of Your male slave and the son of your female slave. My forehead is in Your Hand (i.e. you have control over me). Your Judgment upon me is assured and Your Decree concerning me is just. I ask You by every Name that You have named Yourself with, revealed in Your Book, taught any one of Your creation or kept unto Yourself in the knowledge of the unseen that is with You, to make the Qur'an the spring of my heart, and the light of my chest, the banisher of my sadness and the reliever of my distress.

07/01/2016

(( INVOCATION FOR WHEN ENTERING A MARKET ))
"
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَشَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ حَيٌّ لاَ يَمُوتُ، بِيَدِهِ الْخَيْرُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
"
209. Laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, yuhyee wa yumeetu, wa Huwa hayyun laa yamootu, biyadihil-khayru, wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer.
"
None has the right to be worshipped but Allaah alone, Who has no partner. His is the dominion and His is the praise. He brings life and He causes death, and He is living and does not die. In His Hand is all good, and He is Able to do all things.

22/10/2015

KADA KA WUCE / YI HAQURI KA TSAYA,
KA KARANTA..
"
"
DA FARKO DAI....
Ina so ku sani Cewa.......
ADDININ MUSULICI / YANA TAFIYA NE DA
JAGORANCI...
"
Wannan Kenan,,,
"
"
'YAN-UWA / LALLAI NA FAHIMCI
CEWA......
"
QASA TA, TA ( NIGERIA ).....
Tana daya Daga Cikin Qasashen Duniya, da
ake yawan Samun (Sa6ani) Da (Rikici) mai
Zafi / akan Mas'alar Gudanar da wata
Ibadah Mai ayyanannen Lokaci...
"
MISALA KAMAR HAKA...
* azumin watan ramadan-
* azumin Sittu Shawwal-
* Azumin Ranar Arafah-
* Azumin Tasu'a, Da A'shurah
* Babbar sallah da Qaramah...etc..
"
"
BAYAN HAKA...
Jama'ar Musulmi / Sun karkasu Game da
fahimtarsu akan Magance Aukuwar
Wannan Mas'alar.........
"
* WASU SUNA DA RA'AYIN...
Ji, Da bin abinda Shugabanni s**a Zartar...
"
* WASU KUMA....
Suna Ganin Cewa: / Babu haujjar bin
Shugaba, alokacin da S**a Tabbatar da
Ganin (Wata) ko Zuwan wani lokacin Ibada
Ayyananne....
"
* SA'ANNAN KUMA...
Akwai masu Ganin Cewa: / Gwara ma subi
fatawar Malamansu akan Mas'alar,
MISALI: / Idan malaminsu yace musu suyi,
To zasu yi / Idan kuma yace musu,
karsuyi, To baza suyi ba.......
"
* BAYAN HAKA KUMA...
Akwai masu ganin Cewa: / In dai ba
malaminsu ba, To babu Wanda Zai Tsara
musu Doka a addini Subi / Tunda ana sa
Son Zuciya a Jagorancin yau....
"
'YAN-UWA....
Wannan yasa / muke Samun Matsala,
aduk sanda Muka Tashi Gudanar da wata
Ibada mai ayyanannen Lokaci...
"
"
TURQASHI....
Dan-uwa mai Karatu / Ina so ka Sani
Cewa....
"
Wannan Sa6anin fa...
Haka yake Gudana a Birane. Da
Qauyuka...
"
KUMA HAKA YAKE GUDANA...
A Tsakanin Malamanmu, Da marasa
Karatunmu,.
"
KUMA HAR YAU...
An kasa Shawo kan Wannan Mas'alar a
Tsakanin Al-Ummar Musulmai.....
"
KUSAN MA INCE....
Abin Qara yawa yake yi aduk Shekara....
"
ATAQAICE DAI....
'yan-uwa da yawa / Sunji cewa ance a
tashi da Azumi yau...
"
DAGA BISANI KUMA...
Sai s**a ji ance kada ayi azumin (Tasu'ah)
ayau 22/10/2015 miladiyya....
"
GUBE... 23/10/2015 (M) Ce /..
Ranar da Za'a Tashi da ........
(Azumin Tasu'a)
"
"
DAN HAKA...
AQA'IDA TA Musulinci / In dai Sugaban
Musulmai ya bada Sanarwar Ranar da
Za'ayi Azumi, Ko ranar da Za'a Gudanar
da wata Ibadah mai ayyanannen Lokaci /
To ya Zama wajibi akan Musulmai Suyi
masa Biyayya / koda ko suna da yaqini
akan abin da s**a fahimta....
"
DOMIN...
Manzon Allah (s.a.w) yace:
AZUMI, SHINE: RANAR DA MAFIYA YAWA
DAGA CIKIN MUTANE SUKE YIN AZUMI...
"
DAN-HAKA....
Duk wanda ya tashi da azumi yau / Idan
yaga Zai kai azuminsa, To falillahil
hamd....
"
IDAN KUMA..
Zai aje ye ne / To babu Laifi....
"
MUNA ROQON ALLAH (s.w.t)
ya datar damu akan Dai-dai —

