05/05/2026
Daga Adamu Media.
A yau, Najeriya na tunawa da cikar shekaru 16 da rasuwar tsohon Shugaban Kasa, , wanda ya rasu a ranar 5 ga Mayu, 2010 bayan fama da jinya.
Marigayi Yar’Adua, wanda aka haifa a ranar 16 ga Agusta, 1951 a , ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da s**a yi fice wajen nuna gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen tabbatar da adalci a mulki.
Kafin hawansa kujerar shugabancin kasa a shekarar 2007, Yar’Adua ya rike mukamin gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2007, inda ya gudanar da mulki cikin tsari da bin doka, abin da ya sa aka dauke shi a matsayin daya daga cikin gwamnoni mafi nagarta a lokacin.
A matsayinsa na Shugaban Kasa, Alh. Umaru Musa Yar'adua ya yi kokari wajen inganta dimokuradiyya tare da daukar matakai na yaki da cin hanci da rashawa. Daya daga cikin abubuwan da s**a ja hankalin al’umma shi ne yadda ya fito fili ya amince cewa zaben da ya kawo shi mulki na da kura-kurai, matakin da ya nuna gaskiyarsa da kaskantar da kai.
Haka kuma, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan samar da zaman lafiya a yankin Niger Delta ta hanyar shirye-shiryen sulhu, wanda ya taimaka wajen rage tashe-tashen hankula a yankin.
Rasuwarsa ta jefa Najeriya cikin jimami, inda aka bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin kasa da mutunta jama’a. Duk da gajeren lokacin da ya yi a mulki, gudummawar da ya bayar na ci gaba da zama abin koyi ga shugabanni na yanzu da masu tasowa.
Yayin da ake cika shekaru 16 da rasuwarsa, al’umma da dama na ci gaba da tuna shi a matsayin shugaba mai gaskiya, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa kasa.
Allah ya jikan, ya ba shi Aljannatul Firdausi.
04/05/2026
DA ƊUMI-ƊUMI:
Peter Obi, Rabi'u Kwankwaso, Aisha Binani da Kabiru Marafa sun zama 'yan Jam'iyyar NDC a hukumance, bayan sun karɓi katin shiga Jam'iyyar a sakatariyar Jam'iyar da ke Abuja, bayan ficewarsu daga ADC.
01/05/2026
Allah Ya yiwa shahararren mawaki Alhaji Surajo Mai Asharalle rasuwa.
Allah Ya gafarta masa.
Za'ayi Jana'izar da da karfe 2:30 a gidansa dake Kofar Kaura Katsina
29/04/2026
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Congratulations Hon. Haruna Maiwada.
25/04/2026
Gwamna Radda da Pantami Sun Hadu a Katsina Gabanin Lakcar Yaye Dalibai.
Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda, ya hadu da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, CON, a daren jiya a birnin Katsina.
Farfesa Pantami ya isa jihar Katsina ne domin gabatar da lakcar taron yaye dalibai (Convocation Lecture) na Cibiyar Fasaha da Gudanarwa ta Jihar Katsina, inda ake sa ran lakcar za ta mayar da hankali kan ilimi, fasaha da ci gaban matasa.
Wannan ganawa ta nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin shugabanci da masana wajen bunkasa ilimi da ci gaban al’umma a jihar.
24/04/2026
Tinubu Ya Rantsar Da Dr. Muttaqha Darma Matsayin Ministan Gidaje
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon Ministan Gidaje da Bunkasa Birane na Tarayya a ranar Juma'a.
Rantsar da Dr. Darma, wanda dan asalin jihar Katsina ne, ya biyo bayan amincewa da takardar nadinsa da Majalisar Dattawa ta yi. Ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa wanda ya yi murabus kwanan nan.
A wani takaitaccen biki da aka gudanar a fadar mulki ta Villa, Shugaba Tinubu ya taya sabon ministan murna, inda ya bayyana cewa ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen neman ci gaba.
Shugaban ya yaba wa Dr. Darma inda ya ce: "Kuna da kwarewa da kyakkyawan tarihin aiki. A matsayinmu na shugabanni, muna bukatar kwararru irinku. Babu shakka kun taka rawar gani a duk inda kuka yi aiki a baya, don haka kun dace da wannan matsayi."
Wane ne Dr. Muttaqha Darma?
Dr. Darma babban masani ne kuma kwararren mai gudanarwa wanda ya yi karatun digiri na uku (PhD) a fannin harkar kasuwanci daga Jami'ar Liverpool, da kuma wani PhD din a fannin "Industrial Engineering" daga Amurka.
