ADC TV AREWA

ADC TV AREWA

Share

Barka da zuwa shafin ADC TV AREWA shafin da ke kawo muku sahihan labaran siyasa cikin harshen Hausa da rahotanni cikin sauti da bidiyo da kuma rubutu

28/05/2026

Bello El-rufai Muna Jan Kunnenka Akan Ka Cire Kanka Wajen Murɗe ZABEN MONYE Idan Kuma Kaƙi Wallahi KujerarkA Sai Ka Rasata Kaima.

Babu wanda zai Zabe ka a KAWO CONSTITUENCY in babu MONYE, in kunne yaji jiki ya tsira.

Gargadin kungiyar Monye Kurum ga Bello El-Rufai

28/05/2026

Sakamakon zaɓen Kawo Constituency ya gagara sanarwar saboda wasu dake ƙoƙarin murɗe zaɓen

26/05/2026

Zaɓen primary election da ya gudana a gundumar kawo.

Hon Aminu Adam Monye ya samu ƙuri'u masu yawan gaske

15/05/2026

A wannan lokaci na siyasa, a Doka Gabasawa ana buƙatar muhimmiyar zaɓin wanda ya dace wajen wakilci a majalisar jihar Kaduna. A cikin 'yan takarar jam'iyyar ADC, akwai wasu da dama, amma akwai ɗaya wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaba matashi mai hangen nesa Hon. Muhammed Sufyan.

Hon. Sufyan matashi ne mai kuzari da jajircewa wajen kula da al'amuran yau da kullum na al'umma. Bai tsaya kawai ga kalaman siyasa ba; yana aiki kafada da kafada da jama’a wajen samar da taimako, da tallafawa al'umma a fannoni da dama. Irin wannan hali na sadaukarwa da kulawa ya sanya shi zama ɗan takara wanda ya cancanci samun goyon bayan mu.

Saboda haka, muna kira ga sauran ƴan takarar jam'iyyar ADC da a samu fahimta da haɗin kai ta hanyar janyewa, domin mu bai wa Hon. Muhammed Sufyan damar wakiltar Doka Gabasawa. Wannan mataki zai tabbatar da cewa matashi mai hangen nesa, wanda ya damu da bukatun al'umma, ne zai jagorance mu a majalisar jihar Kaduna.

Allah ya tabbatar mana da Alkhairi

MS MEDIA TEAM
15/05/2026

Photos from ADC TV AREWA's post 14/05/2026

Today, Atiku Abubakar formally submitted his presidential nomination form at the headquarters of the African Democratic Congress, marking another significant step in the journey toward rebuilding Nigeria.

What remains truly inspiring is the growing momentum across the country — a renewed belief among Nigerians that competent, inclusive and purposeful leadership can restore hope and move the nation forward. The movement continues to grow stronger.

Photos from ADC TV AREWA's post 13/05/2026

Sakamakon Zaman Meeting Na Ƴan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna A Jami'iyyar ADC!

Malam ya turo ɗaya daga cikin matansa (ASIYA) domin tayi zama da dukkan masu takarar kujerar gwamnan jihar kaduna. A saƙon da asiya ta gabatar musu a wajen zaman, ta sanar musu da cewa malam Nasir El-Rufai bashida wani ɗan takara, don haka suje suyi consensus, idan bai yuwuba ashiga primaries duk wanda Allah ya baiwa shikenan.

Wannan shine sakamakon zaman da'akayi a yau. kar wasu sudinga amfani da jita-jita suna haifarwa al'umma rikici acikin jami'iyya.

Yanzu dai kowa ya tattare ƙafar wandonsa ya nemi matsaya😅!¡

12/05/2026
Photos from ADC TV AREWA's post 07/05/2026

Alhamdulillah Yanzu Yanzu ‘Dantakara Gwamna Ajihar Kaduna Hon Shu’aibu Idris Miqati Yase Form ‘Dinshi, Allah Yabamu Nasaran Cin Primary Election Da General Election

Photos from ADC TV AREWA's post 07/05/2026

GANI YA KORI JI: Matasa Sun Samu Dama, Godiya ga Hon. Aminu Adam!

A Kawo Constituency, matasa sun fara ganin canji mai ma’ana! Hon. Aminu Adam, ɗan takarar majalisar jihar Kaduna, ya nuna jajircewa wajen samar da aikin yi, inda yanzu haka matasa 30 s**a yi passing out a Federal Fores Guard sanadinsa. Wannan aikin ya nuna yadda Hon. Aminu Adam ke ɗaukar bukatun al’umma da muhimmanci, musamman matasa.

Ba wai kawai zaben kujerar majalisa ba ne wannan, zaben shugaba mai hangen nesa wanda ke ganin matasa ginshiƙi na ci gaban al’umma. Tare da irin wannan jagoranci, matasa a Kawo suna samun damar shiga harkokin gwamnati, samun ilimi, da kuma tallafi a rayuwarsu.

Hon. Aminu Adam ya tabbatar da cewa siyasa a Kawo ba kawai kujerar kai tsaye ba ce, aa hanyar kawo canji mai ɗorewa ga al’umma ce.

Kawo Constituency, lokaci yayi da za mu tashi mu zabi shugaba mai aiki, wanda zai kawo wa Kawo Constituency ci gaba ta fannoni daban-daban musamman aikinyi ga mata da matasa.

Mu yi Hon Aminu Adam da farar zuciya.



Muneer Yusuf Assalafy
DG Media
Monye Media Team
07/05/2026

Want your business to be the top-listed Government Service in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kaduna