15/09/2015

WATAN ZUL- HIJJAH:
Watan Zul - Hijjah shine wata na karshe a
cikin jerin watannin Musulunci, Allah SWT
ya albarkaci watan da falala da alkhairai
masu tarin yawa, wanda ya kunshi ayyuka
kamar:
- Aikin Hajji wanda daya ne daga cikin
rukunan musulunci.
- Ranar Arfa wacce wadanda basu samu
damar zuwa Hajji ba ke samun
tagomashin yin azumi kamar yadda
Sunnah ta tabbatar.
- Kwanaki goma na farkon watan masu
falala, wanda yin aikin kirki a cikin su yafi
fita jihadi.
- Layya wacce Allah ya shar'anta ta akan
mutane tun lokacin Abal Anbiyah Ibrahim
(AS).
- Sallar Idi wacce take da tarin hikimomi a
cikin ta.
Allah ka rabautar damu alkhairan dake
cikin wannan ranaku masu falala.

15/07/2015


"
"
'YAN-UWA-
Ina mai Matuqar Farincikin Gabatar muku
da Wannan Lakcar, Mai Suna Kamar
haka.......

"
"
ZAN GABATAR DA WANNAN LAKCAR/ BA
DON KOMAIBA......
"
"
SAI DAN-
yadda naga Sallar tana Qara Fuskantaru a
'yan-wasu Kwanaki da zasu zo Nan bada
Dadewa ba..
"
"
DAN HAKA-
Muyi haquri mu Karanta Wannan Saqon,
Domin amfanin kanmu da Iyalinmu...
"
"
'YAN-UWA,
KAMAR YADDA NACE-
"
* MECE CE SALLAR-IDI ???
"
"
AMSA-
sallar-idi, / Sallace da ake gabatarda ita a
wani Lokaci Ke6antacce, a wata Siffa
Ke6antacciya, Sau biyu (2) a Shekara....
"
"
'YAN-UWA-
Kafin in kaiga fashin Baqin Wannan Ta'arifi
na Sallar-idi, / bari in gabatar muku da
Tabbatuwan Sallar-idin Tukun.....
"
"
TABBATUWAR SALLAR-IDI,
'YAN-UWA-
Sallolin idi, guda biyu (2) da musulunci
yake da su Sune kamar haka.....
* BABBAR-SALLAH
* QARAMAR- SALLAH
Dukkansu sun Tabbata a Sharia..
"
"
QARAMAR-SALLAH
Qaramar sallah, itace Sallar da ake
gabatarwa, a Ranar daya (1) ga watan-
(( Shawwal )) don Nuna Godiya ga Allah
(s.w.t) akan Baiwar da yayi mana na
Kammala Azumin Watan- (( Ramadan ))...
"
"
'YAN-UWA-
Wannan Sallar ta Tabbata A Cikin Alqur'ani
mai Girma....
Suratul- ( A'ala ) aya ta 14-15 ....
"
"
SANNAN
* imam Bukhariy da-
* imam Muslim bin hajjaj da-
* imam abu Dauda da-
* imam Nasa'i
Sun Rawaito daga ( Jabir ) (r.a) yace: .....
NA HALARCI SALLAR-IDI, TARE DA
MA'AIKIN ALLAH (s.a.w)..
"
"
HAKA SHIMA-
( Bara'u Dan Azib ) (r.a) yace: ...
MANZON ALLAH (s.a.w) yayi mana
huduba a Babban Sallar-idi, / bayan idar
da sallar idin...
"
"
DAN-HAKA-
Ataqaicen-Taqaitawa, Sallar idi, Sunnah ce
mai Qarfi...
"
"
SA'ANNA-
maza, da mata, / yaro, da Babba,
