KARIMIN GWAMNA 😇
FALLE BIYU CE DA YARDAR ALLAH
Aky2027 BichiFirst Strategic Network
AKY 2027 – Bichi First Strategic Network is a grassroots political movement in Bichi Local Government
01/04/2026
President Bola Ahmed Tinubu has appointed Prof. Yusuf Mohammed, Kano State APC Secretary as the Chairman Governing Council of the Federal Polytechnic Kaltungo.
Congratulations sir👏
Bichi always First.
Wannan gadar damargu ce wadda zababben dan majalissar tarayyar mai wakiltar karamar hukumar bichi Hon. Abubakar kabir abubakar ya aiwatar.
wannan gada tana daya daga cikin muradan marigayi Alh kabiru abubakar, mahaifi ga Hon abba bichi. wanda Allah bai bashi damar yi ba, cikin ikon Allah daya daga cikin jajirtattun yayansa ya çıka masa wannan muradi.
Allah ya sakawa Hon abba bichi da alkhairi ya jiqan magabata, Amin.
Ahmad Mohd Garba
DG. Bichifirst strategic network.
24/03/2026
GWAMNONIN NAJERIYA SUN HALARCI BIKIN KARƁAR BAKUNCIN GWAMNAN ZAMFARA
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorinsa gwamnonin jihohin Najeriya, sun halarci bikin karɓar bakuncin Gwamnan Jihar Zamfara, H.E Dauda Lawal, a wani taro mai cike da armashi da muhimmanci ga harkokin shugabanci a ƙasar nan.
A wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa, H.E Kashim Shettima, CON, ya wakilci Shugaban Ƙasa, inda ya isar da saƙon gwamnati kan buƙatar ƙarfafa haɗin kai tsakanin matakan gwamnati domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ministoci, shugabannin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki, lamarin da ya nuna yadda shugabannin ƙasar ke ba da muhimmanci ga irin waɗannan tarurruka domin tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi rayuwar al’umma.
A cikin jawabai da aka gabatar, an jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jihohi wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, bunƙasa tattalin arziki, inganta ilimi da lafiya, tare da samar da ayyukan yi ga matasa.
Haka kuma, an nuna cewa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin shugabanni na da matuƙar tasiri wajen samar da nagartaccen shugabanci.
Masu sharhi na ganin cewa irin wannan taro na taimakawa wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin shugabanni, da kuma samar da sabbin hanyoyi na haɗin gwiwa da za su amfani al’umma.
Taron ya gudana cikin nasara, tare da nuna kyakkyawar alama ta haɗin kai da ƙudurin ciyar da Najeriya gaba.
Falle biyu ya Allah 🤲
Alfarmar watan Ramadana.
Abba4+4
#
Click here to claim your Sponsored Listing.
