05/08/2025 Oyoyo Abban kanawa GWAMNAN JIHAR KANO ALH ABBA KABIR YUSUF YA GABATAR DA SABBIN MA’AIKATA 1,038 A BANGAREN NOMA A yau, Litinin 4 ga Agusta, 2025, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wani taron haɗin gwiwa tare da wasu daga cikin sabbin ma’aikata 1,038 da gwamnatin jihar ta dauka aiki a bangaren noma. Taron ya gudana a dakin taro na Coronation Hall, da ke cikin Fadar Gwamnatin Jihar Kano. Wannan mataki na daukar sabbin ma’aikata wani bangare ne na shirye-shiryen gwamnatin jihar na inganta harkar noma da tabbatar da dorewar samar da abinci a cikin jihar. Sabbin ma’aikatan za su rinka aiki a fannoni daban-daban na noma, ciki har da hanyoyin zamani na kiwon amfanin gona, kula da gonaki, kiwon dabbobi, da kuma wayar da kan manoma kan sabbin dabarun noma. A yayin taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafa wa manoma da bunkasa tattalin arzikin karkara ta hanyar samar da kwararru a bangaren noma, tare da basu horo na musamman domin inganta ayyukansu. Sabbin ma’aikatan dai sun fito ne daga dukkan kananan hukumomin jihar, domin tabbatar da cewa dukkan yankuna sun amfana daga wannan shirin. Wannan na daga cikin matakan gwamnati na rage matsalar rashin aikin yi da bunkasa tattalin arzikin jihar ta hanyar noma.