26/09/2026
KCPC TA DUBA INGANCI DA NAUYIN JARKOKIN MAN GIRKI A KASUWAR GALADIMA
Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano (KCPC) ta gudanar da aikin duba inganci da nauyin jarkokin man girki da wasu ’yan kasuwa ke sayarwa a Kasuwar Galadima da ke Kano.
An gudanar da aikin ne domin tabbatar da cewa ana bin ƙa’idoji da dokokin da s**a shafi kare haƙƙin masu sayayya, tare da duba tsaftar wuraren da ake gudanar da sana’ar, domin kare lafiyar al’umma.
Da yake jawabi, Sakataren Zartarwar Hukumar, Dr. Ibrahim G. Muhammad , ya bayyana cewa Hukumar za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da kare haƙƙin masu sayayya da kuma tabbatar da cewa kayayyakin da ake sayarwa suna da inganci.
Ya buƙaci al’umma da su riƙa sanya ido tare da kula da dukkan kayayyakin da suke saya, musamman kayayyakin abinci, yana mai cewa rashin kulawa daga masu sayayya na iya ba da dama ga wasu ’yan kasuwa marasa gaskiya su gurɓata ko su sauya ingancin kayayyaki.
Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa irin goyon baya da gudunmawar da take bai wa Hukumar wajen tabbatar da kare haƙƙin masu sayayya da kuma ɗaukar matakan da s**a dace kan duk wani laifi da ya shafi masu sayayya.
A ƙarshe, ya ja hankalin masu harkar man girki da su marawa Hukumar baya wajen yaƙi da gurbatattun kayayyaki da kuma bin ƙa’idojin da aka gindaya, domin kare lafiyar al’ummar Jihar Kano.
Daga:
Jamilu Mustapha Yakasai
Daraktan Wayar da Kai na Hukumar KCPC