11/05/2018
BYCC FUNTUA ZONAL MEETING TODAY IN FUNTUA.
This is a youth organisation that promotes the good ideologies of our candidate
11/05/2018
BYCC FUNTUA ZONAL MEETING TODAY IN FUNTUA.
07/03/2018
Garkuwa ikon Allah
A madadin shuwagabanni da mambobin kungiyar BYCC reshen jihar katsina suna gayyatar yan uwa da abokan arziki zuwa wajen nadin sabon Garkuwan Katsina Alhaji Abubakar Yahaya Kusada.
Wanda mai martaba Sarkin katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman zai tabbatar masa a fadarsa dake Kofar Soro katsina.
Ranar 31-03-2018 idan Allah yYa kaimu
Allah Ya bada ikon zuwa ameen
Allah Ya yiwa Garkuwa Jagora ameen
By Labaran s kankara
V.C Bycc katsina chapter
On behalf of the entire members of BYCC nation wide, i will use this medium to condole the family of Arc. Nasir Lawan, Bycc Katsina state and Nig at large.
May Arrahman favour Him, Algaffur forgive him and grant him jannatul firdausi amin.
Alh Adamu Nguru
Bycc Nat. Coordinator.
On behalf of the entire members of BYCC nation wide, i will use this medium to condol the family of Arc. Nasir Lawan, Bycc Katsina state and Nig at large.
May Arrahman favour Him, Algaffur forgive him and grant him jannatul firdausi amin.
Alh Adamu Nguru
Bycc Nat. Coordinator.
03/10/2017
Kungiyar BYCC karkashin jagorancin Speaker Kusada sun kai ziyarar rasuwar Arc Nasir Lawal | Hausa-Katsina Post Maigirma Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Katsina Rt. Hon. Abubakar Yahya Kusada ya jagoranci tawagar kungiyar matasa ma su goyon bayan shugaba Buhari zuwa
02/10/2017
A yau, karkashin jagorancin Rt. Hon. Speaker Abubakar Yahya Kusada mun je ta'aziyar rasuwar abokin gwagwarmayarmu Nasir Lawal Danmowa Jibia, wanda Allah Ya yi wa rasuwa ranar Asabar da ta wuce.
An yi wannan tafiya da wasu daga cikin mambobi na BUHARI YOUTH CONGRESS FOR CHANGE (BYCC)
Muna rokon Allah Ya gafarta ma Nasir.
30/09/2017
We are truly from God and to Him we shall return.
We lost a friend, a colleague a true Activist; Architect Nasir Lawal Danmowa.
He was so gentle and a good listener, he served BYCC-KT as Organising Secretary.
Allah SWT Ya gafarta ma ka Nasir. NASIR LAWAL Danmowa
05/07/2017
Kyakkyawan karshe.
Allah kajikan Danmasanin kano da Rahmar ka tare da iyayen mu damu kanmu intamu tazo
:IMAGINE IF IT WAS BUHARI THAT DIDN'T PROVIDE ENOUGH FUNDS
"NASS reduced the budget of 2nd Niger bridge from 15billion to 10billion naira. Lagos ibadan expressway from 31billion to 10billion naira.
And these people were the same that this project was budgeted at the cost of N140bn just because they got their kicked then.
Note contractors are being owed 10billion naira and are threating to stop work on the roads.
Meanwhile NASS has increased their budget from about 100billion naira to 125billion naira. Budget for Mambilla power project was also reduced.
The monies realised from this cuts have been put into constituency projects by NASS.
So when driving through lagos ibadan expressway and you spend hours in holdup know who caused your problem.
Know who is sabotaging Nigeria when we don't have improved power supply, etc.
NASS members are united, the SE senators did not complain when the budget for 2nd Niger bridge was reduced, the SW senators did not complain when the budget for lagos ibadan expressway was cut, the NE senators did not complain when the Mambilla power broject was cut.
Yet ordinary Nigerians want to kill themselves over CRK /IRK curriculum and other ethno/religious issues".
MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA.
Shekaru uku baya, ma fi akasarinmu. hankalinmu a tashe yake, idanuwanmu ba su rufo da nufin yin barci, kullum mun yi fakare muna jiran ko ta kwana, da yawa daga cikinmu sun gamu da wani ibtila'i, ko dai na Boko Haram, ko na masu satar mutane, ko na barayin shanu, ko kuma rugujewar tattalin arziki. Wadannan matsaloli ne da in dai ba su shafe ka kai tsaye ba, to sun shafi wani wanda ka sani, haka muka yi ta zama da tashin hankali har Allah Mabuwayin Sarki Ya kawo mana irin abunnan da Bahaushe kance 'jirgin Annabi Nuhu'.
