mu koyi musulunci daga malaman mu

mu koyi musulunci daga malaman mu

Share

“Shafi domin yada ingantaccen ilimin Musulunci daga Alƙur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na ƙwarai.”

23/05/2026

🌸 Kyawawan Ɗabi’un Manzon Allah (ﷺ) 🌸
Daga Anas Ɗan Málik (R) ya ce: ((Ya wuce ta kusa da wasu yara ƙanana sai ya yi musu Sallama, sannan ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana yin hakan))

📚 Sahihul Bukhári.
✨ Wannan yana nuna irin tawali’u da rahamar Manzon Allah (ﷺ). Duk da matsayinsa, yana kula da yara yana gaishe su cikin fara’a da ƙauna.

🤝 Mu ma mu koya yin sallama da fara’a ga manya da yara, domin sallama tana ƙara soyayya da haɗin kai a tsakanin Musulmi.

23/05/2026

Tanadin kiyama

23/05/2026

🌿 MUHIMMANCIN ZIKIRI 🌿
Manzon Allah (ﷺ) ya ce:
((Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa (Zikiri) da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce))
📚 Sahih al-Bukhari 6407

✨ Darasi:
Zikiri yana raya zuciya, yana kawo nutsuwa da kusanci ga Allah. Kada ka bari harshenka ya daina ambaton Allah.
🤲 Allah Ka sanya mu cikin masu yawan zikiri.

Kuna jin daɗin wadannan sakonnin hadisai me zakuce

22/05/2026

🌸 KYAKKYAWAR MU’AMALA KO DA GA DABBA 🌸

Daga Shaddadu Dan Aus (R), Manzon Allah (ﷺ) ya ce:
((Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa a dukkan komai. Idan za ku kashe, ku kyautata kashewa. Idan kuma za ku yanka (dabba), ku kyautata yankawa. Ɗayanku ya wasa wuƙarsa, sannan ya hutar da abin yankansa)).
📚 Sahih Muslim

✍️ Darasi:
Musulunci addini ne na rahama da tausayi. An umurce mu da kyautatawa a cikin komai, har ma da yadda ake mu’amala da dabbobi.
🤲 Allah Ka sanya mu cikin masu kyautatawa a dukkan al’amuranmu

21/05/2026

Kuce Ameeeen yen uwa Musulmai albarkacin wannan watan

20/05/2026

💔 DAMUWA!!! 💔

Wani lokacin kana ganin damuwarka ita ce mafi girma…
Sai kuma ka ji labarin wani, ko ka ga halin da wani yake ciki, sai ka gane cewa har yanzu kana cikin ni’imar Allah mai yawa.
Akwai mutanen da suke murmushi alhali zuciyarsu cike take da ciwo…
Akwai masu fama da matsaloli amma babu wanda ya sani sai Allah.
Shi ya sa kada ka manta da ‘yan uwanka a cikin addu’a. 🤲
Ka roƙi Allah Ya yaye musu damuwa, Ya sauƙaƙa musu rayuwa, Ya cika musu zukata da nutsuwa.
Wataƙila addu’ar da za ka yi wa wani ita Allah zai sa ta zama sanadin warware damuwarka. ✨
Ka daina raina damuwar mutane, domin kai ba ka san irin nauyin da suke ɗauke da shi a zuciyarsu ba.
Mu zama masu tausayi, masu addu’a, masu fatan alkhairi ga juna. 🤍

20/05/2026

🌙 Hadisi Kan Layya 🌙

Daga Anas ibn Malik (R) ya ce: ((Muhammad (ﷺ) ya yi layya da raguna biyu masu launin fari gauraye da baƙi masu ƙahonhuna, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah (Bismillahi), tare da yin kabbara (Allahu Akbar), sannan ya ɗora ƙafarsa a gefen wuyansu))
📚 Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim.

📝 Darasi: Hadisin yana nuna falalar yin layya da kuma yadda Muhammad (ﷺ) ya kasance yana yin ta da kansa cikin tsoron Allah da ambaton sunansa.

20/05/2026

Kasan shekarun masifu saurara har ƙarshe kaji

20/05/2026

Ina masu hankalin cikin mu ku saurara zaku fahimta

19/05/2026

🌙 Falalar Kwanaki Goman Farkon Zul-Hijjah
Daga Abdullahi Ɗan Abbas (R) Manzon Allah (ﷺ) ya ce:
((Babu wasu kwanaki da aikin alkhairi a cikin su ya fi soyuwa a wajen Allah fiye da waɗannan kwanakin — yana nufin kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah. Sai Sahabbai s**a ce: Ya Manzon Allah, ko da kuwa Jihadi ne saboda Allah? Ya ce: Ko da kuwa Jihadi ne saboda Allah, sai dai mutumin da ya fita Jihadi da ransa da dukiyarsa sannan bai dawo da komai daga cikinsu ba))
📚 Bukhárí.

✨ Darasi: Wadannan kwanaki dama ce mai girma ga:
Sallah
Azumi
Zikiri
Sadaka
Karatun Alƙur'ani
Yawaita istigfari
Kada mu bari kwanakin su wuce ba tare da kyawawan ayyuka ba. 🤍

Kuyi share don wasu ma su amfana

19/05/2026

✨ Manzon Allah (ﷺ) ya koyar da mu cewa mafi kyawun ɗabi'un Musulunci sun haɗa da ciyar da mabukata da kuma yaɗa sallama tsakanin mutane. 🤝🍽️

Wani mutum ya tambayi Manzon Allah (ﷺ) cewa: ((Waɗanne ɗabi'u (ayyuka) na Musulunci s**a fi? Sai ya ce: Ka ciyar da abinci (ga mabuƙata), kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba))
📚 Sahih al-Bukhari 28

Want your business to be the top-listed Government Service in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Kano Nigeria
Kano