APC Social Media Organisation Katsina State

APC Social Media Organisation Katsina State

Share

All Progress Congresses

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 13/05/2026

Sakamakon Zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina na 8 a Shekarar 2026

Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ta gudanar da Taro na 8 a shekarar 2026 a yau Laraba, 13 ga Mayu, 2026, inda ta tattauna kan muhimman abubuwa da rahotanni da aka gabatar mata tare da amincewa da abubuwa kamar haka:

1. Amincewa da ɗaukar ƙarin matasa 361 a sashe na biyu na shirin koyon noma da kiwo na zamani na Dikko Radda Agric Training and Empowe Program a Cibiyar Horaswa ta Makera Songhai da ke Dutsin-ma. Shirin horaswar zai mayar da hankali kan bunƙasa ƙwarewar matasa a tsarin noma na zamani da ya haɗa fannoni daban-daban, ciki har da noman amfanin gona, kiwo, kiwon kifi, sarrafa kayayyakin noma da shi kanshi kasuwancin noma.

2. Amincewa da karɓa tare da yaɗa sakamakon Binciken Gidaje (General Household Survey – GHS) na shekarar 2025. Wannan amincewar na da nufin aiwatar da tsarin bunƙasa karkara, tare da amfani da bayanan binciken a matsayin abin dogaro ga jihar domin magance ƙarancin ingantattun bayanai da ke kawo cikas ga tsare-tsaren gwamnati, wasu Ma’aikatu, Hukumomi da kuma abokan hulɗar ci gaba da ke zuwa jihar.

3. Amincewa da bayar da kwangilar kammala cibiyar halba ruwa ta zamani da sauran kayayyaki a Madatsar Ruwa dake Ajiwa. Wannan aiki zai taimaka wajen dawo da aikin madatsar ruwan tare da ƙara yawan samar da ruwa ga birnin Katsina da garuruwan dake kewaye da ita.

4. Amincewa da ƙara alawus ɗin tallafin karatu (Scholarship) da kashi 100 ga ɗaliban jihar da ke karatu a manyan makarantu daban-daban a faɗin ƙasar nan. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na faɗaɗa damar samun ilimi, rage wa ɗalibai nauyin kuɗaɗen karatu da kuma ƙarfafa ƙwazon karatu.

5. Amincewa da bayar da kwangilar cigaba da aikin sabon Filin Wasanni na Garin Charanchi, wanda ya haɗa da gina filin ƙwallon ƙafa na zamani, shimfiɗa ciyawa ta zamani, babban ɗakin wasanni na bai daya da sauran ayyuka. Idan aka kammala aikin, filin wasan zai zama ingantaccen cibiyar wasanni ta zamani.

6. Amincewa da bayar da kwangilar saka ciyawa ta zamani mai inganci (FIFA Quality Pro-Generation Hybrid Synthetic Grass) a Filayen Wasanni na Malumfashi da Funtua. Aikin na da nufin mayar da filayen wasan zuwa matakin ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa harkokin wasanni da bunƙasa ruhin wasanni a tsakanin matasan jihar.

7. Amincewa da ƙaddamar da shirin bayar da tallafin karatun jami’a na musamman ga ɗalibai 50 mafi hazaƙa daga kowace ƙaramar hukuma 34 ta jihar. Tallafin zai haɗa da biyan kuɗin makaranta gaba ɗaya tare da ba su alawus na shekara-shekara. Shirin na da nufin bai wa hazikan ɗaliban jihar damar ci gaba da karatu ba tare da tangarda ta rashin kuɗi ba.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 13, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 13/05/2026

‎Cikin Hotuna: Yadda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ya Sabunta Zauren Majalisar Zartarwa Dake Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Wadda Aka Maidata Ta Zamani, Aka kuma Ƙaddamar da ita a yau Laraba 13 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki ta 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 12/05/2026

“Jihar Katsina ta Zama Abin Koyi Wajen Tsarin Samar da Tsaro Mai Dogaro da Al’umma (Community)”- Rundunar Sojan Nigeria

A ranar talata, 12 ga Mayu, 2026, Rundunar Sojin Najeriya ta yabawa Gwamnatin Jihar Katsina bisa ingantaccen tsarin tsaro mai dogaro da haɗin kan al’umma, inda ta bayyana jihar a matsayin abin koyi a ƙasa wajen haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da al’umma domin magance matsalolin tsaro.

