30/08/2026
Alhamdulillah! Gwamnatin Jihar Kano Ta Warware Rikicin BUK–Rimin Zakara na Shekaru 50!
Bayan kusan shekaru hamsin na takaddama da tashin hankali, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano, ya ɗauki matakai masu ƙarfi da gaggawa domin kawo ƙarshen dogon rikicin ƙasa tsakanin Jami’ar Bayero Kano (BUK) da mazauna Rimin Zakara.
Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jajirce sosai wajen tabbatar da anyi adalci, sulhu da samar da zaman lafiya mai ɗorewa, ta hanyar biyan diyya ga masu filayen da abin ya shafa, tare da biyan kuɗin gine-ginen da ke kan waɗannan filaye.
Wannan mataki ya zama babban tarihi, domin ya kawo ƙarshen rikicin da ya ɗauki kusan shekaru 50, tare da samar da mafita mai adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Ana gayyatar duk waɗanda abin ya shafa kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta tantance su, da su halarci taron:
📍 Coronation Hall, Jihar Kano
📅 Litinin, 31 ga Agusta, 2026
⏰ 10:00 na safe
Shekaru 50 na rikici. An kawo ƙarshensa. An zaɓi hanyar adalci, sulhu da zaman lafiya.
Abba Kabir Yusuf: Warware tsofaffin matsaloli, dawo da amana, da tabbatar da adalci.
ENGLISH
Alhamdulillah! The 50-Year BUK–Rimin Zakara Crisis Has Been Resolved By Kano State Government
After nearly five decades of dispute and tensions, His Excellency Alhaji Abba Kabir Yusuf, Executive Governor of Kano State, has taken decisive and timely steps to bring an end to the long-standing land dispute between Bayero University Kano (BUK) and the residents of Rimin Zakara.
Governor Abba Kabir Yusuf has made significant efforts to ensure justice, reconciliation and lasting peace through the payment of compensation to affected landowners and payment for structures situated on the affected plots.
This marks a historic milestone, bringing an end to a dispute that has lasted for almost 50 years, while providing a fair resolution for those affected.
All affected persons who have been verified by the Department of State Services (DSS) are invited to attend the programme as follows:
📍 Coronation Hall, Kano State
📅 Monday, 31st August 2026
⏰ 10:00 AM