Zuwan shugabancin Muhammadu Buhari ya zame mana wani sanadi na fitonmu daga doguwar ninkayar da ta yi nufin karar da mu, wadda aka cusa mu da karfin tsiya, tsaro ya fara samuwa, nutsuwa da kwanciyar hankali s**a fara tabbatuwa, tattalin arziki ya fara murmurewa daga farmakin da kurayen kasa s**a kai masa, muka fara koyon yin da'a da yin daidai ko ba a tirsasa mu ba, akidar mutanen dauri ta fara dawowa jikinmu. Al'amura s**a fara saituwa a kasa, a kullum ana kara samun cin galabar danniya da wawurar baitilmani, almubazarancin da barayin dukiyar kasa suke yi ya fara bankwana. A yanzu ne za ka shiga masallaci ka yi sallah ba wata fargaba, mabiya addinin kirista su shiga coci ba wata damuwa, kai hatta wanda ba shi da addini ya amince kasar ga ta k**a hanyar gyara.
Abin mamaki, a sanina, idan amarya ba ta hau doki ba, ai kuwa ba za a dora mata kaya ba. Duk da dumbin alfanu da ake samu, wasu da ba su kishin kansu sun dauki kahon zuka sun caka wa BUHARI, sun mayar da shi ba ya da wani kokari, kuskure kadan za a samu su ci gaba da yadawa su kuzuzuta, amma kuma sai su yi biris da nasarar da BUHARI ya samu komin girmanta. ba za su yaba ba, k**ar malam ya ci shirwa za ka ji su, don munafinci.
Abun yana bani takaici idan na ga talakan da ke a karkara ya zauna yana zagin shugaba Buhari, wani abu wai bakin kaza, ya zauna ya yi ta kakaba masa MUTUWA, sai ka ce shi mai fadin ba zai mutu ba, mun dade da amincewa idan wa'adin mutum ya yi ba a jira, idan kuma bai yi ba, sai dai a yi kushe da hassada, amma BUHARI yana nan daram, a tunanina zuwa yanzu ya k**ata ma su irin wannan dabi'ar su gane abun a hannun Allah yake.
Za ka sha mamaki, idan ka ga ma fi yawan masu irin wannan mummunar fata ba su da wata riba ko da mutuwa shugaba ya yi, watakila sai ta zakin munafinci da jam'iyanci. Inda za ku gane karya suke munafukai ne, ba ranar da za su yi yabo, ko su ba da shawara, sai dai s**a da bambadanci. Wani abu kuma, ma fi yawan ma su surutun su ma ba mutanen kirki ba ne ko a gidajensu, abin nan ne na kyamar Karen da ke a gindin dinya. Ba sa kyautata wa kowa bare inganta rayuwar wani, amma a haka suke cin zarafin Buhari.
Wani abu da na lura da shi mafi yawan ma su yin mummunar fata ga Buhari, ba su ma san dalilin da ya sa suke zagin sa ba, kawai sun biye wa jam'iyanci da son zuciya.
A lokuta da dama, saniya ba ta sanin amfanin jelarta, sai bayan babu ita. Irin kokarin da dattijon nan yake yi, na gina sahihiyar kasa mai 'yanci da yalwa, ba lallai ba ne mu gane ta a yau, kila sai bayan ba shi, mu yi da na sani a lokacin da bai da amfani.
Fatanmu a kullum Allah Ya zaba mana abin da yake ma fi alheri ne a rayuwarmu, duk mai muguwar fata ga Shugaba Buhari da mu kanmu muna rokon ALLAH Ya mayarwa mashekiya da kaikayinta.
Ba za mu gajiya ba muna addu'a Allah duk wanda yake munafuntar Musulmi da Arewa Ya Allah Ka kakkarya shi.
ALLAH YA RABA MU DA RANAR YABO
Ahmad A Bawa
Faskari.
Katsina State Coordinator
BUHARI YOUTH CONGRESS FOR CHANGE (B.Y.C.C)
DAGA MAJALISSAR DOKOKIN JAHAR KATSINA...
√√√Dokar kula da hukumar alhazai....
Majalissar dokoki ta jiha zata duba tare da gyaran dokar data kafa hukumar kula da alhazzai ta jiha domin inganta ayyukan hukumar. Wannan yana daga cikin wasu shawarwari 21 da kwamitin kula da harkokin addinin musulunci ya bayar.
Wasu daga cikin shawarwarin sun hada da:
*duba yiyuwar kafa hukumar hukunta masu laifi da s**a shafi aikin hajji k**ar yadda akayi a jihar Kano
*tsaurara matakan tantance alhazai musamman mata domin hana masu ciki zuwa aikin hajji
*hana dukkan wanda baya da ilimin addini ya zama jagoran alhazai daga kananan hukumomi
√√√Habbaka hanyar samar da kudaden shiga ta jiha....
