Siyasar Kano Update

Contact the organization

Siyasar Kano Update Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Siyasar Kano Update, Political organisation, Kano.
(1)

Case closed 🔐
07/10/2026

Case closed 🔐

HON. FA’IZU ALFINDIKI YA KARƁI FITILUN SOLAR 250 DAGA SANATA BARAU I. JIBRIN DOMIN HASKAKA KANO MUNICIPALMataimakin Shug...
07/10/2026

HON. FA’IZU ALFINDIKI YA KARƁI FITILUN SOLAR 250 DAGA SANATA BARAU I. JIBRIN DOMIN HASKAKA KANO MUNICIPAL

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya samar da fitilun Solar sama da 250, domin rabawa a mazabu 13 na Ƙaramar Hukumar Kano Municipal.

Hon. Fa’izu Alfindiki, tare da Mataimakin Shugaban APC na Jihar Kano, Alhaji Baba, za su jagoranci rabon fitilun ga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar.

Manufar wannan shiri ita ce haskaka unguwanni da tituna, inganta tsaro, da kuma sauƙaƙa rayuwar al’umma, ta hanyar samar da ingantaccen hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

Daga manyan tituna zuwa ƙananan lungunan birni—za mu ci gaba da haskaka Kano. 💡

Maganar gaskiya, Sanata Barau I. Jibrin na taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar APC da kuma ga...
06/10/2026

Maganar gaskiya, Sanata Barau I. Jibrin na taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar APC da kuma ganin jam’iyyar ta samu ingantaccen tsari da haɗin kai daga sama har ƙasa a Jihar Kano.

Abin da ya fi fitowa fili a siyasarsa shi ne kira da yake yi akai-akai na haɗin kai, fahimtar juna da kauce wa rikicin cikin gida. Duk da dimbin magoya baya da yake da su a sassa daban-daban na Kano, musamman Kano ta Tsakiya da Kano ta Kudu, ya kasance yana bayyana buƙatar a rage sabani, a haɗa ƙarfi wuri guda domin a samu ci gaban jam’iyya.

A siyasar Kano, haɗin kai abu ne mai matuƙar muhimmanci. Jam’iyyar da take son samun gindin zama tana buƙatar shugabanni da magoya baya su fahimci cewa bambancin ra’ayi ba lallai ya zama dalilin rarrabuwa ba. A wannan fanni, Sanata Barau ya ci gaba da bayyana matsayinsa na neman sulhu, haɗin kai da gina jam’iyya mai ƙarfi.

Tun kafin sauye-sauyen siyasar da s**a kawo wasu sabbin daidaito a cikin tsarin APC na Kano, Sanata Barau ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a jihar. Yanzu abin da ake buƙata shi ne ci gaba da gina fahimtar juna tsakanin dukkan ɓangarorin siyasar APC domin tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar.

Muna addu’ar Allah Ya ci gaba da jagorantar shugabanninmu zuwa abin da zai kawo zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban siyasa a Jihar Kano. Allah Ya ba kowa ikon yin siyasa cikin mutunci, haƙuri da kishin al’umma.

Khatimu Kulkul
06 Oct 2026.

06/10/2026

Duk mai son nasarar jam’iyar APC a jihar Kano dole ya goyi bayan zaman lafiya da hadin kai. Lokacin rigima ko kalaman tunzuri ya wuce nasara kawai muke nema.

04/10/2026

Sakon Gwamnan Jihar Kano kan Dambarwar slda take faruwa cikin Jam'iyar APC a Kano ta Arewa, Daga bakin Gwanin Al'kurani Alh Ali Bukar Makoda.

04/10/2026

Sababbin hukumomin tsara birane guda biyu da Gwamnatin Abba Gida Gida ta kirkiro; Kano State Development Control Agency (KADCA) da Kano State Metropolitan Management Agency (KAMMA). Za su mayar da hankali wajen inganta modern urban planning da development control a Kano — tun daga development approvals, zuwa monitoring, compliance da enforcement na dokokin gine-gine.

Wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa biranenmu suna bunkasa cikin tsari na zamani ba harigido da awon igiya, tare da rage gine-gine barkatai marasa tsari wasu ma a magudanan ruwa, sannan hukumomin zasu inganta IGR na Jihar Kano ta hanyar proper planning and development control.

Kabiru Garba ✍🏻

Abdulkadir Hamma Saleh ya fice daga PDP a jihar GombeDaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP kuma tsohon mai neman tiki...
04/10/2026

Abdulkadir Hamma Saleh ya fice daga PDP a jihar Gombe

Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP kuma tsohon mai neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 4 ga Oktoba, 2026, wadda ya aike wa shugabannin PDP na jihar Gombe da karamar hukumar Nafada ta hannun shugaban jam’iyyar na mazabar Nafada West, Hamma Saleh ya ce ya dauki matakin ne saboda dalilai na kashin kansa.

Ficewar Hamma Saleh na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke kara shirye-shirye gabanin babban zaben 2027. Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, yana mai kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, yana mai cewa zai bayyana matakinsa na siyasa na gaba idan lokaci ya yi.

DCL Hausa

03/10/2026

Na ji wasu su na cewa wai Jam’iyyar APC akwai rigima,To muna gaya musu gidan da ba kowa, ana jin magana?”

— Hon. Umar Haruna Doguwa,
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.

03/10/2026

Fire 🔥🔥🔥

DAMBATTA/MAKODA FEDERAL CONSTITUENCY MEGA EMPOWERMENTƊan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dambatta/Makoda Federal Constitu...
03/10/2026

DAMBATTA/MAKODA FEDERAL CONSTITUENCY MEGA EMPOWERMENT

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dambatta/Makoda Federal Constituency ya gabatar da gagarumin shirin tallafawa al’ummar mazabarsa, inda ya raba tulin motoci, tarin babura, kekunan ɗinki, da sauran kayan tallafi masu tarin yawa, kamar yadda kuke gani a cikin hotunan.

Wannan babban shiri ne da zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma, musamman wajen bunƙasa sana’o’i da dogaro da kai.

Lallai ya cancanci yabo da jinjina bisa wannan ƙoƙari na nuna kulawa da jajircewa wajen hidimtawa al’ummar da yake wakilta. Wannan shi ne wakilci na gari da ake bukata.

Khatimu Kulkul
03 Oct 2026.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Siyasar Kano Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Siyasar Kano Update:

Shortcuts

Share