Daraktan Sashen Nazarin Haɗin Gwiwa na Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Sojoji (Armed Forces Command and Staff College-AFCSC) da ke Jajin jihar Kduna, Birgediya Janar K. Rabiu ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da Tawagar Nazari ta 5 ta manyan jami’ai (Study Group 5 of Senior Course 48) ta kai Gidan Gwamnatin Katsina.

Ziyarar na cikin shirin rangadin nazari na muhalli mai taken: “Ƙarfafa Haɗin Kan Al’umma Domin Inganta Tsaro da Wadata ta Ƙasa.” Birgediya Janar Rabiu ya bayyana cewa an zaɓi Katsina cikin jihohi bakwai saboda muhimmancinta da kuma sabbin tsare-tsaren tsaro da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Ya ce tawagar ta ƙunshi mutum 91 da s**a haɗa da ɗaliban manyan hafsoshin soja, malamai da jami’an gudanarwa, tare da wasu ɗalibai daga ƙasashen Gambia, Côte d’Ivoire da Liberia. Ya ƙara da cewa manufar ziyarar ita ce nazarin hanyoyin haɗin kan al’umma da jami’an tsaro wajen magance matsalolin tsaro.

Birgediya Janar Rabiu ya yabawa Gwamnatin Jihar Katsina bisa samar da kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin jama’a da jami’an tsaro, yana mai cewa irin wannan haɗin kai na da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa da tsaron ƙasa.

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa tsaro ta hanyar bai wa al’umma damar taka rawa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

Gwamnan ya bayyana irin nasarorin da aka samu ta hannun rundunar Katsina State Community Watch Corps, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen inganta tattara bayanan sirri da kuma saurin kai dauki saboda sanin yankuna da yanayin al’umma da jami’an ke da shi.

Gwamna Radda ya jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa da kowa, tare da kira ga ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin sojoji, ‘yan sanda, sarakunan gargajiya da sauran ƙungiyoyin tsaron al’umma.

Haka kuma ya yi gargaɗi ga masu bai wa yan ta’adda bayanai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar, ciki har da matakan tsaron makarantu da ake aiwatarwa.

Zaman ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, Alh Faruk Lawal Jobe, Kakakin Majalisa, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, Alƙalin Alƙalai, Justice Musa Danladi, Grand Khadi, Sakataren Gwamnati, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 12, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 12/05/2026

Gwamna Radda Ya Kaddamar da Kwamitin Farfado da Zaman Lafiya na Shirin DDR a Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da Kwamitin farfado da Zaman Lafiya da Tsaro (State Disarmament, Demobilization and Reintegration -DDR), a wani bangare na kokarin gwamnatin jihar na inganta zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyi, da samar da hanyoyin warware rikice-rikice a fadin jihar.

Wannan shiri ya samo asali ne daga Tsarin Manufofin Kasa da Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC) tare da hadin gwiwar Shirin Birtaniya na Karfafa Zaman Lafiya da Juriya a Najeriya (UK SPRING) s**a tsara bayan gudanar da tuntubar yankuna shida na kasar nan.

An zabi Jihar Katsina a matsayin daya daga cikin jihohin gwaji wajen aiwatar da shirin saboda irin kokarin da take yi na inganta tsaron al’umma ta hanyar hadin kai da amfani da hanyoyin zaman lafiya wajen magance matsalolin tsaro.

Kwamitin ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki daga hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, malamai, da kungiyoyin fararen hula.