Harta mata masu yin ( Al'ada ) suma
Anbasu Izinin Zuwa Masallacin idi, Domin
Nuna Farinciki da Godiya Ga Allah (s.w.t)
"
"
TAMBAYA
MENE NE LADUBBAN ZUWA SALLAR-
IDI, ???
"
"
AMSA-
YANA DAGA CIKIN LADUBBAN ZUWA
MASALLACIN IDI, KAMAR HAKA....
* Ana so kaci abinci kafin ka tafi
masallacin-idi,/ amma a Qaramar-sallah
* Ana so ka Sanya Sabon kaya, idan kana
da iko,
* Ana so kafito Tsaf-tsaf, ka sanya Turare
* Ana so ka dinga yin wannan zikirin a
hanyarka ta Zuwa masallacin Idi, GASU
KAMR HAKA..
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
LA,ILAHA ILLALLAH
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
WALILLAHIL-HAMDU
anso kadiga maimaitawa har sai kaje
masallacin idin
* sallar-ida, / Ba'a yi mata Nafila, saidai
Tahiyyatul-masjid, shima sai in ka samu
Wuri a Cikin masallaci
AMMA'
Idan baka sami wuri a cikin masallaci ba,/
to Babu wata Nafila da Zaka yi, zaka zauna
ne kawai a harabar Masallaci ba tare da
yin Nafilaba
* Ana so ka Tsaya bayan an kammala
Sallar idi,/ Domin sauraren
(( Kudubah )) .....
"
"
'YAN-UWA-
WANNAN SHINE SAQON DA NIKE SO IN
KAWO MUKU

15/05/2015

HAKKIN MAKOCI.

Manzon Allah saw. Yace :

A. bazai shiga Aljannah ba. Wanda makocinsa bai Aminta daga cutar sa ba.

B. Jibrilu bai gushe ba. Yanayi mini wasiyya da Makoci, har sai da na dauka, zai sashi cikin makota.

C. Duk wanda yayi imani da Allah taala, da ranar lahira, ya karrama makocinsa.

D. mafi alkhairin makota a wajan Allah, wanda yafi alkhairi ga makocinsa.

E. ka kyautata makotakar, wanda yayi makotaka da kai, sai ka zama cikkakan musulmi.

F. Bashi da imani wanda ya koshi makocinsa yanajin yunwa.

MUMMUNAR MAKOTAKA.

>Takurawa Makoci.
>Hassada ga Makoci.
>Wulakanta Makoci.
>Yin baa ga Makoci.
>Tona asirin Makoci.
>Bibiyar Makoci da Sa ido.
>Bata makoci a wajan mutane.
>Shiga hakkin Makoci.
>Damun Makoci da karar inji.
>Leken Makoci ta taga.
>Gina masai ko rijiya a jikin katangar Makoci.
>Kiwon kaji ko tantabaru suna Damun Makoci.
>Rashin fadawa yara hakkin makota.
>Damun makota da kade kade da wake wake.
>CIN Amanar Makoci
Rashin gudunmawa ga Makoci.
>Rashin sanin halin da Makoci yake ciki.
>Rashin bawa Makoci aro.
>Rashin zuwa duba Makoci.
>Rashin taya murna ko jaje ga Makoci.
>Gaba da Makoci.
Takurawa Makoci da karar inji.
>Rashin kaiwa Makoci taimakon gaggawa.
>Tankin ruwa ya rika zuba gidan makota.

