12/08/2026
A matsayina na matashi mai kishin cigaban matasa da al’ummarmu, na yi imani cewa babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa ba tare da bai wa matasa dama da muhimmancin da s**a cancanta ba.
Na yi imani cewa matasa ba shugabannin gobe kawai ba ne, mu ne ginshiƙan cigaban yau. Muna da basira, ƙwazo, ilimi da hangen nesa da za su iya kawo sauyi mai ma’ana idan aka ba mu dama da goyon baya.
A matsayina na wanda yake da kishin matasa, a kullum ina burin ganin an ƙarfafa matasa ta hanyar ilimi, horo, samar da ayyukan yi, da kuma ba su damar shiga harkokin jagoranci da yanke shawara. Lokaci ya yi da za a daina kallon matasa a matsayin masu jiran gado kawai, a fara kallon su a matsayin abokan hulɗa wajen gina al’umma mai inganci.
Ina kira ga gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara zuba jari a cikin matasa, su saurari muryoyinsu, su ba su dama, tare da samar da yanayin da zai ba su damar amfani da basirarsu domin kawo cigaba da canji mai kyau.
Ga ’yan uwana matasa, ina ƙarfafa mu da mu kasance masu kishin ƙasa da al’umma, masu neman ilimi da cigaba, masu aiki tukuru da kuma masu fata. Mu haɗa kai domin gina makoma mai kyau ga kanmu da waɗanda za su zo bayanmu.
Barka da Ranar Matasa ta Duniya.
Hon Tasi'u Sa'ad Umar {Mai Ishiriniyya }
State Chairman,
Mai Ishiriniyya Movement Kano State.