Mambobin Kwamitin:

1. Secretary to the State Government — Chairman
2. Honourable Attorney-General of the State
3. Honourable Commissioner, Ministry of Internal Security and Home Affairs
4. Honourable Commissioner, Ministry of Agriculture
5. Honourable Commissioner, Ministry of Youths and Sports Development
6. Special Adviser, Community Security Watch
7. State Commandant, Katsina State Community Security Watch Corps
8. Executive Secretary, SEMA
9. Executive Director, Katsina State Development Management Board
10. Chairman, House Committee on Security
11. Representative of the Nigeria Police Force
12. Representative of Katsina Emirate Council
13. Representative of Daura Emirate Council
14. Representative of the Council of Ulama
15. Representative of Civil Society Organizations
16. Governor’s Office/MISHA — Secretariat

An dorawa kwamitin alhakin bai wa gwamnati da Majalisar Tsaro shawara kan harkokin farfado da zaman lafiya ta hanyar shirin na DDR, da tsaron al’umma. Haka kuma zai kula da tantancewa, rajista, gyaran hali, da sake shigar da mutanen da s**a ajiye makamai cikin al’umma domin rungumar zaman lafiya.

Gwamna Radda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da amfani da hanyoyin inganta tsaro, hadin gwiwa, da dabarun zaman lafiya wajen magance matsalolin tsaro da tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar Katsina.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, Alh Faruk Lawal Jobe, Kakakin Majalisa, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, Alƙalin Alƙalai, Justice Musa Danladi, Grand Khadi, Sakataren Gwamnati, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 12, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 12/05/2026

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Samu Gagarumin Yabo Kan Ci Gaban Lafiya da Horar da Kwararrun Likitoci

An yiwa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda wannan yabo ne, a ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026, a lokacin da tawagar masu sake tantance ƙwararrun likitoci daga sashen Obstetrics and Gynaecology na Kwalejin likitoci na Afrika ta yamma s**a kawo mashi ziyarar ban girma ga Mai Girma Gwamnan a ofishin sa bayan kammala aikin sake tantancewa (re- accreditation) a asibitin Turai Yar’Adua Maternal and Children.

Tawagar ta bayyana gamsuwa da irin gagarumin sauyi da ci gaba da s**a gani a asibitin idan aka kwatanta da ziyarar da s**a kawi asibitin shekaru biyu da s**a gabata, tare da yabawa gwamnatin jihar bisa jajircewa wajen bunƙasa ɓangaren lafiya da horar da likitoci masu neman ƙwarewa ta musamman (Residency Training) a cikin jihar.

Masu tantancewar sun bayyana cewa tsawon shekaru da dama likitocin jihar suna fita zuwa wasu manyan asibitocin ƙasar nan domin samun horon ƙwarewa, sai dai a yanzu gwamnatin Gwamna Radda ta samu nasarar samar da sassa shida da aka amince da su domin gudanar da irin wannan horo a asibitocin gwamnati na jihar Katsina, lamarin da zai rage wahalar tura likitoci zuwa wasu jihohi domin ƙarin horo.

A nasa jawabin, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa ɓangaren lafiya fifiko tare da samar da ingantattun kayan aiki da horo domin tabbatar da samun nagartaccen tsarin kula da lafiya ga al’umma.

A wani ɓangaren kuma, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya Hon. Musa Adamu Funtua, ta gabatar wa Mai Girma Gwamna jerin lambobin yabo da karramawa da gwamnatin jihar ta samu sakamakon ci gaban da aka samu a ɓangaren lafiya.

Daga cikin karramawar akwai lambar yabo daga Hukumar Rajistar Ma’aikatan Kiwon Lafiyar Al’umma ta Najeriya a matsayin gwamnan da yafi kowane gwamna daukar ma’aikatan lafiya a Nigeria, da kuma kyautar “Nurse-Friendly Governor’s Award” daga National Association of Nigeria Nurses and Midwives bisa irin gudunmawar gwamnatin jihar wajen bunƙasa harkokin jinya da ungozoma.

Jihar Katsina ta kuma samu lambobin yabo kan sakin kuɗaɗen tallafi domin yaƙi da cututtuka masu yaduwa, tattara kuɗaɗen cikin gida domin shirye-shiryen lafiya, da kuma matsayi na biyu a ƙasa baki ɗaya wajen tsarin kula da rarraba kayayyakin magungunan zazzabin cizon sauro na shekarar 2025.

