Kai tsaye interview Dr, Hamza Ibrahim ikara tare da manema labarai daga wajen taro Umar Musa yar'aduwa conference centre kafuna
Dr Hamza Ibrahim Ikara Support Group
All Progressive Congress ✔️✔️🇭🇳🇭🇳🇭🇳✔️✔️✔️
Our Mission is to Construct and Institute a Progressive Local Government and State Anchored on Social Democracy👍👍👍
26/01/2026
Vol 2
3. Bukatun ci gaba – Akwai manyan bukatu na ci gaba da wakilci nagari da Ikara ke fuskanta, wanda wakili na gida zai fi fahimta.
4. Hadin kai da zaman lafiya – Ba a taɓa samun rikici ko rarrabuwar kai daga Ikara ba wajen neman dama; hakan shaida ce ta balaga a siyasa.
*ME YA SA DR. HAMZA IBRAHIM IKARA YA FI KOWA CANCANTA*
Mai Girma Gwamna, idan aka zo batun wanda ya dace a goya masa baya, ba shakka Dr. Hamza Ibrahim Ikara ya wuce cancanta. Dalilai kuwa suna da yawa:
1. MUTUM MAI ILIMI DA HANGEN NESA
Dr. Hamza mutum ne mai zurfin ilimi, fahimtar harkokin gwamnati, da sanin dokoki. Wannan ilimi ne da ake buƙata a Majalisar Wakilai domin tsarawa, muhawara, da kare muradun jama’a.
*2. MUTUM MAI HALAYE NAGARI*
Ya shahara da gaskiya, tawali’u, da mutunta kowa. Bai san bambanci ba tsakanin talaka da mai kuɗi. Wannan hali ne da jama’a ke buƙata daga wakilinsu.
3. ƊAN JAM’IYYA NA GASKIYA (APC)
Dr. Hamza ya tsaya tsayin daka tare da APC tun daɗe, a lokutan wahala da na sauƙi. Ba ɗan anfani da jam’iyya ba ne, illa mutum mai kishinta.
4. ƊAN IKARA NA GASKIYA
Ya san matsalolin Ikara da Kubau dalla-dalla: noma, ilimi, lafiya, tsaro, da matasa. Wakilci daga irin wannan mutum zai kawo sauyi na gaske.
KIRA GA MAI GIRMA GWAMNA
Mai Girma Gwamna Uba Sani, kai shugaba ne da ake girmamawa saboda ka na sauraron jama’a kuma kana yanke hukunci bisa adalci. Wannan dama ce ta rubuta sunanka da zinariya a tarihin Ikara da Kubau ta hanyar mara wa Dr. Hamza Ibrahim Ikara baya.
Goyon bayanka zai:
Ƙarfafa haɗin kan APC a yankin
Kara wa jama’a kwarin gwiwa
Tabbatar da nasarar jam’iyya cikin sauƙi
Samar da wakilci nagari a Majalisar Tarayya
*KAMMALAWA*
A ƙarshe, Mai Girma Gwamna, muna roƙonka da ka yi duba na adalci da hangen nesa. Lokacin Ikara ne, kuma Dr. Hamza Ibrahim Ikara shi ne mafi cancanta. Babu wanda ya fi dacewa a goya masa baya face shi.
Allah Ya ja zamaninka, Ya ƙara maka basira da nasara, Ya kuma sa ka yanke hukunci da zai amfani al’umma baki ɗaya.
AYIK✍️✍️✍️
26/01/2026
BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KADUNA
VOL 1
Sanata Uba Sani, CON
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,
Mai Girma Gwamna, muna miƙa gaisuwa ta musamman tare da fatan alheri, zaman lafiya, da ƙara samun nasara a jagorancinka mai cike da hangen nesa, adalci, da kishin al’umma. Lallai shugabancinka ya kawo sabuwar fata da kwarin gwiwa ga al’ummar Jihar Kaduna, musamman ma yankunan karkara da aka dade ana kallon su a baya.
Mai Girma Gwamna, wannan rubutu na zuwa gare ka ne domin bayyana ra’ayi, fata, da kuma muradin al’ummar Ikara da Kubau Federal Constituency, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci na shirin siyasa. Rubutun na nufin bayyana gaskiya da adalci dangane da kujerrar Wakilin Tarayya (House of Representatives) ta Ikara/Kubau, wacce a fili take nuna cewa lokacin Ikara ne, kuma akwai mutum guda da ya fi kowa cancanta da ya dace a goya masa baya—Hon. Dr. Hamza Ibrahim Ikara.
IKARA DA KUBAU: TARIHI, ADALCI, DA JUYIN JUYA HALI
Mai Girma Gwamna, Ikara da Kubau ba sabbin yankuna ba ne a siyasar Jihar Kaduna da ta ƙasa baki ɗaya. Yankuna ne masu tarihi, mutunci, da rawar da s**a taka a siyasa, ilimi, kasuwanci, da zaman lafiya. Duk da haka, idan aka yi la’akari da tsarin raba dama da wakilci, Ikara ta dade tana haƙuri, tana jiran lokacinta cikin biyayya da biyayyar jam’iyya.
A siyasa, adalci shi ne ginshiƙi. Idan aka ce lokaci ya yi na wani yanki ya wakilci jama’a, hakan yana ƙarfafa haɗin kai, kwanciyar hankali, da amincewa da shugabanci. A yau, babu shakka cewa lokacin Ikara ya yi na riƙe wannan kujera domin a cika tsarin daidaito da gaskiya.
DALILIN DA YA SA IKARA TA CANCANTA A YANZU
1. Haƙuri da biyayya – Ikara ta nuna ladabi da biyayya ga jam’iyya da shugabanci a tsawon lokaci.
2. Gudummawa ga nasarar APC – A kowane zaɓe, Ikara na daga cikin yankunan da s**a tsaya tsayin daka wajen ba APC ƙuri’u
24/12/2025
24/12/2025
.
A daedae lokacin da wasu suke raba kudaden da bazasu kashe kishi ba,Shi Kuma Dr Hamza Ibrahim Ikara appointment yake rabawa ga 'ya'yan talakawa domin su dogara dakansu.Allah ya karawa Dr Hamza Ibrahim Ikara Hikima,Tausayi da taimakon jama'a.
Thank you Dr!!!
Ikara/Kubau Sai Dr
26/10/2025
.
.
💪💪💪💪
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Address
Anguwar Turaki Ikara
Kaduna
234
