18/05/2026
Minista Darma Ya Tallafawa Dalibai 33 Kudin Rubuta Jarabawar NECO a Katsina
Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ya bayar da tallafin sama da Naira Miliyan ɗaya (1,072,000) domin biya wa dalibai 33 kudin rubuta jarabawar NECO a jihar Katsina.
An mika tallafin ne ta hannun mataimakin Ministan na musamman, Alhaji Gambo Garba, yayin wata ziyara da tawagarsa ta kai makarantar mata ta WTC da ke Katsina domin ganawa da shugabar makarantar, Hajiya Hadiza Nasir.
A cewar Gambo Garba, Ministan ya amince da bayar da tallafin ne bayan samun roko daga makarantar dangane da halin da wasu daga cikin daliban ke ciki, musamman marasa galihu da marayu da ke fuskantar barazanar rasa damar ci gaba da karatu.
Ya bayyana cewa Injiniya Darma na daga cikin masu bai wa harkar ilimi muhimmanci, yana mai ganin cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma da makomar matasa.
Da take jawabi bayan karbar tallafin, shugabar makarantar ta nuna godiyarta ga Ministan, tana mai cewa duk da ta nemi taimako daga mutane da dama, Injiniya Muttaqha Rabe Darma ne kadai ya amsa koken daliban tare da daukar nauyin kudin jarabawar nasu.
30/04/2026
Ministan Gidaje Ya Jajirce Wajen Sa Ido Kan Ayyukan Karsana da Gidajen Sojoji a Abuja
Ministan Gidaje da Raya Birane na Najeriya Engr. Muttaqha Rabe Darma PhD ya ci gaba da nuna ƙwazo da jajircewa wajen duba manyan ayyukan gidaje a Abuja, inda ya kai ziyara a Karsana Renewed Hope City da kuma Gidajen Sojojin Tarayya.
Ziyarar ta nuna himmarsa wajen tabbatar da inganci, sa ido kan ci gaban ayyuka, da kuma ganin an kammala su cikin lokaci domin amfanin al’umma.
Wannan mataki na nuni da kudurin gwamnatin Tarayya na samar da gidaje masu sauƙin kuɗi, rage gibin matsuguni, da inganta rayuwar ƴan ƙasa.
Team Eng. Muttaƙa Rabe Darma #
27/04/2026
Da Capacityn Ka kaje Jagora.
Duk sai ka gine Najeriya ta koma gidaje.
25/04/2026
Radda Ya Taya Muttaqha Rabe Murna Kan Mukamin Minista
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Dr. Muttaqha Rabe Darma murna kan nadin da aka yi masa a matsayin Ministan Gidaje da Raya Birane.
Radda ya bayyana nadin a matsayin amincewa da kwarewa da jajircewar Darma, yana mai cewa yana da yakinin zai kawo ci gaba a fannin a matakin kasa.
Haka kuma, gwamnan ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zaben kwararru domin bunkasa kasa, tare da jinjinawa tsohon ministan, Ahmed Musa Dangiwa, kan gudummawar da ya bayar.
25/04/2026
Dakta Muttaqa Darma: Sabon Ministan Gidaje da Ci gaban Birane da ke da gogewa a injiniyanci da mulki
Katsina Times
Dakta Muttaqa Rabe Darma na daga cikin sabbin jiga-jigan gwamnati da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa amanar jagorantar Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane, wani muhimmin fanni da ke da alaka kai tsaye da rayuwar al’umma.
Darma ƙwararren masani ne da ya haɗa ilimin kasuwanci da injiniyanci, inda ya samu digiri na uku (PhD) a fannin kasuwanci daga Jami’ar Liverpool, sannan ya ƙara wani digiri na uku a fannin Industrial Engineering daga Amurka. Hakan ya ba shi damar fahimtar yadda ake haɗa fasaha da dabarun gudanarwa wajen warware matsalolin ci gaba.
Ya fara harkar ilimi ne da digiri na farko a Mechanical Engineering daga Jami’ar Bayero Kano (BUK), kafin ya tsunduma cikin aikin gwamnati da koyarwa.
A bangaren aiki, ya rike muƙamin Sakataren Gudanarwa na Asusun Tallafa wa Fasahar Man Fetur (PTDF) tsakanin 2008 zuwa 2012. Haka kuma ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, da kuma Kwamishinan Matasa da Walwalar Jama’a a Jihar Katsina, inda ya taka rawa wajen tsara manufofi da aiwatar da ayyukan raya kasa.
Bugu da ƙari, ya taba koyarwa a Jami’ar Bayero Kano, sannan kafin naɗin nasa a matsayin Minista, ya kasance Shugaban Cibiyar Bunƙasa Ɗan’adam ta Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Masu lura da al’amuran gwamnati na ganin cewa haɗuwar gogewarsa a ilimi, injiniya da mulki na iya taimakawa wajen tunkarar ƙalubalen samar da gidaje masu araha da kuma inganta tsarin birane a faɗin ƙasar nan.