17/09/2026
Akan Kudi Bilion Nawa ?🤔
Hukumomi a Jihar Jigawa sun fara rabon kaji ga mata masu juna biyu da masu shayarwa domin inganta abinci mai gina jiki da lafiyar uwa da jariri.
Shirin, wanda gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar UNICEF ke gudanarwa, ya shafi mata daga ƙananan hukumomin Dutse, Kafin Hausa da Ringim.
An ƙaddamar da rabon ne a Dutse ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun ce shirin na daga cikin matakan tallafa wa mata da yara wajen samun abinci mai gina jiki da inganta lafiyar iyalai a jihar.