Bashir Iliyasu Sabitu Galma

Bashir Iliyasu Sabitu Galma

Share

Lailaha'illallah Lailaha'illallah Lailaha'illallah Lailaha'illallah
. Muhammad Rasulullah Sallallahu Alaihi Wasallam

Photos from Bashir Iliyasu Sabitu Galma's post 18/09/2025

Bata-gari sun kai wa wani matashi hari, sun sassare shi har s**a karya masa hannaye biyu

Mun samu rahoton mummunan hari da ya faru a daren jiya bayan kammala taron kaddamar da aikin hanyar Kayarda da Gwamna Uba Sani ya gudanar a karamar hukumar Lere.

Wannan bawan Allah, Mai suna Jaro Janta K Dodo, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga wajen taron, ya gamu da wasu bata-gari da ba'a san ko su waye ba, inda s**a kai masa hari, s**a sassare shi, tare da karairaya masa hannaye guda biyu.

Lamarin ya tayar da hankula a yankin, inda jama’a ke kira ga hukumomi da su gaggauta daukar mataki domin k**a wadanda s**a aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da adalci.

Muna yi masa fatan samun sauki da waraka cikin gaggawa. Allah Ya kare mu daga irin wannan tashin hankali.

KHM TV HAUSA.

18/09/2025

Earnesto Valverde (kocin Bilbao): "Idan da Arsenal gasar La Liga suke buga wa, to tabbas zasu iya lashe gasar sau 10 a jere. A Spain, samun nasara ya ta'allaka ne gaba ɗaya a kan tarewa, su kuma Arsenal suna da mafi kyawun masu tsaron baya a nahiyar Turai a halin yanzu."

Shin kun yarda?

• Fagen Wasanni

18/09/2025

Allah ya jikan Kakana Malam Sabitu ya sabunta Rahma gare shi

Photos from Bashir Iliyasu Sabitu Galma's post 15/11/2023

ALLAH SARKIN IKO: Yadda wani Shehin Malami A Adamawa mai suna Sheikh Dahiru Ganye, ya kasance da k**anni guda da Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A), farkon fitowar hoton mutane dadama sun yi tsammanin hoton Shehi ne, sai daga bisani wasu s**a fayyace cewa ba hoton Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) ba ne.

BABU SHAKKA AKWAI WATA HIKIMA TA ALLAH A CIKIN WANNAN AL'AMARI.

• Sunan su Iri Guda.
• k**anni Guda
• Tsara a Shekaru
• Fulanine duka.
• Musulmi Yan Darikar Tijjaniyya.

ALLAH YA BAMU ALBARKACINSU, ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W).

15/10/2023

ZAHIRIN RAYUWAR WADANDA BA SU JE JAMI'A BA

Sanarwa: Asalin rubutun nan ba ni na yi ba. Fassarawa kawai na yi don amfanin jama'armu. Kuma na dan yi canje-canje a ciki don ma'anar ta fito wa Bahaushe tarwai. A turakar Yayana Malam Aliyu Nuhu na ga rubutun. Shi ma kuma ya ce ya kwafo ne.

Ga abin da aka ce:

Ka dauki naira dubu 50, ka ba matashin da ya kasa kammala sakandare, za ka ga ya sayi risho da kayan tuya yana soya indomie yana sayar wa mutane, ko ka ga ya fara sayen gwanjo yana sayarwa, ko ka ga yana sayar da takalma 'yan Kwatano. Wani ikon Allah, a cikin shekaru uku zuwa biyar da fara bizines dinsa, za ka ga matashin nan ya yi aure abinsa. Ya sayi dan mashin dinsa Jinchen, har ma ya kai ga sayen fili don fara gini. Rayuwarsa ta dauki saiti.

Amma ka dauki naira miliyan daya, ka ba matashin da ya kammala jami'a, za ka ga ya sayi waya qirar IPhone 11 Pro Max ko Samsung Galaxy S20. Kuma ya sayi wandunan jeans damammu da 'designer shirts.' Sannan za ka ga yana daukar budurwarsa suna zuwa cin burger ko shawarma suna daukar selfies har kudin su qare. Bayan sun qare, za ka ga ya koma wurin mai indomie din can da bai gama sakandare ba yana cin bashin na dare ko bashin kudin fita da sunan jiran aikin ofis.

Abin tambayar a nan shi ne, shin ilimin boko yana qyanqyasar mutakabbiran marasa lissafi ne?

Kalla! Sam ilimin boko ba ya yin haka. Amma in har matashi bai kula ba, to rayuwar ilimin tana sa mutum ya riqa yi wa abin da qila shi ne dalilin arziqinsa gani-gani. Da haka sai ya tsallake damarsa saboda hangen dala. Wannan kuma na daga cikin dalilan da ke sa ake yawan samun marasa aikin yi cikin masu ilimi. Kafin ka ce me, sai wancan da bai ma kammala sakandare ba, ya yi bunqasar da zai zo ya dauki wanda ya kammala jami'a aiki, yana biyansa albashi a kowane wata.

28/09/2023

Farfesa Ibrahim Maqari Yana Cewa;

Wata rana an tambayi Maulana Sheikh Ibrahim Inyass (RA) menene hujjan yin MAULUD ?