Dan Uwa Yaya kake da makocinka.?

26/04/2015

Allah ta’ala ya halicci bayi da falalarsa ya bayyana musu daidai daga kuskure, Annabi s.a.w yace ‘ babu wani mutum da Allah zai bashi wani Shugabanci, ya mutu ranar mutuwarsa alhali yayi algus cikin wannan jagoranci face Allah ya haramta aljannah a gareshi.
Alokacin da fir’auna da kasaitarsa da jin ya isa ya dinga azabtar da banu isra’il ya rika kashe mazansu yana barin mata, ya rika rarraba kawunansu zuwa ga kungiya kungiya, ya shimfida zalunci yadda yakeso, a lokaci daya Allah yai masa mummunan kamu, ”Allah taala yace ‘sai muka damqeshi da rundunarsa muka kuma watsasu cikin kogi, kayi dubi zuwaga yadda qarshen azzalumai ya kasance”. na da ikon yin zalunci amma ya haramtawa kansa ya kuma haramtashi ga bayi atsakaninsu domin samar musu da rayuwa mai nagarta. Zalunci tun daga ranar da aka fara yinsa baikai labari ba sai dai yakai me yinsa ga nadama.
Hakanan buktanassar a shekara ta 576 kafin miladiya daya samu iko akan yahudawa ya riqa gallaza musu azaba, daularsa bata wuce hamsin ba ta ruguje.
Haka mutanen makkah yayinda s**a riqi siyasar zaluntar musulmai da azabtarsu basuyi qarko ba face an gama dasu an ruguje gumakansu a dan lokaci da bai wuce shekaru takwas ba.
A lokacin da hajjaj bn yusuf yadau salon gallazawa Mutane da kashesu babu gaira babu dalili. kowa yasan yadda qarshensa ya kasance.
Da wannan nake jan hankalin shuwagabanni idan har suna gani cewa
zaluntar talakawa da kashesu shine siyasar da zata tabbatar musu da mulkinsu to sun yi kuskure don kuwa zalunci baya qarko!!!
Shuwagabanni kuji tsoron Allah kuyi adalci ga talakawanku.
Mu kuma talakawa mu sani cewa tafarkin manzo s.a.w shine haquri akan zaluncin shuwagabanni da kuma yi musu adduar Allah ya shiryesu, ba wai Allah ya tsine musu ba, domin idan mun tsine musu, wahar kanmu zata sake dawowa kuma da muni, haramunne daukan makami domin yakarsu ko tsine musu akan Mimbari.
Kuma dukkan wadannan fitintinu da suke faruwa muma sai mun yiwa kanmu garan bawul, mun chanja sannan Allah ya amshi addu’ar mu.
Domin Allah ta’ala yana cewa;
1. “Kuma duk abin da ya same ku na wata masifa, to, game da abin da
hannayen ku s**a aikata ne, kuma (Allah) yana yafewar (wadansu
laifukan) masu yawa”. SHURA:30.
2. “Barna ta bayyana a cikin kasa da teku (wato ko’ina), saboda
abin da hannayen mutane s**a aikata. Domin Allah ya dandana musu
sashin abin da s**a aikata, tsammanin su za su komo (kan hanya).”
Rum:41
3. Kuma da yawa daga cikin al karya akwai wadda tayi tsaurin kai daga
barin umurnin ubangijinta da manzanninsa, sai mu ka yi mata hisabi
(sakamako), hisabi mai tsanani, kuma muka azabtar da ita, azaba abar
kyama”. Dalak:8.
4. “…lallai ne, Allah ba ya canza abinda yake akan Mutane har sai
sun canza abin da yake a rayukan su. kuma idan Allah yayi nufin wata
azaba ga mutane, to, babu mai iya mayar da ita, kuma ba su da wani
majibinci baicin shi (Allah)”. Ra’ad:11.
5. “Kuma wadanda s**a kafirta, sashen su majibintan sashe ne, idan ba
ku aikata haka ba (ku musulmi), wata fitina za ta kasance a cikin
kasa, da fasadi babba”. Anfal:73
Daga Qarshe muna addu’a Allah ya dawo da ‘ya’yan mu da wasu s**a gudu da su a garin Cibok ta jihar Borno. wayanda s**a rasa rayukansu kuma Muna addu’an Allah ya jikansu da raham.
Sannan muna musu bishara da Cewa “Allah taala yace ‘ lalle tare da tsanani akwai.sauki’ sayyiduna umar yace tsanani bai taba rinjayar sauki biyu ba’. Allah ta’ala yace ‘ kasa ta Allah ce yana gadar da ita ga wanda yaso’ yace ‘ mun ributa a cikin Zabuura bayan ambato cewa lalle kasa bayina salihai su zasu gajeta’ Annabi s.aw yace ‘ kuyi hakuri har sai kun iskeni a bakin tabki’ Lalle Allah yana tare da masu hakuri, kuma baya tauye ladan masu hakuri. Allah ya bamu hakuri
Ya Allah mun tuba, ka yafe muna, ka bamu ikon daukar matakin da ya
dace. kuma ya Allah ka kawo muna saukin wadannan musibu, idan kuma Mutuwa tazo muna addu’an Allah yasa mu cika da imani. Amin

