Alh. Jafar Muhammad Shanono, OON

Website

Alh. Jafar Muhammad Shanono, OON This is the Official page to promote the activities of Alh. Jafar Muhammad Shanono. Jarman Kano, Kano Emirate.
(1)

Officer of the Order of the Niger (OON)
Fmr Talban Karaye
Fmr Ajiyan Kano.

09/10/2026

VIDEO| Isowar Mai Girma Jarman Kano Alhaji Jafar Muhammad Shanono OON, Mai Girma Sarkin Ɓukur Alhaji Nasiru Suleiman Muhammad da Wazirin Ɓukur Alhaji Yakubu Muhammad da tsohon minister Alhaji Bala Borodo da Alhaji Salis Garba Muhammad na SPDC Abuja da dagatan garin Kachako da Shanono da sauran ‘yan uwa da abokan arziki daga wurare daban-daban a kasar nan Masarautar Kano Domin godiya da kuma jaddada mubayi’a Ga Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD CON.

HOTUNA: Yayin Zaman Fadancin Jiya Alhamis 26th  Rabi’ul Thani 1448H/8th October 2026 zuri’ar Sarkin Bukur Muhammadu Dan ...
09/10/2026

HOTUNA: Yayin Zaman Fadancin Jiya Alhamis 26th Rabi’ul Thani 1448H/8th October 2026 zuri’ar Sarkin Bukur Muhammadu Dan Shanono da kuma Murabutawan Shanono da kuma ‘yan uwan Mai Girma Jarman kano Alhaji Jafar Muhammad Shanono OON s**a kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD CON ziyara ta Musamman A Fadarsa Domin godiya da kuma jaddada mubayi’a.

A cikin Wannan Gagarumin tawagar Akwai Mai Girma Sarkin Ɓukur Alhaji Nasiru Suleiman Muhammad da Wazirin Ɓukur Alhaji Yakubu Muhammad da tsohon minister Alhaji Bala Borodo da Alhaji Salis Garba Muhammad na SPDC Abuja da dagatan garin Kachako da Shanono da sauran ‘yan uwa da abokan arziki daga wurare daban-daban a kasar nan da s**a Samu Halarta.

Muna Addu'an Ubangiji Allah Ya karawa Sarki Lafiya Da Imani, Allah Ya karawa Sarki Daraja Da Daukaka, Allah Ya Tsare Mana Shi, Ya karawa Rayuwarsa Albarka, Yan'uwa Da Abokan Arziki Da S**a Samu Damar Halarta Dama Wanda S**ayi Mana Fatan Alkhairi Da Addu'a. Allah Ya karba Mana Amin. Mungode.

Isah Isah Ibrahim ✍🏿
27th Rabi’ul Thani 1448H/9th October 2026.
Photo credit 📸 Majeeda Studio

ALHAMDULILLAH Ya ALLAH Muna Roqonka Ka Kara Mana Son Annabi Muhammadu ﷺ, Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira,  Allah Ya K...
08/10/2026

ALHAMDULILLAH

Ya ALLAH Muna Roqonka Ka Kara Mana Son Annabi Muhammadu ﷺ, Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira, Allah Ya Kara Bamu Lafiya Da Zaman Lafiya, Allah Yasa Lahiran Mu Tafi Duniyan Mu.

Ina Muku Fatan Alkhairi Da Kuma Barka Da Yammaci.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🙏🙏🙏NASIHA CE;Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ruwaito Hadisi daga Annabi ﷺ ya ce: "Kun san w...
08/10/2026

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🙏🙏🙏

NASIHA CE;

Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ruwaito Hadisi daga Annabi ﷺ ya ce: "Kun san wane ne matsiyaci? Matsiyaci daga cikin al'ummata shi ne wanda zaizo ranar alkiyama da Sallah da Azumi da Zakka, amma kuma yazo ya zagi wannan, yayi kazafi ma wannan, yaci kudin wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan...sai a debo daga cikin ladarsa a ba wannan..a ba wannan..har sai ladarsa ta kare bai gama biyan hakkinsu ba, sai a debo zunubansu a jefa masa, sannan a wurga shi cikin wuta". Sahihul Jami' (87).

Allah ya karemu baki daya. Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi ﷺ.

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Warhaka 🙏🙏🙏

26th Rabi’ul Thani 1448H/8th October 2026.

ALHAMDULILLAH.Ya ALLAH Muna Roqonka ka Kara Mana Lafiya Da Zaman Lafiya, ALLAH Yasa Mugama Da Duniya Lafiya, ALLAH Ya Ka...
07/10/2026

ALHAMDULILLAH.

Ya ALLAH Muna Roqonka ka Kara Mana Lafiya Da Zaman Lafiya, ALLAH Yasa Mugama Da Duniya Lafiya, ALLAH Ya Kara Biyawa Kowa Bukatunsa Na Alkairi, ALLAH Ya Sadamu Da Albarkan Dake Cikin Wannan Rana.

