07/10/2026
Matasan NYSC 20 da aka sace a Imo sun shaƙi iskar yanci
Kafatanin matasan nan 20 da za su tafi aikin yi wa ƙasa hidima na NYSC tare da wani mutum ɗaya da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha a Jihar Imo sun samu ’yanci
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa dukkan waɗanda aka kuɓutar ɗin a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a asibitin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke birnin Owerri.