Tarihinsa na karatu da aiki ya hada da:
• Digiri na farko a fannin "Mechanical Engineering" daga Jami'ar Bayero ta Kano (BUK).
• Ya taba zama Sakataren Gudanarwa na Asusun Tallafawa Fasahar Man Fetur (PTDF) daga 2008 zuwa 2012.
• Ya rike mukaman Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, da kuma Kwamishinan Matasa da Walwalar Jama'a a Jihar Katsina.
• Ya taba zama malami a Jami'ar Bayero ta Kano.
Kafin wannan nade-nade, Dr. Darma shi ne Shugaban Cibiyar Bunkasa Dan Adam ta Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.
Sabon ministan ya sha alwashin yin amfani da kwarewarsa domin tabbatar da cewa an samar wa 'yan Nijeriya gidaje masu rahusa da kuma inganta biranen kasar kamar yadda tsarin gwamnati mai ci ya tanada.
24/04/2026
Shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya rantsar da sabon ministan Gidaje da raya birane na Najeriya Engr. Muttaka Rabe Darma, a fadar Shugaban kasa dake Abuja da yammacin yau Juma'a 24/4/2026.
23/04/2026
Gwamnan Katsina Ya Sauya Mukaman Mashawarta Biyu Domin Inganta Ayyukan gwamnati
Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sauya mukaman mashawarta na musamman guda biyu domin ƙarfafa aiwatar da manufofi da inganta ayyukan gwamnati.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha, Abdullahi Garba Faskari, ya fitar a ranar 23 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an mayar da Abubakar Ahmed Tsanni daga Sashen Matasa da Wasanni zuwa Sashen Ci gaban Al’umma, yayin da Nasiru Ahmed Mulumfashi ya tashi daga Sashen Raya Karkara da Walwalar Jama’a zuwa Sashen Matasa da Wasanni.
A cewar sanarwar, sauyin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na ƙara ƙwarewa, kirkire-kirkire da inganci a harkokin mulki.
Ta kuma ce gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa mashawartan za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta muhimman manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa a sassan da aka tura su.
Haka kuma, gwamnan ya buƙaci su gudanar da aikinsu da jajircewa, gaskiya da kuma ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu ga gwamnati da al’ummar jihar.
23/04/2026
Yanzu Yanzu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na ganawa da gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
23/04/2026
Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara Ya Roƙi Kada a Mayar da Shi Gidan Yarin Kuje.
Abduljabbar Nasir Kabara ya bayyana cewa babban abin da yake roƙo ga hukumomi shi ne kada a mayar da shi gidan yarin Kuje, yana mai cewa rayuwarsa na cikin haɗari idan aka kai shi can.
Shehin malamin ya ce ko da kuwa kotu za ta yanke masa kowane irin hukunci, bai nuna damuwa da hakan ba, amma abin da ya fi damunsa shi ne batun tsaron lafiyarsa yayin zaman kurkuku.
A cewarsa, yana fargabar cewa zaman sa a gidan yarin Kuje na iya jefa shi cikin barazana, duk da cewa bai fayyace cikakkun dalilan wannan tsoro nasa ba.
Ya kuma roƙi hukumomin da abin ya shafa da su yi la’akari da wannan buƙata domin tabbatar da kare rayuwarsa da tsaron lafiyarsa.Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara Ya Roƙi Kada a Mayar da Shi Gidan Yarin Kuje.
Abduljabbar Nasir Kabara ya bayyana cewa babban abin da yake roƙo ga hukumomi shi ne kada a mayar da shi gidan yarin Kuje, yana mai cewa rayuwarsa na cikin haɗari idan aka kai shi can.
Shehin malamin ya ce ko da kuwa kotu za ta yanke masa kowane irin hukunci, bai nuna damuwa da hakan ba, amma abin da ya fi damunsa shi ne batun tsaron lafiyarsa yayin zaman kurkuku.
A cewarsa, yana fargabar cewa zaman sa a gidan yarin Kuje na iya jefa shi cikin barazana, duk da cewa bai fayyace cikakkun dalilan wannan tsoro nasa ba.
Ya kuma roƙi hukumomin da abin ya shafa da su yi la’akari da wannan buƙata domin tabbatar da kare rayuwarsa da tsaron lafiyarsa.
23/04/2026
Anyi zanga zangar cire shugaban INEC a jahar katsina...kwamred Hamza yunusa jibia na cikin wadanda s**a yi magana a gaban ofishin INEC na kasa dake katsina