25/04/2015

Abu Zarr al-Ghafari said: “The Messenger of Allah (SAW) said: ‘Sadaqah is prescribed for every person every day the sun rises.’ I said: ‘O Messenger of Allah, from what do we give sadaqah if we do not possess property?’ He said: ‘The doors of sadaqah are takbir (Allahu Akbar), Subhan Allah, Alhamdulillah, La-ilaha-ilAllah, Astaghfirullah,enjoining good, forbidding evil, removing thorns, bones and stones from the paths of people, guiding the blind, listening to the deaf and dumb until you understand them, guiding a person to his object of need if you know where it is, hurrying with the strength of your legs to one in sorrow who is appealing for help, and supporting the weak with the strength of your arms. These are all the doors of sadaqah.” [Ahmad]
In other words one does not need to have financial resources to earn the reward of sadaqah. There are many deeds that qualify as sadaqah with Allah (subhana wa ta’ala). In addition to those listed above the following ordinary courtesies are also sadaqah if we do them with the intention of pleasing Allah with them.
1. To administer justice between two people is sadaqah.
2. To assist a man upon his mount so that he may ride it is sadaqah.
3. To place his luggage on the animal is sadaqah.
4. A good word is sadaqah.
5. Every step taken toward prayer is sadaqah.
6. Your smile for your brother is sadaqah.
7. Planting anything from which a person, an animal or anything eats is sadaqah.