Ina Yiwa Kowa Fatan Alkhairi Da Kuma Barka Da Yammaci.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🙏🙏🙏NASIHA CE: SALLAH GINSHIKIN ADDINI...Annabi ﷺ ya ce: "Farkon abinda ake yiwa mutum hisabi...
07/10/2026

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🙏🙏🙏

NASIHA CE: SALLAH GINSHIKIN ADDINI...

Annabi ﷺ ya ce: "Farkon abinda ake yiwa mutum hisabi a kan sa a lahira shi ne Sallah. Idan ta yi kyau sauran ayyukansa za suyi kyau. Idan kuwa ta baci duk sauran ayyukansa zasu ruguje" Sahihul Jámi': 2573

Allah ya bamu ikon kiyaye dokokinsa Bijahi Rasulillahi ﷺ.

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Warhaka.🙏🙏🙏

25th Rabi’ul Thani 1448H/7th October 2026.

ALHAMDULILLAH🙏🙏🙏Ya Allah Yasa Muga Annabi Muhammadu ﷺ, Ya Allah Ya Biyawa Kowa Bukatansa Na Alkhairi, Ya Allah Yasa Mu g...
06/10/2026

ALHAMDULILLAH🙏🙏🙏

Ya Allah Yasa Muga Annabi Muhammadu ﷺ, Ya Allah Ya Biyawa Kowa Bukatansa Na Alkhairi, Ya Allah Yasa Mu gama Da Duniya Lafiya, Ya Allah Ya Bamu Albarkan Dake Cikin Wannan Rana.

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Yammaci.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.Ya Allah don albarkacin sunanka ALQAWIYYU ka Qarfafemu ka karemu daga sharrin maqiya da maha...
06/10/2026

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Ya Allah don albarkacin sunanka ALQAWIYYU ka Qarfafemu ka karemu daga sharrin maqiya da mahassada.

Don Albarkacin sunanka "ALHAFIZU" ka kiyayemu daga sharrin talauci da bashi da sharrin kowanne mugu daga cikin halittu baki daya.

Don albarkacin sunanka ALWADUDU Ya Allah ka hada kanmu, ka Qara mana Qaunar junanmu.

Don albarkacin sunanka ASH SHAFIY Ya Allah ka bamu lafiya daga kowacce chuta, ka warkar da majinyatan mu na gida dana asibiti.

Don albarkacin sunanka AL GAFFARU ka gafarta mana dukkan zunubanmu, ka bamu ikon tuba daga kowanne laifi.

Don albarkacin sunanka AR RAZZAQ ka azurtamu da arziki na halal, ka yalwata ka sanya albarka cikin duk abinda ka bamu.

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Warhaka 🙏🙏🙏

24th Rabi’ul Thani 1448H/6th October 2026.

ALHAMDULILLAH 🙏🙏🙏Ya Hayyu Ya Qayyum Duhun KabariFitinar KabariKuncin KabariBala'in Kabari Ya Allah Kai ne mafi tausayin ...
05/10/2026

ALHAMDULILLAH 🙏🙏🙏

Ya Hayyu Ya Qayyum

Duhun Kabari
Fitinar Kabari
Kuncin Kabari
Bala'in Kabari

Ya Allah Kai ne mafi tausayin masu tausayi, mafi karamcin masu karamci. Ya Allah don tausayin nan naka gare mu ka kyautata rayuwarmu, ka ji kanmu duniya da lahira.Ya Allah Ka kiyashe mu daga zafin fitar rai, da azabar kabari da kuma mummunar makoma. Don karamcin nan naka Ya Allah ka bamu mafi kyawu a duniya da lahira. Ya Allah Ka kiyaye mu daga sharrin masu sharri. Allah ya bamu albarkar dake cikin rayuwar mu ta duniya da lahira Bijahi Rasulillahi ﷺ 🙏🙏🙏

Ina muku fatan Alkhairi Da Kuma Barka Da Yammaci.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM HATSARIN MUTUWA DA BASHI AKAN KAManzon Allah ﷺ Yace: “Na Rantse Da Wanda Raina Yake Hannunsa...
05/10/2026

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

HATSARIN MUTUWA DA BASHI AKAN KA

Manzon Allah ﷺ Yace: “Na Rantse Da Wanda Raina Yake Hannunsa, Da Za'a Kashe Mutum Ta Hanyar Ɗaukaka Addinin Allah (ﷻ), Sai A Rayar Dashi, Sannan A Sake Kashe Shi, Sannan a Ƙara Rayashi, Sannan a Sake Kashe Shi, Sannan a Kuma Kashe Shi Da BÃSHI Akansa, Bazai Taɓa Shiga Aljannah ba Har Sai An Biya Masa Wannan Bashin”.
{Nisã'i Ya Ruwaitoshi}

Allah ya tsare mu. Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi ﷺ

23rd Rabi’ul Thani 1448H/5th October 2026.

Address

Shanono LG
Kano
704102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alh. Jafar Muhammad Shanono, OON posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share