29/05/2026
Taron shuwagabanin campaign na Hon Ibrahim Aliyu Wusono kenan Wanda ya gudana a gidan Director campaign na wosono
Hon Usman Ibrahim
Taron ya gunane a karkashin Jagorancin Alh Umar saeed chairman committee
Taron ya kunshi Abubuwa da dama masamman zaben fidda gwani da jam iyar ADC ta gudanar a makon daya gabata
inda Al umma da dama s**a tabbatar da ba adalciba a zaben fidda gwani na jam iyar ADC
abisa wanan dalilin yasa aka kirataron Dan Asamu mafita Dan ganin anyima Al ummar karamar Hukumar Igabi adalci
akarshe Al ummar Igabi masamman na jam iyar ADC suntabbatar zaben ba
bayan angama sauraren korafen Dan takaran majalisan tarayya na karamar Hukumar Igabi ya godema Allah tare da Al ummar karamar Hukumar Igabi abisa irin soyayya da s**a nuna masa lokacin zaben fidda gwanin
bayan haka manabin dukkan matakai Dan ganin anbima Al ummar Igabi hakkinsu akan wanan zaben Dan haka Yana kira ga Al ummar Igabi masamman magoya bayansa su jira suji irin matakin da zasu dauka anan gaba kadan in Sha Allahu
Muna Rokon Allah yayi mana jagora yabamu Nasara
25/05/2026
Wallahi Kare Saidai ya Mutu da haushin Kura. Kaikuma mai bakin ciki kaje bakin cikin ta kasheka. Hon. Ibrahim Aliyu Wusono da Allah ya dogara don haka taron yuyuyu nan a yuyuyu zasu kare kuma in sha Allah sai mun kaisu kasa
24/05/2026
Assalamu Alaikum.
Inaso nayi Amfani da wannnan Damar Domin Tunasantar da Al'ummar karamar Hukumar igabi Cewa Gobe LITINI Za a gudamar da zaben Fidda Gwani a jam’iyyar ADC.
Da wannan nake Rokon Al'umar Karamar Hukumar Igabi Daso tai maka Su bawa wannan bawan Allah dama Ta hanyar Zabar sa a Matsayin Halastaccen Dan Takara, Domin kuwa Kowa yasanshi.
mutum ne Gogagge a Siyasa,kuma masanin Siyasa, kuma mutum ne na mutane, baya kyamatar kowa, Kamar Dayan Abokin Hamayyasa wannan kowa yasan hakan. Wusono Shine yasan matsalar Yan karkara domin kuwa ya kasan ce Bashi da girman kai.
lungu da sako na kauyukan karamar Hukumar igabi yasan su badan komai ba sai Dan ziyara da yake kai masu akai kai. Babu gayyatar da zakai wa Wusono bai zoba, kaga ko wannan shine Cikakken Wakili.
Kuma Dan Allah Mutanen Igabi Shin Sauran Mazabu bayi ne? da Mazaba daya ce zata Dinga Mulkar mu, Mai yasa baza a bawa wasu Mazabu damar ba? Kuma bayan Suma sunada Cikakken Dan siyasar da a kaduna ma ana Alfahi dashi.
Mu mutanen Igabi bazamu ki Cin BIRI MUCI DILA BA.
Da wannan Dalilin Nake San wannan bawan Allah din. Allah Ubangiji ka zama Gatan mu 🙏.
22/05/2026
Amana sai Dan Amana Allah ya taimaki DG. Mai capacity
22/05/2026
Uban Bello Dan Aliyu Uban Aliyu Ka rigasu kace Allah Nasara takace dayardan Lillahil wahidil qahhar
Na Annabi yace Amin
21/05/2026
Rt. Hon Ibrahim Aliyu Wusono ba gaba da gaba ba koda ta baya sai an duba. Ka ginasu sunyi Butulci Allah zai rushe maka su gabaki dayansu
21/05/2026
Congratulations Ibrahim Aliyu Wusono as consensus candidate in ADC Igabi LG House of Rep's
20/05/2026
Daga Mando dake maza6ar Afaka ward
inda committee campaign na Ibrahim Aliyu Wusono ta ziyarci maza6ar Afaka akarkashin jagoranci Director campaign Hon Usman Ibrahim
sun ziyarci maza6an ne Dan Rokon Arziki a wajen Al ummar maza6an na Afaka Dan Niman goyon baya Dan samun Nasara azaben fidda gwani na jam iyar ADC da akesa ran za ayi agobe Alhamis
bayan haka wosono yaroki Arziki a wajen Al ummar maza6an Afaka ward sun amsa masa zasuyi da yardan Allah
Ibrahim Aliyu Wusono
ya kaddamar da committee campaign dinsa na maza6ar Afaka ward Dan samun cikakken Nasara azaben kasa Baki daya na 2027
akarshe wosono yamika godiya ga Al ummar Afaka abisa irin Gudumawan da suke bashi asiyasance yayi Godiya sosai
yaroki Allah ya tabbatar mana da Nasara acikin wanan takara namu
Amin
20/05/2026
Daga Gwaraji ward
inda committee campaign na dan takaran majalisan tarayya na karamar Hukumar Igabi a Karkashin Jagorancin Hon Usman Ibrahim
tare da dan takaran majalisan Muka ziyarci maza6ar Gwaraji ward Dan ziyaran sarakuna tare da Niman goyon baya Al umma dan samun Nasara azaben fidda gwani na jam iyar ADC dake tafe a gobe Alhamis
bayan haka Hon Ibrahim Aliyu Wusono ya kaddamar da committee campaign na maza6an Gwaraji ward inda Hon Muhammad Haruna a matsayin chairman committee na campaign din na Gwaraji ward
akarshe Hon Ibrahim Aliyu Wusono
ya Mika godiyansa ga Al ummar Gwaraji ward abisa cikakken goyon baya dasuke bashi da asiyasance
yakuma godema Hakimin mazabar Gwaraji abisa kokari dayakeyi na Samar da Zaman lafiya dayakeyi a yakin
Muna Rokon Allah ya tabbatar mana da Nasara acikin wanan tafiya
Amin
19/05/2026
Daga maza6ar Zangon Aya
inda committee campaign na Ibrahim Aliyu Wusono s**a ziyarci maza6ar na z/Aya tare da kaddamar da committee campaign na maza6an z/Aya
bayan haka Dan takaran majalisan tarayya na karamar Hukumar Igabi Ibrahim Aliyu Wusono yashiga cikin garin z/aya Dan yin ta aziyya na wasu Yan uwa da s**a rasu a Daren jiya
wosono yaroki Allah ya gafarta wayanda s**a rigamu
bayan haka Dan takaran majalisan tarayyan yashiga lungu dasako na maza6an z/Aya Dan Rokon Arziki wajen Al ummar z/aya
akarshe wosono yamika godiya ta musamman ga Lamido Ibrahim z/Aya abisa irin Gudumawan da yake bayarwa masamman a cikin committee na campaign dinsa
yayi fatan Allah yabasu Nasara Baki daya
Muna Rokon Allah yayi mana jagora