24/10/2025
Baba ya ce "Juma'a mubarak"
Allah ya karɓa mana.
Abdulaziz Abdulaziz 🖊️
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Reporters TV, Government Official, Daura, Katsina.
24/10/2025
Baba ya ce "Juma'a mubarak"
Allah ya karɓa mana.
Abdulaziz Abdulaziz 🖊️
29/06/2025
AKUME REMAINS SGF
There has been no change in the status of His Excellency, Senator George Akume, as Secretary to the Government of the Federation.
President Bola Ahmed Tinubu, currently in Saint Lucia, has not made any new appointments.
The information circulating about Akume’s replacement is untrue. Agents of mischief fabricated it.
The Presidency advises Nigerians to disregard the fake news.
Bayo Onanuga
Special Adviser to the President
(Information and Strategy)
June 28, 2025
27/06/2025
Benefits for the home and individuals of the Tax Reform Bills, which were signed by our President Bola Ahmed Tinubu.
28/03/2025
AlhamdulilLah, ana ta daɗa rage mugun iri!
Har yanzu akwai sauran rina-a-kaba a yaƙi da mugaye ƴan ta'addan daji amma ko shakka babu ana ganin haske. Daga shigowar gwamnatin Bola Tinubu zuwa yau an yiwa ƴan daji ɓarnar da ba a taɓa yi musu ba. Ya zuwa yanzu an kashe fitattun ɓarayin daji kamar haka:
1. Ali Kachalla/Ƙawaje
2. Kachallah Dogo Kwaddi
3. Lawali Dodo
4. Ɓoderi
5. Sani Wala-birki
6. Kachallah Hana-Zuwa
7. Damina
8. Kachalla Sani Dangote
9. Kachalla Adamu
10. Halilu Sububu
11. Baleri
12. Modi Modi
13. Kachalla Mai Shayi
14. Kachalla Tsoho Lulu
15. Ibrahim Nagure
16. Kachalla Makore
17. Bulak
18. Tukur Sharme
19. Hassan Ɗantawaye
20. Ɗan-Isuhu
Wannan nasara da ake samu ta kawo sauƙi ƙwarai ga al'ummomin dake maƙwabtaka da waɗannan miyagu. Insha Allah za a cigaba da nasara akan mugaye domin ƴantar da mutanen da suke ƙuntatawa a ko-ina-da-ina.
Allah ya cigaba da ɗora nagari akan mugu!
26/02/2025
Na yi farin ciki da saukowar farashin kayan abinci musamman ma yanzu da muke fuskantar azumi. Muna ganin haske da cigaba. Yayin da ƙasashe da yawa ke fama da matsaloli, mu a Najeriya muna ganin sauyi me kyau. A hankali al'amura na daidaita, sauƙi na ƙara samuwa. Mungodewa Allah!
– Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron ƙoli na jam'iyyar APC
15/02/2025
Shugaba Tinubu A Taron AU
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗau hoto tare da sauran Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci a wajen Zama na 38 na Taron Babbar Majalisar Ƙungiyar Haɗa Kan Afrika (AU) a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha a ranar wannan Asabar ɗin.
Hoto na 2: Shugaba Ahmed Tinubu tare da sauran Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci suna halartar Zama na 38 na Taron Babbar Majalisar Ƙungiyar Haɗa Kan Afrika (AU) a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.
13/02/2025
Wallahi Tallahi Na Yi Nadamar Tallata Tinubu A Zaben 2023, Inji Danbilki Kwamanda
Me za ku ce?
FIFTEEN years ago, the matter was raised and addressed. 👇🏽
05/02/2025
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kashe Naira biliyan 80 don sake ginawa da gyara madatsar ruwa ta Alau dake jihar Borno a wani bangare na kokarin shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da inganta harkokin ruwa a yankin.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja, wanda shugaba Tinubu ya jagoranta.
Utsev ya bayyana cewa gwamnatin jihar Borno za ta hada hannu da gwamnatin tarayya domin gudanar da aikin wanda aka shirya kammala shi cikin watanni 24.
Ya kuma jaddada cewa za a kammala kashi na farko na aikin gyaran tsakanin watan Fabrairu zuwa Yuli na shekarar 2025 domin dakile matsalar ambaliyar ruwa a jihar.
02/02/2025
Nasarorin da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cimma a cikin watan January.
.
*Tsarabar Mako daga fadar shugaban ƙasa* mai ɗauke da ayyukan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar a cikin makon da ya gabata.
Sako daga ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai Abdulaziz Abdulaziz
31/01/2025
Yadda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Yayi Sallar Juma'a tare da Khalifan Tijjaniyya na Duniya, Sheikh Ibrahim Inyass, Shekh Mahi Inyass a Masallacin Fadar Shugaban Kasa.
Khalifan ya yi wa Najeriya addu'ar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, Kana ya yi wa Shugaban kasar fatan samin nasarar aiyukan da ya ke yi na sake raya kasa.