Sai Shehu yace rashin Hujja Maulidi shine ya kawo hujjan mu na yin mauludin Domin akwai Abunda yafi Qarfin hujja Shehu yace baka ga duk Qur'ani, ba inda Allah yacema UWA ta so DAN ta ba ?

Ai Allah bai cema UWA ta so DAN taba, saboda bata bukata sai ance mata ta so shi zata so shi. Domin Allah ya riga ya shuka son DAN acikin UWAN, Amma shi DAN da a kasan zai iya Qin biyayya baka ga wuri daban daban Allah yake umartarsa da bin iyaye ba?

SHARHI

PROFESSOR IBRAHIM MAQARI yana cewa: Watarana an taba haduwa da wata mata aka nunamata wani malami "imamul Faharrazi" aka ce mata kinga malamin can zai iya baki Hujja dubu akan samuwan Allah

Sai matan tace "Allah sarki miskini!

Ai yana da shakka dubu ne a zuciyarshi shiyasa har zai iya samo hujja dubu in ba haka ba ya za'ayi mutum, in ba mahaukaci ba yadauko "touch light" da rana kuma yace wai yana neman Rana.

Duk girman hujja ai bata kai "touch light" rana tare da ubangiji ba, Allah da yakira kansa "Azzahiru" kuma yake bukatan wata hujja tazo ta bayyana dashi ? Ai Lamarin Akwai Abun dubawa

Allah yakarawa PROFESSOR lafiya da fahimta bijahi (S.A.W). Ameen Yaa Allah ina muku barka da shiga watan da aka haifi shugaban mu Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi Wasallam)

18/09/2023

Ƴan Majalisar Dokokin Jihar Kano za su yi karo-karo daga albashinsu don taimakawa wannan matashi da ya mayar da Tsintuwa ta Miliyoyin Kuɗi.

18/09/2023

Abin mamaki baya karewa a Najeriya dan takaran Gwamna ya zama Dan Mediya😀😀😀

18/09/2023

Al Nassr ta sauka Iraq domin fafata gasar Zakaru ta Nahiyar Asiya, kuma ta soke daukar atisayen ta a yammacin yau saboda dandazon magoya da s**a mamaye sansanin saboda suna son ganin Cristiano Ronaldo.

Photos from Bashir Iliyasu Sabitu Galma's post 18/09/2023

Mai Martaba Khaleefa Muhammad Sanusi II ya halarci mitin na mambobin SDG na Duniya na shekara da sukeyi da Sakataren Majalisar dinkin duniya da Mataimakiyar sa da Praminista ta Barbados da sauran mambobi a hedikwatar Majalisar dinkin Duniya a New York, kasar Amurka, kuma ya kaiwa Jakadan Nigeria a Majalisar dinkin Duniya ziyara a ofishinsa, haka kuma yayi mitin da Jakadan Sudan a Majalisar dinkin duniya a ofishinsa dake cikin Majalisar. Lahadi 17th September, 2023.

HH Muhammad Sanusi II was at the UN Headquarters to attend the SDG Advocates Annual Meeting with SG & DSG, in attendance also were the Prime Minister of Barbados and other SDG members. HH also paid a courtesy call to Nigerian Permanent Representative to UN in his office, and had a meeting with Ambassador Al-Harith Idriss a Permanent Representative of the Sudan to the UN.
Sunday 17th September, 2023.

13/09/2023

YADDA SHA'ANIN RUWAYAR SALATIN IBRAHIMIYYA YA KASANCE.

Lokacin da Sahabi Bashir Bin Sa'ad ya tambayi MANZON ALLAH (S.A.W) : ALLAH ya umarce mu da mu yi maka Salati, to ta yaya zamu yi ma ka shi? ANNABI (S.A.W) yayi shiru na tsawon lokaci, Maruwaicin yace: Har sai da muka shiga damuwa saboda shirun da yayi, tukunnah daga baya ya karanto Salatin Ibrahimiyya.

Misalin yadda abin yake (ANNABI S.A.W madaukakine ga daukar siffa a misali da komai da kowa) amma k**ar kai ne kaje gaban Sarkin garinku, sai mai fadi yace da ku: Lallai ku gaisar da wannan Sarki na ku kuma ku jinjina gareshi, sai wani daga cikinku yace da Sarki "Mai Martaba koya mana yadda zamu gaisar da kai kuma mu jinjina maka", shin aikin mai martaba ne koya muku yadda zaku gaisar da shi kuma ku jinjina masa?

To amma saboda saukin hali irin na MANZON ALLAH (S.A.W) da kuma dabi'arsa ta "Tawadi'u" ya sanya ya bashi salati na Ibrahimiyya a irin salon "Kada ku fifita ni akan Yunusa Dan Matta" amma lallai umarnin ALLAH kai tsaye na "KU YI SALATI A GARE SHI" to kofa ce budaddiya na yi masa salati da kowacce siga, muddin babu guluwi, ko illa cikin kalmonin. Domin shi bai hani da hakan ba, Sahabbai sun yi masa salati ta sigogi mabambanta, haka nan Malaman Musulunci su ma sunyi masa da sigogi mabambanta, kuma ALLAH ya karba, kuma sun dace Duniya da lahira.

ALLAH KA DATAR DA MU FAHIMTAR NASSI, YADDA YA DACE.

ALHAMDULILAH

Muhammad Usman Gashua

Want your business to be the top-listed Government Service in Kaduna South?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Galma
Kaduna South
8187865483