Waɗannan karramawa na nuna irin ci gaba da gwamnatin Gwamna Radda ke samarwa a ɓangaren lafiya da kuma yadda ƙoƙarin gwamnatin ke ci gaba da samun karɓuwa daga hukumomi da ƙungiyoyi na ƙasa da na duniya.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 12, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 11/05/2026

Gwamna Radda Ya Cika Alkawari, Ya Bai Wa Hazikan Ɗaliban KTISM Kyautar Motoci

A ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya cika alkawarin da ya yi wa ɗalibai biyu da s**a zama zakaru cikin ɗaliban makarantar kimiyya da fasaha ta Katsina Institute of Technology and Management (KTISM), a lokacin bikin yaye ɗaliban makarantar da ya gudana a cikin watan da ya gabata.

​Wannan karramawa ta zo ne a matsayin lada ga ƙoƙari da kuma kwarin gwiwa ga sauran ɗaliban jihar su jajirce wajen neman ilimi, musamman a ɓangaren kimiyya da fasahar zamani.

​Zakarun ɗaliban da S**a Samu Kyautar wannan karramawa su ne:​Ibrahim Mainasara Bugaje: Daga sashen Networking and System Security, wanda ya kammala da maki mai ban mamaki na 4.92 (CGPA),
​Aisha Isyaku: Daga sashen Computer Software Engineering, wanda ta samu maki na 4.75 (CGPA).

Da yake hannanta makullan motocin ga ɗaliban, Gwamnan ya bayyana farin cikin shi bisa samun damar cika alkawarin da ya dauka, ya kuma ja hankalin ɗaliban da su kara zage damtse wajen samun nasara a dukkanin matakin da s**a tsinci kansu a ciki.

Shugaban makarantar Dr. Musa Zayyad wanda ya samu wakilcin Hayatu Khalel Bako wanda ya samu rakiyar Librarian Dr. Hindatu Salisu Abubakar, da Bursar Mal Mustapha Abubakar Sadauki, iyayen yaran da dai sauran su.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 11, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 10/05/2026

Gwamna Radda Ya Yi Bankwana da Maniyyata Aikin Hajji Mutane Sama Da Dubu Biyu Na Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi bankwana da maniyyata aikin Hajji kimanin mutane 2,035 daga jihar kafin tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Da yake jawabi yayin taron bankwana da aka gudanar a sansanin Alhazai (Hajj Camp) na Jihar Katsina, Gwamna Radda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali ga dukkan maniyyatan jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar wa maniyyatan kayan tallafin Sallah kamar yadda aka saba yayin da suke ƙasa mai tsarki, tare da kira gare su da su kasance jakadu nagari na Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya a lokacin zamansu a Saudiyya.

Gwamnan ya kuma shawarci maniyyatan da su yi amfani da kuɗaɗen alawus ɗin tafiyarsu cikin hikima tare da dagewa wajen yi wa jihar da ƙasa addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

Gwamna Radda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin jami’ai 240 domin kula da gudanar da harkokin aikin Hajji cikin nasara. Jami’an sun haɗa da malaman addini, ma’aikatan lafiya, masu ɗaukar kaya, jami’an hukumar jin daɗin Alhazai da sauran wakilan gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin shugaban tawagar gwamnati- Amirul Hajj.

Haka kuma, Gwamnan ya umarci shugabannin tawagar da su sanya ido sosai kan yadda jami’an da aka tura aikin ke gudanar da ayyukansu tare da kai wa gwamnati rahoto kan yadda s**a gudanar da aikinsu.

Tun da farko, Amirul Hajj kuma shugaban tawagar jihar, Barrista Ahmed Usman El-Marzuk, ya gode wa gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi musu na jagorantar maniyyatan jihar zuwa ƙasa mai tsarki. Ya bayyana cewa an gudanar da tarurruka daban-daban domin wayar da kan jami’an aikin Hajji kan nauyin da ke kansu.

A nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama, ya yaba wa Gwamna Radda bisa ci gaba da ba da goyon baya domin nasarar gudanar da aikin Hajji a jihar.

Shi ma kwamishinan Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Farfesa Sheikh Bin Usman, wanda Alhaji Umar Kalgo ya wakilta, ya sanar da ƙaddamar da katin shaidar Nusuk Card, wanda zai zama katin izinin shiga Masallacin Harami da sauran wurare masu tsarki a Saudiyya.

