05/06/2026
Friday Message from the Executive Chairman of Kurfi Local Government
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.
On this blessed Friday, I extend my warm greetings to the good people of Kurfi Local Government. As we gather for Jumu'ah prayers, let us continue to pray for peace, unity, progress, and prosperity in our communities.
May Allah (SWT) bless our families, strengthen our bonds of brotherhood, and guide us toward all that is good. Let us remain law-abiding, support one another, and work together for the continued development of Kurfi Local Government.
I appreciate your trust, support, and cooperation. Together, we will continue to build a brighter future for our people.
May Allah accept our prayers and grant us abundant blessings, good health, and success in this life and the Hereafter.
Jumu'ah Mubarak.
Malam Babangida Abdullahi Kurfi
Executive Chairman, Kurfi Local Government Area.
04/06/2026
We will never forget the tremendous contributions you have made to the people of Kurfi Local Government. May Almighty Allah reward you abundantly, grant you good health, wisdom, and continued success in all your endeavors.
The Executive Chairman of Kurfi Local Government, Malam Babangida Abdullahi Kurfi. 🙏🏾🤲🏾
03/06/2026
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kurfi, Malam Babangida Abdullahi Kurfi, ya ƙaddamar da mambobin kwamitin Renewed Hope Agenda a matakin ƙaramar hukuma.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar a Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Kurfi, inda shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana muhimmancin kwamitin wajen tallafa wa manufofin Renewed Hope Agenda da kuma ci gaban al'umma.
Mambobin kwamitin da aka ƙaddamar sun haɗa da:
Ahmed Surajo
Sanusi Ado Kurfi
Badiya Bature
Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu cikin gaskiya da riƙon amana.
Amin🤲.
28/05/2026
KYAUTAR RIYAL HAMSIN GA KOWANE ALHAJI DA HAJIYA NA AIKIN HAJJIN BANA DAGA SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KURFI.
Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Kurfi, Malam Babangida Abdullahi Kurfi ya baiwa alhazan bana na faɗin ƙaramar hukumar Kurfi kyautar Riyal 50 ga kowane alhaji da alhajiya domin tallafa musu yayin gudanar da ibadar aikin hajji.
Wannan karamci na nuna ƙauna da kulawar shugaban ga al’umma tare da fatan Allah Ya karɓi ibadun alhazanmu baki ɗaya.
Allah Ya dawo dasu gida lafiya.
Amin 🤲.
27/05/2026
SAƘON BARKA DA SALLAH DAGA SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KURFI
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
Ina mai matuƙar farin ciki da miƙa saƙon taya murna ga ɗaukacin al'ummar Ƙaramar Hukumar Kurfi da ma al'ummar Musulmi na duniya baki ɗaya bisa wannan babbar rana ta Sallah mai albarka.
Wannan lokaci ne na godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa ni'imomin da Ya yi mana, tare da tuna muhimmancin biyayya, haƙuri, sadaukarwa da kuma taimakon juna. Ina kira ga al'ummarmu da su ci gaba da rungumar zaman lafiya, haɗin kai, mutunta juna da kuma nuna ƙauna ga maƙwabta domin ci gaban ƙaramar hukumar mu da ƙasa baki ɗaya.
A madadina, iyalina da kuma gwamnatin Ƙaramar Hukumar Kurfi, ina addu'ar Allah Ya karɓi ibadunmu da sadaukarwarmu, Ya yafe mana kura-kuranmu, Ya albarkaci gidajenmu, Ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa, lafiya da ci gaba mai albarka.
Ina kuma gode wa al'ummar Kurfi bisa irin goyon baya, haɗin kai da addu'o'in da suke ci gaba da ba mu. Da yardar Allah za mu ci gaba da aiki tukuru domin kawo ayyukan alheri da ci gaba ga dukkan sassan ƙaramar hukumar mu.
Allah Ya sa mu yi Sallah lafiya, Ya maimaita mana irin wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki.
EID MUBARAK!
Malam Babangida Abdullahi Kurfi
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kurfi
Cut-see: Bash Kurfi
SSA Media to the Executive Chairman, Kurfi Local Government.
25/05/2026
SAƘON RANAR LITININ (MONDAY MESSAGE) DAGA SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KURFI, MALAM BABANGIDA ABDULLAHI KURFI
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Ina miƙa gaisuwa ta musamman ga ɗaukacin al'ummar Ƙaramar Hukumar Kurfi. Muna gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba mu damar shiga sabon mako cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Ina kira gare ku da mu ci gaba da kasancewa masu haɗin kai, zaman lafiya da biyayya ga doka domin ci gaban ƙaramar hukumar mu. Gwamnatin mu za ta ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinta wajen samar da ayyukan alheri da inganta rayuwar al'umma a fannoni daban-daban.
Ina roƙon Allah Ya sanya albarka a cikin wannan sabon mako, Ya ba mu nasara a cikin ayyukanmu na yau da kullum, Ya kare mu daga dukkan sharri, Ya kuma ci gaba da ɗora Ƙaramar Hukumar Kurfi a kan turbar ci gaba da wadata.
Allah Ya albarkaci Ƙaramar Hukumar Kurfi, Allah Ya albarkaci Jihar Katsina, Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya.
Babangida Abdullahi Kurfi
Executive Chairman, Kurfi Local Government.
23/05/2026
Kurfi A Ward Ta Gudanar da Zaɓen Fidda Gwani Ta Hanyar Consensus
A yau, Kurfi A Ward ta gudanar da zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ta hanyar consensus, inda aka amince da goyon bayan mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya samu nasarar lashe zaɓen.
Mai girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kurfi, Malam Babangida Abdullahi Kurfi, ya halarci wannan muhimmin taro tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a matakin Kurfi A Ward.
Taron ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali, inda mahalarta s**a nuna cikakken goyon baya da haɗin kai ga jam'iyyar da kuma shugabanninta. An kuma yi addu'o'in neman nasara da ci gaban ƙasa tare da fatan alkhairi ga jam'iyyar APC a zaɓuɓɓukan da ke tafe.
SSA MEDIA AND PUBLICITY TO THE EXECUTIVE CHAIRMAN OF KURFI LGA.
22/05/2026
JUMMA'A MUBARAK
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
On behalf of the Executive Chairman of Kurfi Local Government Area, Hon. Malam Babangida Abdullahi Kurfi, I extend my warmest Jumma'a greetings to the good people of Kurfi LGA and beyond.
As we gather for this blessed Friday prayer, I pray that Allah (SWT) accepts our acts of worship, forgives our shortcomings, and showers His mercy, peace, and blessings upon our families and communities.
May this sacred day bring unity, progress, good health, and prosperity to all our people. Let us continue to support one another and work together for the development and advancement of Kurfi Local Government.
May Allah (SWT) grant us a peaceful and rewarding Jumma'a and bless our dear Kurfi with continued peace and progress.
Jumma'a Mubarak.
Hon. Babangida Abdullahi Kurfi
Executive Chairman, Kurfi Local Government Area.
19/05/2026
During an inspection of the ongoing project at SAMA'ILA MAMMAN PRIMARY SCHOOL, KURFI, by the leadership of Babangida Abdullahi Kurfi, led by the Supervisory Councillor of Works and Housing Department, Yusuf Shehu Wurma.
The inspection was carried out to assess the level of work completed and ensure the project meets the expected standard for the benefit of the people of Kurfi.
19-05-2026.