Katsina State Hisbah Board Command Headquarters

Katsina State Hisbah Board Command Headquarters

Share

Fadakarwa, hani ga yin mummuna da horo da yin kyakkyawan aiki.

Photos from Katsina State Hisbah Board Command Headquarters's post 23/04/2026
22/04/2026
Photos from Katsina State Hisbah Board Command Headquarters's post 26/03/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN,

A CIKIN JIMAMI DA MAIDA AL'AMURRA GA ALLAH MU KE SANAR DA AL'UMMA RASUWAR ƊAN UWA, MALAM SHEHU LADAN ARMY Army Shehu Ladan.

MAL. SHEHU LADAN ARMY ƊAN HISBAH NE, KUMA MALAMI A HASSAN USMAN KATSINA POLYTECHNIC. YA BADA GUMUMMUWA MAI YAWA A AL'AMURRAN ADDINI. BA MU SAN KOMI GAME DA SHI BA SAI ALHERI.

ZAA YI JANAZA YAU, ƘARFE 2:30, A MALUMFASHI.

ALLAH YA GAFARTA MASA, YA KYAUTATA BAYANSA, YA BA MU HAƘURIN JURE WANNAN BABBAN RASHI.

02/11/2024

Kanan mu da gwabnatin tarayya tayi kinnafin tace kudin fansa million 10

05/07/2024

Alhamdu lillah. Lahadi 7/7/2024 ita ce 1 ga watan Muharram 1446 AH in Allah Ya Kai mu. Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan sabuwar shekarar Ka tsare mu daga sharrukan da ke cikinta.

13/06/2024

*AZUMI RANAR ASABAR*
Yin Azumi Ranar Asabar yanada halaye guda biyar (5).
1- ya kasan ce na farilla ne. Kamar Ramadan, ko ramashi, Azumin Kaffara, Azumin chanji hadayar Tanatu'i, da makamantan haka
Wannan ya halartar.
2- Hada Asabar da jumu'a ko lahadi. Wannan ma ya halasta.
Annabi SAW ya shiga wajan daya daga cikin matan sa (Juwairiyya bintu Haris) ya sameta tana Azumi Ranar jumu'a sai yace mata :( kinyi jiya tace a'a, yace zakiyi gobe tace a'a yace kici Abincin ki).
Wannan ya nuna Idon mutun yayi Azumi jumu'a ko zanyi lahadi ya halasta yayi Asabar.
3- Asabar ta fado kwanakan da aka shar'anta azumtar su, Kamar ta fado kwanakan farin wata (Ayyamul bidhi 13,14,15 ga kowa ne watan musulunci), ko ta fado Ranar Ashura, ko Ranar Arafah, ko makamantan su.
Yin Azumi irin haka ya halasta, saboda ana azumtar ranakun ne ba Asabar ba.
4- Ta fado Ranar da mutun ke Azumi.
Kamar mutumen da ke Azumi irin na Annabi Dauda wato yayi Azumi yau ya sha ruwa gobe.
Shima wannan ya halas ta.
5- Mutun ya ware Asabar da yin Azumi ita kadai.
Wannan ne Annabi SAW ya Hana a cikin hadisin yusurah bintu Alsalmiyya Kamar yanda Iman Tirmizi ya ruwaito. in hadisin ya inganta.

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Katsina