Majalissar zartaswa ta gabatar da wani kuduri gaban majalissa domin neman shawarar majalissar ta yadda za'a inganta hanyoyin samar ma jiha kudaden shiga. Shugaban majalissar Alh. Abubakar Yahya Kusada ya sanar da nadin kwamitin da zaya binciko hanyoyin da s**a k**ata domin nemo shawarwari k**ar yadda gwamnati ta nema. Wannan kwamitin nada membobi guda 5 wadanda s**a hada da yan majalissu masu wakiltar Charanchi, Matazu, Baure, Malumfashi sai kuma wanda zaya jagoranci kwamitin wato Hon. Hambali Faruk daga Katsina. Shugaban majalissar ya umurci membobin kwamitin su tuntubi masu ruwa da tsaki da masana tattalin arziki tate da kwishinan kudi na jiha, babban accountant, da shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jiha don neman shawarwarinsu.
√√√Samin mak**ar aiki.........
An gabatar da wani taro na kwanaki 2 don inganta jwazo da sanin mak**ar aiki ga yan majalissu na jihar nan a filin shakatawa na Yankari dake jihar Bauchi wanda wata chibiya tare da hadin gwiwar jihar Katsina s**a gabatar.
Manufar wannan taro shine domin zaburar da yan majalissun domin su samu zarafin yin wakilci na gari ga wadanda suke wakilta musamman mutanen karkara. Abubuwan da aka tattauna a wajen taron sun hada da:
*hanyoyin samar da sahihan dokoki wadanda zasu amfami al'umma
*matsalolin da s**a shafi kasafin kudi
*lura da yadda ake kashe kudaden gwamnati.
Shugaban majalissar Alh. Abubakar Yahya Kusada yace kofar majalissa a bude take domin karbar shawarwari ta yadda al'umma zasu amfana da romon damakaradiyya.
BUHARI YOUTH CONGRESS FOR CHANGE (B.Y.C.C)
KATSINA STATE CHAPTER.
Assalamu Alaikum
A daidai irin wannan lokaci da muke tunawa tare da farin cikin nasarar da muka samu ta cin zaben Shugaba Muhammadu Buhari. Ya kyautu mu kara taya juna murna da karfafa guiwa wajen ci gaba da jajircewa wajen nema da tabbatar da ingattaccen canji a cikin kasarmu Nijeriya.
Hakika kusan daga 2012-2015 matasan Nijeriya masu fafutukar neman canji mun sadaukar da lokutanmu da duk wani hali da muke da iko da shi don fafutukar tallata kyawawan manufofin JANAR BUHARI, wannan ya taimaka gaya wajen dasa so da Kauna da goyon bayan JANAR a cikin fadin Najeriya har ma da kasashen ketare, sak**akon mayar da zantukansa lazimi akan harsunanmu da yadda alkalumanmu suke kwana da yini zaba kalaman janar, ba ma k**ar a dandulan sada zumunta 'SOCIAL MEDIA' da muka mayar gidajenmu na biyu, nan muke kwana nan muke wuni har Allah Ta'ala Ya kaddara samun nasararmu a filin dagar da bamu dauki mak**ai ba.
A yau da muke murna da farin cikin nasarar da muka samu tun shekara biyu da s**a wuce, yana da kyau mu fahimci cewa yanzu aiki yake, ba a yi komai ba wai an raka bako ya dawo, a yanzu ne JANAR BUHARI ke bukatarmu fiye da lokutan baya.
A yanzu za mu taya shi addu'a da wayar da kan 'yan kasa a fahimta da su halin da ake ciki. domin kada mu bata rawarmu da watsal-watsal, mu yi bitar batun nan na bambancin hakuri da rashinsa kadan ne, mu kara hakuri kadan sai mu ci moriya da yawa.
Dukkaninmu muna sane da kyawawan kudurorin JANAR, amma rashin hakurinmu yana neman ya sa mu aibata tare da rusa duk gwagwarmayar da mu ka yi a baya, muna manta cewa kasar sai da aka gama lalata ta an nakasa ta ta ko'ina, sannan Allah Ya kawo BABA BUHARI. Masana suna cewa ba don saukin da Allah Ta'ala ya kawo mana ba da yanzu Allah kadai ya san mummunan halin da muke a ciki.
B.Y.C.C na kira ga dukkan al'umma da mu kara hakuri mu ci gaba da taya shuwagabanninmu a kowane mataki addu'ar samun nasara domin mu talakawa mu huta mu ji dadi a cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Na gode
Ahmad A Bawa Faskari
Katsina state Coordinator
BUHARI YOUTH CONGRESS FOR CHANGE (B.Y.C.C)