25/04/2015

.
~~~ # MANUFARMU~~~
=Yau kimanin shekara 37 ke nan da Allah (s.w.a) cikin ikonsa ya azurta mu da wannan Kungiya ma albarka wato Jama'atu-Izalatil-Bid'ah-Wa'ikamatis-Sunnah (JIBWIS), wanda kafin samuwarta, al'ummar Musulmin wannan kasa suna zama ne zama irin na naga yadda iyayena suke addini don haka ni ma zan yi, babu yin bincike a gano mece ce Sunnah? mece ce al'ada? Wanda a wancan lokaci sai ka ga an dauki al'ada an fifita ta aka Sunnah.
To, Allah (s.w.a) sai ya samar da wannan Kungiya, ta soma kira da bambance mene ne al'ada kuma mene ne Sunnah?
=Tabbas malamanmu a wancan lokaci sun sami cikas da dama daga malaman Bid'ah, amma da yake gaskiya daya ce, wanda a lokacin 90 acikin dari yan Bid'ah ne.
=Amma a halin da muke ciki sai mu godewa Allah tunda a yanzu idan ka dubi Musulmin wannan kasa zaka ga kashi 80 acikin 100 sun zama Ahlus-Sunnah.
=Ashe kuwa kungiyar # Izalahta yi babban jihadi ta fuskar wayar wa jama'a kai don su san abin da ke wajibi a kansu na addini, kuma su san yadda zasu bambanta tsakanin al'ada da addini.
=Kuma wani abin ban sha'awa a nan shi ne yadda aka fara wannan tafiya, ba a taba jin an ce gashi wannan kungiyar ta ka sa tafiyar da wannan babban aiki ba, maimakon haka ma, sai kara habaka takeyi.
=Mai karatu zai ce to, wa ke basu kudi suna tafiyar da aikace-aikacenta. To, da farko dai tun da aka kafa wannan kungiya kimanin shekara 37 a wannan kasa, babu wata Gwamnati ko wasu jama'a da za a ce suna tallafa mata wajen tafiyar da aikace-aikacenta, sannan babu wata hukuma ko wata kasa da take taimaka mata da wasu kudi ko kayan aiki.
=A halin da ake ciki wannan kungiya tana da akalla yan agaji sama da Miliyan biyu wanda mafi yawansu matasa ne majiya karfi, suna bada gudumawarsu gareta Fisabilillah.
=To. amma wani abin ban haushi a irin yadda shugabannin wannan kungiya s**a tashi ba dare ba rana don suga sun isar da sakon Allah ga al,umma, sai gashi an sami wasu matasa suna raina wa Malamanmu, Magabata da s**a shuka alkhairi a kan wannan Da'awa.
=Muna yi wa Malamanmu addu'ar Allah ya saka musu da alheri akan irin sadaukar da rayuwarsu don ci gaban addinin Musulunci a wannan kasa ta Nigeria. A da in an ce wannan dan ne sai kaga har kyamar sa ake yi, amma yanzu sun zama abin so, abin sha'awa.
=Allah ya daukaki addinin Musulunci, Ya daukaki kungiyar da shugabanninta akan kokarin da suke yi na bayyana wa al'umma gaskiya akan addininsu. Ameeen.
Abu-Khadijah,
19/04/2015

10/12/2014

***HADISIN NA YAU***


An kar6o daga Abi huraira (r.a) yace:- Hakika Annabi (s.a.w) yace:-

''Allah (s.w.a) yace:- Dan Adam yana cutar dani yana zagin zamani Nine zamani Al-Amari yana hannuna Ina jujjuya dare da yini''


(Bukhari 7491, Muslim 2246)



Shiga wannan koren rubutun kayi like na wannan shafin mai Al-barka
Jibwis Social Media Kano Municipal Nigeria

Photos from Al,azkar FIL kitabullahi wassunnah's post 20/07/2014

Aslm warahmatullah
a madadin dukkanin members na wannan page mai albarka nake taya yan uwa musulman duniya baki daya murnar zagayowar wannan wata mai albarka,watan da allah s.w.t ya ke saukar da rahama akan bayinsa, watan da ake son ya waita karatun alqur'ani mai girma.watan da allah yake bude kofofin aljannah ya kuma rufe kofin wuta, acikin watan akwai daren lailatul qadr wanda alkhairan dake cikinsa sun fi na wata dubu.....MA'ANA (RAMADAN MUBARAK) Ina mai addu'a allah ya sadamu da alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka, ameeeeeeeen

Want your business to be the top-listed Government Service in Ibadan?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address

SABUA
Ibadan
ZIPCODE