Sauran masu jawabi a wajen taron sun shawarci maniyyatan da su kasance masu biyayya ga doka, ladabi da kyawawan ɗabi’u tare da kauce wa duk wani hali da zai ɓata sunan Jihar Katsina da Najeriya a ƙasa mai tsarki.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 10, 2026

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 09/05/2026

Gwamna Radda Ya Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki na Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira da a inganta haɗin kai, kusanci da al’umma, da kuma inganta hanyoyin sadarwa tsakanin masu ruwa da tsaki na siyasa a jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja, wanda ya haɗa manyan jami’ai daga Katsina masu mukamai a gwamnatin tarayya, ‘yan majalisar dokoki, shugabannin hukumomi, ‘yan takarkari da sauran jiga-jigan siyasa.

Gwamna Radda ya jaddada buƙatar farfaɗo da kungiyar masu ruwa da tsaki na Jihar Katsina (Katsina Stakeholders’ Forum) domin ƙarfafa haɗin kai da haɗa hannu wajen ci gaban siyasa da shugabanci a jihar da yankin.

Haka kuma, ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ci gaba da bayyana nasarori da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ƙarfafa hulɗa da al’umma ta hanyar amfani da kafafen sadarwa da kuma ƙarfafa ayyukan siyasa a daga tushe.

Taron ya kuma tattauna batutuwan shugabanci, siyasa, ƙara tallafawa hukumomin tarayya, da kuma damuwar da ake da ita kan ƙarancin wakilcin yankin Arewa maso Yamma a ɗaukar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 9, 2026.

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 08/05/2026

HOTUNA

Yadda gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya halarci ofishin jam’iyyar APC na kasa don tantancewa a matsayin dan takarar gwamna a kakar zaben shekarar 2027.

08/05/2026

Kwamitin Tantance Gwamnonin Jam'iyyar APC Wadanda Suke Neman Sake Tsayawa Takara Ko Masu Neman Takarar Kujirar Majalisar Dattawa.

Mai Girma Zababben Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Farfesa Nentawe Yilwatda Shi Zai Jagoranci Kwamitin Tantance Gwamnoni Na Jam'iyyar APC Yayin Da Sakataren Jam'iyyar APC Na Kasa, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, Ph.D, Ya Zama Sakataren Kwamitin Tantance Gwamnoni, Sauran Membobin Kwamitin Sun Hada Da Membobin APC National Working Committee Da Sauran Su.

Za'a Gudanar Da Tantance Gwamnoni Masuci Dake Neman Sake Tsayawa Takara Ko Neman Kujerun Majalisar Dattawa Ne Daga Ranar Juma'ah, 8 Ga Watan Mayu Zuwa Asabar, 9 Ga Watan Mayu, 2026, a Rana Ta Farko Za'a Fara Zaman Tantancewa Daga Karfe 4:00 Na Yamma a Rana Ta Biyu Kuma Za'a Fara Da Karfe 10:00 Na Safe.

An Shirya Tantance Duk 'Yan Takarar Gwamna Daga Asabar, 9 Ga Mayu Zuwa Lahadi, 10 Ga Mayu, 2026, a Zauren APC National Working Committee ( NWC ) Sakatariyar APC Ta Kasa, Dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Rabi'u Garba Gaya !

Photos from APC Social Media Organisation Katsina State's post 07/05/2026

LABARI CIKIN HOTUNA:

Yadda gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya mayar da fom din tsayawa takara ga kwamitin tantancewa na jam’iyyar APC a Abuja.

Satin da ya gabata ne maigirma gwamna ya yanki tikitin sake tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina karo na biyu a kakar zaben shekarar 2027 dake tafe.

Gwamna ya samu rakiyar jiga-jigab jam’iyyar da masu ruwa da tsaki ciki hadda tsohon gwamna, Malam Aminu Bello Masari, Sanata Abu Ibrahim, Alh Dahiru Barau Mangal, Kakakin Majalisar Dokoki, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, shugaban jam’iyyar na jihar, Dr. Bishir Gambo Saulawa, yan takarkarin jam’iyyar APC, yan majalisu, chiyamomi, jami’an gwamnati da sauransu.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 7, 2026.

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Katsina