DAURA Zone SENATE
Shin Ina muka dosa meee??.?
Daura zone post
Wannan page zai rika kawo muku muhimman labarai da suke faruwa a daura zone baki daya
01/07/2022
Gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari ya kaddamar da bayar da tallafin gyara da daga darajar makarantu Sakandire 576 a fadin jihar.
Tallafin dai ya fito ne daga babban bankin duniya ta hanyar wani shiri na habaka ilimin ya'ya mata watau Adolescent Girls Initiative For Learning And Empowerment, AGILE, a turance.
A karkashin shirin, dukkan makarantun za su karbi tallafin kudi ne da jumillar su ta kai sama da Naira biliyan daya domin su inganta harkar koyo da koyarwar su.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Masari ya jawo hankalin al'umma da Sarakunan gargajiya da su tabbatar sun shiga tsarin tare da sa ido wajen ganin an yi abunda ya dace da kudin a makarantun da ke kusa da su.
Tun da farko dai Kwamishinan ilimi a na shi jawabin ya yabawa Gwamna Masari kan irin kokarin da yake yi a fannin ilimi wanda ya bayyana cewa tuni kwalliya ta soma biyan kudin sabulu.
Shi ma a jawabin sa Shugaban shirin na AGILE, Malam Mustapha Shehu ya dauki dogon lokaci yana bayyana yadda shirin ya samo asali da kuma yadda yake yanzu da ma shire-shiren su na ganin shirin ya samu nasara.
Daga karshe Mustapha Shehu ya yabawa Gwamna Masari kan yadda ya ba shirin dukkan goyon bayan da s**a bukata ta bangaren kudi da sauran abubuwan da s**a saukaka masu yin aikin.
Wakilan al'umma, na makarantun da abun ya shafa, jami'an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki duk sun tofa albarkacin bakin su a wurin.
Haka zalika daliban makarantar jeka-ka-dawo ta Kofar Yandaka din sun karrama Gwamna Masari a wurin taron da lambar girmamawa.
YANZU-YANZU: Wata Babbar Kotu A Jihar Kano Ta Dakatar Da Gwamna Ganduje Daga Ciwo Bashin Naira Biliyan 10 Domin Sayo CCTV Camera
Masu karatu me za ku ce?
Daga Muhammad Kwairi Waziri
13/06/2022
BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM
Da kun ji Northern Super Senator Ahmad Babba Kaita ya yi tari a fadin jahar Katsina to alkhairi ne.
Shi yasa mu ma da kun ji mun yi magana to alkhairin shi za mu fadi a jahar Katsina.
Shi ya sa cikin shirinmu na
"KATSINA RESCUE MISSION FOR ABK" PROJECT2023", Insha Allah nan ba da jimawa ba zan fara kaddamar da gudun muwata ta bilbord a kana nan hukumomin Daura, Sandamu, Mai'adua, Bindawa, Kankia, Kusada, Ingawa, Mashi, Dutsi, Zango, Mani da Baure.
Domin duk lokacin da ka temaki mutumin kirki to al'umma ka temaka bashi ba, haka zalika duk lokacin da ka kashe mutumin kirki to al'umma ka kashe.
Alhmdullahi ala kulli halin..
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Muna gadiya ga Allah da yabamu dama ta bude wannan page Wanda zai din kawo muku muhimman labarai da ke faruwa ko da s**a faru
Mungode
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina
6089
