31/07/2025
Alhamdulillah!
Yan'uwa kusa mana Albarka.
Na kammala kusan kashi 80% na wannan littafi mai taken: "Pantami: The Digital Architect of a New Nigeria"
(a cikin harshen Hausa da kuma Turanci).
Wannan littafi ya samu sanyawar albarka da kuma sahalewar Professor Isa Ali Pantami CON, da kansa. Kuma Muna fatan kaddamar da shi (Launching) a cikin birnin Gombe, in sha Allah, bayan kammala aikin gyara da bugawa, muna sa ran Professor da kansa zai kasance babban bako na musamman a taron.
Abubuwan da littafin ya ƙunsa sun haɗa da:
1. Gudunmawar Professor Pantami ga ci gaban Nigeria, tun daga lokacin da yake DG na NITDA har zuwa lokacin da ya zama Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki.
2. Cigaban da aka samu a NITDA a lokacin jagorancinsa, da kuma rawar da hukumar ta taka wajen sauya tsarin digital a Najeriya.
3. Nasarar da Ma'aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin ta samu a karkashin jagorancinsa, da wasu muhimman ayyuka da aka aiwatar a wannan lokaci.
4. Gudunmawar Professor Pantami a fannonin:
A. Noma
B. Lafiya
C. Ilimi
D. Sana’o’i
E. Tsaro
F. Tattalin Arziki
5. Ayyukan talafawa matasa da ya jagoranta daga matakin jaha har zuwa matakin tarayya da adadi da misalan wasu daga cikin matasan da s**a amfana.
6. Ayyukan da ya aiwatar a dukkan jahohi 19 na Arewacin Najeriya, da tasirinsu ga al’umma.
7. Gudunmawar sa ta musamman ga Jahar Gombe, musamman a fannoni kamar:
A. Noma
B. Ilimi
C. Lafiya
D. Sana’o’i
8. Ci gaba da bayar da gudunmawarsa bayan barin kujerar Minista, inda har yanzu yake ba da tallafi da tsari ga al’umma da matasa.
9. Yabon da ya samu daga shugabanni, malamai da dattawan kasa, wanda ke nuna irin girmamawa da martabar da ya samu a idon al’umma.
Allah yasa albarka, Allah kuma ya bamu ikon kammala aikin lafiya. Amin

30/12/2024
27/12/2024
18/12/2024