Akan samu rudani, a wani lokacinma a samu hadari a kan t**i, sakamakon rashin amfani da signa da wasu direboni keyi idan suna tafiya a kan t**i.
Kun kuwa san yadda amfani da signa ke taka rawa wajan rage aukuwar hadari a kan t**i ?
Hanyar Kano
Domin sanin halin da hanyoyin Kano ke ciki, don kaucewa cunkoso, samun bayanai kan yanayin tsaro…
Yayin da wasu matasa ke kokarin hawa wata babbar mota a kan t**in Zaria Road.
Kun kuwa san inda wannan mota ta nufa ?
Sheik Jafar Muhamud Way-Dorayi
@17/06/2026, 01:20pm.
Dame kake tuna Dorayi ?
17/06/2026
Yadda rashin sanya alamomin gargadi ya janyo aukuwar hadari a kan t**in Zaria Road daidai Farm Center, inda ake aikin gina gadar tsallaka hanya shiga kasuwa waya ta Farm Center.
Al’umma na wannan zargi ne bayan da aka samu wani mummunan hadari da yayi sanadiyyar rasuwar wani mutum a daidai wajan da ake gudanar da aikin gadar.
Masu bin hanyar sunyi korafi kan yadda ba’asa alamomin gargadi daga nesa ba, yadda mutum zai san ana aiki kafin ya matso kusa.
Al’umma dai na kira ga dan kwangila da kuma mahukunta da a sanya alamomin gargadi a wannan waje domin kaucewa kara samu hadari.
Yadda hada hada ke wakana a kan t**in IBB Kwari a darannan, daidai lokacin da masu lodi a kan t**in ke cigaba da cin karansu babu babbaka.
Kome doka tace gama da masu lodi a kan t**i?
Yadda aikin Gadar tsallaka t**i ya kusa kammala a Tashar Unguwa Uku Zaria Road.
Talata,16/06/2026, 01:30pm
16/06/2026
Cikin Hotuna: Yadda hanyar shiga Garin Tudun Fulani da Mayama dake Karamar Hukumar Bunkure ke barazana ga rayuwar Al’ummar yankin.
Mazauna yankin sun bayyana damuwa matuka kan yadda ake nuna rashin kulawa ga al’ummar yankin, duba da tsahon lokacin da hanyar ta dauka a haka,wanda lalacewar hanyar ta janyo ana samu jinkiri wajan zuwa leman lafiya da sauran al’amuran su na yau da kullum.
Sun kuma bayyyana yadda mata masu juna biyu ke rasa rayuwarsu akan wannan hanya sakamakon rashin kyau na hanyar.
Sun dai bukaci Gwannati da ta kai musu agajin gaggawa domin suna cikin mahuyacin hali.
Lokacin Daukar Hoto: Talata,16/06/2026,02:30pm
15/06/2026
Cikin kasuwar Farm Center kenan, yadda masu ababen hawa ke ajjiyewa a kan t**i.
Ko me doka tace a kan ajjiye ababen hawa a kan t**i?
Lokacin Daukar Hoto:Litinin,15/06/2026,03:30pm
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
700001
