05/10/2026
WADADA YA RABA MOTOCIN SHARON 20 GA ƘUNGIYOYIN GOYON BAYANSA
Ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, ya raba motoci kirar Sharon guda 20 ga ƙungiyoyi, kungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin mata da sauran masu ruwa da tsaki da ke da alaƙa da shirin siyasarsa na 2027.
An raba motocin ga ƙungiyoyi daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da 9 Ward Progressive Forum for Wadada, Project 146 for Wadada, Wadada Links Office Lafia da Akurba Link Movement for Wadada.
Wasu daga cikin cibiyoyin gargajiya da na al’umma ma sun amfana, ciki har da Eze Igbo Palace da ke Lafia, Och’Idoma, Lafia, da Sokoto, Kebbi and Zamfara Forum na Keffi.
Ƙungiyoyin mata ma sun samu motocin, ciki har da Action Women Group, Association of Female Councillors and Female Politicians in Nasarawa State, da Forum of Women Councillors na shiyyoyin Keffi, Akwanga da Lafia.
Sauran waɗanda aka bayyana a matsayin masu cin gajiyar rabon sun haɗa da Pastor Simeon Bakeri, Nasarawa Aid and Relief Foundation, Agatu Forum, Tiv Forum, Panda Concern Group, Alhaji Musa Oduojbo Ago na Keffi, ERCC Headquarters Nasarawa State, da Maulud Committee a Keffi.
A cewar bayanan da aka fitar, manufar rabon motocin ita ce tallafa wa waɗannan ƙungiyoyi wajen gudanar da harkokinsu da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar masu gudanar da ayyukan wayar da kai da hulɗa da al’umma.