01/09/2026
Gwamnan Kano Ya Shafe Dare Yana Ziyartar Taron Mauludi A Fadin Jihar
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ziyarar dare zuwa wuraren tarukan Mauludi daban-daban a fadin jihar, domin nuna goyon bayansa ga harkokin addini da kuma karfafa alaka tsakanin gwamnati da malaman addini.
Gwamnan ya bar gidan gwamnatin Kano da misalin karfe 10 na dare, inda ya ci gaba da ziyartar wuraren tarukan Mauludi har zuwa safiyar yau. Ya dawo fadar gwamnatin jihar da misalin karfe 7:02 na safe bayan kammala rangadin.
A yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarci tarukan Mauludi da aka shirya a wurare daban-daban da s**a hada da:
1. Sheikh Sharif Sani Jambulo
2. Gidan Qadiriyya
3. Sheikh Maihula
4. Sheikh Aliyu Harazimi
5. Sheikh Malam Kamaluddeen Adamu Nama’aji Alfindiki
6. Sheikh Atiku Sanka
7. Sheikh Mudi Salga
8. Sheikh Tiljani Yan Mota
Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da s**a hada da Sakataren Gwamnatin Jihar, Kwamishinonin Harkokin Addini, Lafiya, Ayyuka, Wutar Lantarki, Kananan Hukumomi, masu ba da shawara na musamman kan harkokin addini, siyasa da hulda tsakanin jam’iyyu, tare da Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa.
WAKILCIN MATAIMAKIN GWAMNA
Saboda yawan tarukan Mauludi da ake gudanarwa a fadin jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, tare da wasu jami’an gwamnati domin wakiltarsa a wasu tarukan.
Wadannan wurare sun hada da:
1. Sheikh Yusuf Makwarari
2. Malam Garba Maimandiri Tudun Nufawa
3. Sheikh Sani Kafinga
4. Gidan Baba Kusa
5. Sheikh Uba Mandawari
6. Sheikh Musa Kalla
7. Sheikh Dan Almajiri
Tawagar Mataimakin Gwamnan ta kunshi Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Kwamishinonin Yada Labarai, Kiwo, Kudi, Albarkatun Ruwa da Muhalli, Kasafin Kudi da Tsare-tsare, da kuma mai ba Gwamna shawara kan harkokin addini, tare da Hon. Mukhtar Ishaq Yakasai.
WAKILCIN SHUGABAN MAJALISAR JIHAR
Haka kuma, Gwamnan ya wakilta Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, tare da wasu jami’an gwamnati domin halartar wasu tarukan Mauludi.
Wuraren da tawagar ta ziyarta sun hada da:
1. Malam Nasidi Goron Dutse
2. Sheikh Uwais Limanci
3. Sheikh Nazifi Alkarmawi
4. Zawiyyar Malam Hamza Gyaranya
5. Malam Yunusa Akwa
6. Malam Alhaji Maikasida Mazankwarai
7. Alhaji Kabiru Sani Kwangila
Tawagar Shugaban Majalisar ta kunshi Kwamishinonin Raya Karkara, Gidaje, Ilimi, Bibiyar Ayyuka, Sufuri, Filaye da Tsare-tsaren Birane, da masu ba da shawara kan harkokin Majalisa da Tsangaya, tare da Hon. Baffa Takai.
Yawan halartar gwamnati da wakilci a wadannan tarukan Mauludi na nuna kokarin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wajen bunkasa zaman lafiya tsakanin addinai, karfafa alaka da malaman addini da cibiyoyin Musulunci, tare da kasancewa tare da al’umma a lokutan muhimman bukukuwan addini.
CRC Media Centre