Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu, Political organisation, matazu, Katsina.

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 20/05/2026

Gwamna Radda Yayi Kira Ga ’Yan Takarar APC Da Su Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, yayi kira ga dukkan ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai a kujeru daban-daban da su fara Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027

Gwamnan yayi wannan kiran ne yayin da yake karɓar wata babbar tawaga daga iyalan fitaccen ɗan kasuwa kuma mai ayyukan alheri, Alh Dahiru Barau Mangal, ƙarƙashin jagorancin dan takarar majalisa mai wakiltar mazabar Katsina, Barrista Abba Dahiru Mangal, a ziyarar godiya da s**a kai masa.

Gwamna Radda ya buƙaci ’yan takarar da su kusanci al’umma tare da neman addu’o’i da goyon baya daga masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma da malaman addini a faɗin jihar.

Haka kuma, ya yabawa ’yan takarar da s**a janye wa Barrista Abba Mangal a takarar kujerar Majalisar Wakilai, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar haɗin kai da balagar siyasa a cikin jam’iyyar APC.

A nasa jawabin, Barrista Abba Mangal ya yabawa salon shugabanci na Gwamna Radda, yana mai cewa nagartaccen shugabancinsa ne ya tabbatar da gudanar da zaɓukan fidda gwani cikin nasara da lumana a faɗin jihar.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa idan aka zaɓe shi zuwa Majalisar Tarayya, zai bayar da wakilci nagari tare da kare muradun al’ummarsa yadda ya kamata.

✍️ Secretary APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU

May 20, 2026.

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 20/05/2026

.
An gudanar da taron tabbatar da takarar Hon. Kabir Faruk domin tsayawa takarar kujerar ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar Hukumar Matazu a zaɓen shekarar 2027 cikin nasara da walwala.
A yayin gudanar da taron, Hon. Kabir Faruk ya samu jimillar ƙuri’u 87, wanda hakan ya tabbatar da shi a matsayin wanda zai wakilci jam’iyya a wannan takara ta 2027. Taron ya gudana cikin tsari da lumana tare da halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban.
Daga cikin waɗanda s**a halarci taron akwai shugaban jam’iyya na Jaha, Dr. Gambo Saulawa, tare da sauran manyan jiga-jigan jam’iyya, stakeholders, matasa, dattawa da kuma magoya baya daga wurare daban-daban na ƙaramar Hukumar Matazu da ma wajenta.
A jawabin sa bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takara, Hon. Kabir Faruk ya nuna godiya matuƙa ga Allah da kuma dukkanin wakilan da s**a ba shi goyon baya da amincewa. Ya kuma yi alƙawarin yin adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba, tare da tabbatar da cewa zai yi aiki domin cigaban al’umma baki ɗaya idan Allah Ya ba shi nasara.
Haka kuma, an yi addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, haɗin kai da cigaban ƙaramar Hukumar Matazu da Jihar Katsina baki ɗaya. Mahalarta taron sun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya tabbatar da alheri, Ya zaunar da al’umma lafiya, Ya kuma ba da nasara ga shugabanni masu kishin jama’a.
✍️ Secretary Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 19/05/2026

GAYYATAR TARO
APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU na farin cikin gayyatar al’ummar Karamar Hukumar Matazu zuwa taron tabbatar da takarar Hon. Kabir Faruk a matsayin Ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina karkashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
📅 Rana: Laraba 20/05/2026
⏰ Lokaci: Karfe 9:00 na safe
📍 Wuri: Sakatariyar Karamar Hukumar Matazu
Muna kira ga dukkan magoya baya da masu fatan alheri da su halarci wannan muhimmin taro domin nuna goyon baya da haɗin kai.
Daukar Nauyi:
APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 11/05/2026



Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji’un.

Ina ƙara jajanta mana tare da miƙa ta’aziyya ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Matazu baki ɗaya, musamman iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu sakamakon harin da ya afku a ƙauyukan Salihawar Maruji, Dugul da Hayin Nomau.

Ina ƙara kira gare mu da mu ƙara dagewa da addu’a, domin babu abin da ya fi ƙarfin Allah.

Shugabannin da suke ƙoƙari wajen samar da tsaro, Allah Ya taimake su. Jami’an tsaronmu da suke sadaukar da rayukansu domin ganin an samu zaman lafiya, Allah Ka ba su kariya, Ka taimake su a kan hakan.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsu, Ya bai wa iyalansu da daukacin al’umma haƙurin jure wannan babban rashi. Allah Ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a karamar hukumar Matazu, Jihar Katsina, da ƙasarmu baki ɗaya. Amin.

اللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ،
وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرُورِهِمْ.

