Northerners Concern

Northerners Concern

Share

VOICE OF THE NORTH

19/02/2026

Barkan mu da shan ruwa...

19/02/2026

Babu wani dan Arewa da ze zabi jam'iyyar APC a zaben 2027 se dan iska
~Sanata Dino Melaye

19/02/2026

Hukumar Hisbah ta k**a mutum tara saboda kin yin azumi a Kano.

16/02/2026

Zargin majalisar dokokin Amurka ga sen. Rabi'u Musa Kwankwaso makarkashiya ce ga siyasar arewacin Nigeria wanda ya k**ata ace shugabanin arewa mun hankalta, mun fito mu wanke dan mu.
~ Hon. Aminu Suleiman Goro

16/02/2026

Dan gwagwarmaya Aminu Warkal ya ajiye mukaminsa na hadimin mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, tare da jaddada mubayi'ar sa ga shugaban darikar kwankwasiyya na duniya Engr. Dr. Muhammad Rabi’u Musa Kwankwaso.

16/02/2026

SANARWA TA MUSAMMAN DAGA COMRD. HUSSAIN SANI IBRAHIM (HON. SPEAKER GWALE)

A yau, bisa ra’ayina kai tsaye — ba ra’ayin wani ba — ina sake jaddada cikakkiyar mubaya’ata, akidata da biyayyata ga jagorancin Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran darikar Kwankwasiyya.

Wannan matsaya tawa ta samo asali ne daga irin cin amanar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir da wasu ‘yan Majalisar Jiha, na Tarayya da shugabannin Kananan Hukumomi s**a aikata. Wadanda gaba daya ba su da karfin kawo kansu kan wadannan muk**ai da suke kai a yau, sai ta sanadiyyar jagoranci da goyon bayan Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso s**a samu wannan dama — damar da ko iyayensu da s**a haife su ba za su iya basu ba.

Abin takaici, a yau su ne s**a juya baya zuwa tsagin da a baya s**a rika kira maciya amanar Jihar Kano.

Tambaya ita ce: shin hakan yana nufin su ma yanzu sun zama maciya amanar Jihar Kano? Me jagora ya aikata musu da har za su saka masa da wannan hali?

Saboda haka, muna nan daram a kan tafarkin jagora. Duk abin da madugu ya ce, shi za mu yi. A Jihar Kano sai abin da jagora ya zartar.

Ku sani cewa daga yanzu wasan siyasa ya fara. Mu a kullum ‘yan gwagwarmaya ne, ‘yan tsagin adawa, kuma wuya ba ta kashe jarumi — sai dai ta kara masa karfi. Ku ci gaba da jin dadi cikin koshin lafiya, domin tafiyar mu ta nasara ba ta da tsayawa.

✊ Muna tare da jagora, kuma nasara tamu ce!

16/02/2026

Kungiyar gwamnonin APC zasu bada tallafin naira biliyan uku N3b ga wadanda iftila'in gobara ya fadawa a kasuwar singa

16/02/2026

Gwamnatin tarayya zata bada tallafin naira biliyan biyar N5b ga wadanda iftila'in gobara ya fadawa a kasuwar singa.

Want your business to be the top-listed Government Service in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Kano