16/11/2024
Shawarwari ga duk matashin da ya tunkari shekaru 30 zuwa sama!
Daga: Mubarak Abdullahi Arts
1. Kayi iya yinka wajen gujewa bashi, sai in ya zama dole, kuma da zarar ka samu sukunin biya to kayi hakan da wurwuri. "Bashi ba karamar barazana bace ga cigaba"
2. Idan Allah ya h**e maka aiki ko sana'a, ka dinga aje wani kaso komai ฦarancinsa, a asusun ajiyarka. "Ajiya maganin wata rana"
3. Aฦalla ka samu abin yi fiye da ษaya, "Gida biyu maganin gobara"
4. A kowace safiya kamin rana ta faษi, yi ฦoฦari ka iya wani sabon abu. Wayar da kake riฦewa makaranta ce babba "Ilmi kogi ne"
5. Aฦalla kowane mako ษaya, ka yi ฦoฦarin karanta wani littafi. Akwai darussa da dama ฦunshe acikin littafai. "Ilmi haske"
6. Ka dinga motsa jiki aฦalla sa'a ษaya a rana. " mafi yawan ciwarwata/cututtuka nada alaฦa da rashin motsa jiki.
7. Ahir, kashe dinka da zaman majalisa, amadadin haka yi wani abin da zai amfaneka da wannan lokaci, ko dai koyon wani abu ko neman ilmi. "Zaman kashe wando illa ce babba, kuma hurumi ne na wanzuwar giba da annamimanci" Ba zaka gane muhimmancin lokaci ba sai girma ya sameka.
8. Ka dinga tashi tunda safe domin tunkarar ayukan ka na wannan rana. "Da sassafe ake k**a fara"
9. Kowane yini kamin rana ta faษi, yi ฦoฦari ka taimaki wani, ko da sadaka koda shawara kai koda da baiwa ฦadangaru ruwan sha ne. "Kar ka manta, wata karuwa ta samu gafarar Allah sak**akon yin taimako irin wannan"
10. Tallafi iyayenka da komai ฦanฦantar abin da Allah ya h**e maka, ko da kuwa suna da sukuni. "Akwai Albarka sosai a taimakawa iyaye da yi masu biyayya"
Duka waษannan matakan nasara ne!
29/09/2024
ุงููููููู
ูู ุตูููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุตูููููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏูุ ุงููููููู
ูู ุจูุงุฑููู ุนูููู ู
ูุญูู
ููุฏู ููุนูููู ุขูู ู
ูุญูู
ููุฏูุ ููู
ูุง ุจูุงุฑูููุชู ุนูููู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ู ููุนูููู ุขูู ุฅูุจูุฑูุงูููู
ูุ ุฅูููููู ุญูู
ููุฏู ู
ูุฌููุฏู
๐๐ค๐ค๐ ๐ข๐ค๐ง๐ฃ๐๐ฃ๐ ๐๐ก๐ก ๐ข๐ฎ ๐ฅ๐๐ค๐ฅ๐ก๐
28/09/2024
Muhammad ษan Abdussalam al-Khushani ya ce:
"Ka guji mace, mai tuno mummuna, mai musun alheri, zancenta barazana, muryarta mai kaifi, mai binne kyawawa, mai tono munana, mai taimakon jujjuyawar zamani a kan mijinta, ba ta taimakon mijinta a kan jujjuyawar zamani, babu tausasawarsa a zuciyarta, ba ta gudun komai ya same shi, in ya shigo gida ta fice, in ya fice ta shigo, idan ya yi dariya ta yi kuka, idan ya yi kuka ta yi dariya, in ya sake ta, ta zame masa alaฦaฦai, idan ya ci gaba da riฦe ta, ta ci gaba da yi masa gashin ฦuma.. yaranta a ฦanjame, gidanta bola, in tana magana tana nuna shi da ษanyatsa, mai haushi tun daga bakin zaure, za ta ษarke da kuka, bayan ita ce ba ta da gaskiya..."
..
Ibn Abd Rabbih 7:121
~~ Sheikh Dr. Aminu Ismail
23/09/2024
Temaka Kafin Kawuce Kabamu Sadakar Hoton Addini Guda Daya Acikin Gallery Din Wayarka.
15/09/2024
ASTAGFIRULLAH for my past
ALHAMDULILLAH for my present
INSHALLAH for my future
14/09/2024
A FAHIMCI WANNAN.
Mafiya yawan masu neman mu sadda suke da bukata; to wannan sunan su abokan mu.
Haka kuma da yawan masu neman mu sadda suke tunanin muna da buฦata; to wannan sune ฦดan uwan mu.
09/09/2024
In namiji yayi dacen mace duk talaucin sa sai kaga alamun nitsuwa da kwanciyar hankali a tattare dashi, zakatar yana ษan jin kansa k**ar basarake tabbas gaskiya ne domin matarsa ta dawo dashi sarki a gidan sa.
Ita kuwa mace in tayi dacen miji nagari, banda nitsuwa da kwanciyar hankali da zaka gani a tattare da ita, zaka tarar tana da wani confidence da ke nuna tana da garkuwa da jigo da ya tsaya mata akan komi na rayuwarta, duk magana za ku ji tana yawan ambaton jarumin rayuwarta domin ya maida ita sarauniya a masarautar sa rayuwar sa.
Tabbas wannan matakine da kowa dake cikin mu ke son kasancewa a cikin rayuwar abokin zaman sa, amma kuma ba'a samun wannan matakin cikin sauqi dole sai kowa ya kiyaye hakkokin sa, ya kyautata, ya muhimmantar da abokin zaman sa, ya yi hakuri, juriya, kawaici da neman agaji da taimakon Allah.
Dawo da mijin ki sarki dan samun damar dawowa dake sarauniyar zuciya ko rayuwar sa.
Dawo da matarka sarauniya dan samun damar dawo da kai sarki kuma abun alfaharin rayuwar ta.
~~ Coach Fatimah Chikaire
07/09/2024
KANA CIKIN TSANANI?
To ka lura:
1) Ba kai kadai bane.
2) Akwai hikima cikin duk abin da Allah ya kaddara.
3) Allah ne kadai Mai kawo alheri ya ije sharri, kar ka ta'allaka da waninsa.
4) Duk abin da ya same ka ba zai kuskure maka ba, abin da kuma ya kuskure maka ba zai same ka ba.
5) Sanin ainihin mece ce duniya zai hutar da zuciyarka.
6) Kyautata zato ga Ubangiji.
7) Zabin Allah ya fi zabin wani.
8) Idan masifa ta tsananta to yayewa na kusa.
9) Kada ka rika tunanin hanya daya ce kadai mafita, don in Allah zai yaye masifa yakan bude hanyoyin da baka taba tunaninsu ba.
10) Yi ta rokon Allah.
ALLAH ta'ala ya yaye mana damuwar mu baki daya, amin.
Dr. Aminu Ismail