DLC Hausa Media

Website Contact the organization

DLC Hausa Media DLC Hausa – Duniyar Labarai kafar yada labarai ce ta zamani da ke kawo sahihai kuma ingantattun labarai cikin harshen Hausa.

APC ta yi gargadi kan zargin shirin Atiku da ADC na ɓata sunan gangaminta a KadunaKwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙa...
24/10/2026

APC ta yi gargadi kan zargin shirin Atiku da ADC na ɓata sunan gangaminta a Kaduna

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da jam’iyyar ADC da shirin yaɗa labaran ƙarya domin ɓata sunan gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Kaduna.

Kakakin kwamitin, Dele Alake, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar 24 ga Oktoba, 2026. Ya zargi ɓangarorin da yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar amfani da bidiyoyin bogi da takardun da aka ƙirƙira, ciki har da wata wasiƙar da ake zargin ta nuna cewa gwamnatin Kaduna ta ware naira tiriliyan 2.3 domin gudanar da gangamin.

Alake ya ce kasafin kuɗin jihar na shekarun 2024, 2025 da 2026 bai kai wannan adadi ba. Ya kuma yi zargin cewa ana shirin yaɗa tsofaffin bidiyoyi da aka sauya domin nuna rashin amincewar jama’a da gangamin, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan.

Source
SokotoCast

24/10/2026

Sponsored

Dear Ahmad Aliyu Sokoto, Ministry of Health Sokoto Sokoto State Primary Health Care Development Agency, Chief Of Stap Government House, Hon Naseer Bazzah, DCL Hausa, Sanata Wamakko

Ina aka kwana akan issue din nan ?

TIRƘASHI: Yadda Wasu Mahalarta Taron Ƙaddamar Da Kamfen Ɗin APC Ke Kwance A Kan Hanya A Kaduna, A Cikin Daren Nan.Mike f...
23/10/2026

TIRƘASHI: Yadda Wasu Mahalarta Taron Ƙaddamar Da Kamfen Ɗin APC Ke Kwance A Kan Hanya A Kaduna, A Cikin Daren Nan.

Mike faruwa ne ?

KO SAMA CE ZATA FAƊODuk Da Irin Ƙazafin Da Ake Yi Mana, Ba Zai Sa Mu  Daina Tallata Tinubu Ba, Inji Shugaban Ƙungiyar Iz...
23/10/2026

KO SAMA CE ZATA FAƊO

Duk Da Irin Ƙazafin Da Ake Yi Mana, Ba Zai Sa Mu Daina Tallata Tinubu Ba, Inji Shugaban Ƙungiyar Izala Ta Jihar Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan.

Wace fata kuke musu ?

MUMMUNAN HATSARIN  MOTA...Mun samu labarin wani hatsari ya faru da wata mota cikin tawagar jahar Sokoto dake kan hanyar ...
23/10/2026

MUMMUNAN HATSARIN MOTA...

Mun samu labarin wani hatsari ya faru da wata mota cikin tawagar jahar Sokoto dake kan hanyar su zuwa Kaduna.

Wata tawagar matasa da s**a kunshi motar (Amirul Hajji) na wasu Kananan hukumomin Sokoto sun sami (Accident) hatsarin mota a hanyar zuwa Kaduna domin taron kaddamar da kamfen din shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da za'a Gudanar a Gobe Asabar.

Da ɗumi-ɗumi: Jaruma Jamila Nagudu ta lashe gasar wakar Mawaki Rarara Mai taken Ina Da Hujjar Yin APC.Jarumar Itace ta z...
23/10/2026

Da ɗumi-ɗumi: Jaruma Jamila Nagudu ta lashe gasar wakar Mawaki Rarara Mai taken Ina Da Hujjar Yin APC.

Jarumar Itace ta zo ta ɗaya ta samu kyautar kuɗi har naira miliyan goma ₦10,000,000 Tare da samun kyautar wata babbar motar zamani.

SHEDUN DUNIYA....Za'ayi jana'izar bayan sallah juma'a a shiyar Gidadawa dake birnin Sokoto, Malamin Makarantar wanda ya ...
23/10/2026

SHEDUN DUNIYA....

Za'ayi jana'izar bayan sallah juma'a a shiyar Gidadawa dake birnin Sokoto, Malamin Makarantar wanda ya rasu yau nbayan fama da jinya a gida da kuma Asibiti.

Mallam Halirru Gidadawa na ɗaya daga cikin Matasa yan Gwagwarmayar ilimi a yankin Arewacin Najeriya, kuma na gaba-gaba wajen ganin matasa sun samu ingataccen ilimi.

Yadda labarin rasuwar sa ta jefa dinbin matasa cikin Jimami da addu'o i ya nuna irin halayen da na kwarai cikin al'ummah.

Muna fatar Allah ya jikan sa da Rahama.
Rahoto: Rchp Abubakar Abdullahi 🗞️

2027: Atiku Ya Bukaci INEC Ta Fitar Da Rajistar Masu Zabe Miliyan 103, Ya Zargi Hukumar Da Hana ’Yan Najeriya Samun Dama...
23/10/2026

2027: Atiku Ya Bukaci INEC Ta Fitar Da Rajistar Masu Zabe Miliyan 103, Ya Zargi Hukumar Da Hana ’Yan Najeriya Samun Damar Dubawa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da gaza samar da rajistar masu zaɓe ta farko domin jama’a su samu damar dubawa, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya raunana amincewar jama’a ga zaɓen shekarar 2027.

Duba cikakken rahoton a sashen comment

LABARAI: Macky Sall ya janye takararsa ta neman Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.Tsohon shugaban ƙasar Senegal,...
23/10/2026

LABARAI: Macky Sall ya janye takararsa ta neman Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tsohon shugaban ƙasar Senegal, Macky Sall, ya janye takararsa ta neman zama Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan wani ƙuri’ar tantance goyon baya da mambobin Kwamitin Tsaro s**a gudanar ba bisa ƙa’ida ta ƙarshe ba, wanda ya nuna cewa bai samu isasshen goyon baya ba

Karanta cikakken rahoton a sashen comment

KARSHEN ZAƁEN GWAJI..Kawo yanzu dai mungama dukan zabukan gwaji da muka shirya tsakanin ƴan takara daban daban, kamar ha...
22/10/2026

KARSHEN ZAƁEN GWAJI..

Kawo yanzu dai mungama dukan zabukan gwaji da muka shirya tsakanin ƴan takara daban daban, kamar haka:

1. Zaɓen Shugaban ƙasa.
2. Zaɓen Gwamnan Sokoto.
3. Zaɓen Gwamnan Zamfara
4. Zaɓen Gwamnan Kebbi.
5. Zaɓen Rep Gada/Goronyo.
6. Zaɓen Sanatan Sokoto ta Kudu.
7. Zaɓen Gwarzon DLC Hausa Media tsakanin ƴan majalisar wakilai 6 na jahar Sokoto, kamar

a) Sokoto North/South.
b) Kebbe/Tambuwal.
c) Gada/Goronyo.
d) Yabo/Shagari.
e) Gudu/Tangaza
f) Binji/Silame.
h) Dange Shune/Bodinga/Tureta.

Zaku iya zuwa kai tsaye ku duba kowanne sakamakon da kuke so sannan kuyi download PDF ko PNG Kai tsaye daga shafin mu a link 👇

Link https://dglhausa.unaux.com/results/
Ko https://dglhausa.unaux.com/download/

Address

No. 45 Tudun Wada Kaduna
Sokoto
58973

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DLC Hausa Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to DLC Hausa Media:

Shortcuts

Share