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 04/05/2026


MAI NEMAN TAKARAR DAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA, MAI WAKILTAR MATAZU LGA
A KARKASHIN JAM'IYYAR APC
A ranar da aka tanada domin miƙa takardun neman takara ga Jam’iyyar APC a matakin jiha, Hon. Kabir Faruk, ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Matazu, ya kai ziyara ta musamman zuwa ofishin jam’iyyar APC na jiha domin miƙa takardar sa ta Nomination Form cikin nasara da cike da farin ciki.
Wannan gagarumin taro ya samu halartar dimbin magoya baya, shugabanni, da al’ummar gari daga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Matazu, lamarin da ya nuna cikakken goyon baya da amincewa da takarar Hon. Kabir Faruk. Hakika, taron ya zama abin tarihi, domin an shaida cewa babu wani ɗan takarar majalisar jiha da ya taɓa samun irin wannan taro mai cike da jama’a da goyon baya wajen miƙa takardarsa kamar yadda aka gani a wannan rana.
A jawabin sa bayan kammala miƙa takardun, Hon. Kabir Faruk ya bayyana matuƙar farin cikin sa da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da kuma irin karɓuwa da goyon bayan da al’umma s**a nuna masa. Ya jaddada cewa wannan ƙwarin gwiwa da jama’a s**a nuna masa zai ƙara masa himma wajen ganin ya wakilci al’ummar Matazu cikin gaskiya, riƙon amana da kishin cigaban yankin.
Haka kuma, ya miƙa godiya ta musamman ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu, Hon. Shamsuddeen Muhammad Sayaya, bisa jagoranci nagari da goyon bayan da ya bayar, tare da gode wa kansiloli da dukkanin abokan aikin sa bisa haɗin kai da s**a nuna. Bugu da ƙari, ya nuna godiya ga dukkanin stakeholders na Matazu, shuwagabannin Jam’iyyar APC a matakai daban-daban, ƴan’uwa da abokan arziki wajen gudunmawar da s**a bayar wajen ganin wannan rana ta kasance mai cike da nasara.
Hon. Kabir Faruk ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Matazu da su ci gaba da ba shi goyon baya tare da yi masa addu’a domin samun nasara a wannan tafiya.
✍️ Bilyaminu Idris Secretary Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 04/05/2026


Muna farin cikin sanar da al’umma cewa an gudanar da raka Hon. Kabir Faruk zuwa ofishin shugaban Jam’iyyar APC, inda ya miƙa takardar fom ɗin sa na neman tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Katsina, domin wakiltar al’ummar Matazu.
Wannan gagarumin mataki ya samu halartar dimbin magoya baya da al’ummar gari, wanda hakan ya nuna cikakken goyon baya da ƙauna da jama’a ke nuna masa.
Muna miƙa godiya ta musamman ga:
Shugaban jam’iyya (Chairman)
Counciloli
Iyayen jam’iyya
Stakeholders
Jami’an gwamnati
Mutanen gari
Ƴan’uwa da abokan arziki
Saboda irin gudummawa, goyon baya da kuma jajircewar da s**a nuna wajen ganin an kai wannan matsayi cikin nasara.
A ƙarshe, muna roƙon addu’o’in al’umma da fatan alkhairi, Allah (SWT) Ya ba Hon. Kabir Faruk nasara a zaɓe mai zuwa, Ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da al’umma za su ɗora masa.
Allah Ya sa mu dace, Ya ba mu nasara.
✍️ SECRETARY APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 01/05/2026


Bismillahir Rahmanir Rahim.
Hakika mulki da iko duka na Allah ne, yana ba wanda Ya so, kuma Yana karɓa daga wanda Ya so. A wannan tafiya ta neman kujera a Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Matazu LGA, mun shaida yadda talakawa s**a ɗaga hannayensu zuwa ga Allah, suna roƙon zabin alkhairi, shugaba nagari, mai tausayi, mai tsoron Allah, wanda zai ɗauki nauyin jama’a da gaskiya da amana.
Mun yi imani da cewa wannan addu’a ta talakawa ba ta tafi a banza ba. Domin kuwa Allah cikin ikonSa da hikimarSa, Ya zaɓi Hon. Kabir Faruk ya zama wanda zai jagoranci wannan amanar ta neman kujerar Malisar jaha. Wannan ba kawai nasara ba ce ta mutum ɗaya ba, nasara ce ta al’umma, nasara ce ta addu’a, nasara ce ta gaskiya da fatan alkhairi.
Ya Allah, muna roƙonKa: Ka sanya wannan nasara ta zama alkhairi ga al’ummar Matazu baki ɗaya. Ka ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa. Ka tsare shi daga son zuciya da zalunci. Ka ba shi hikima, adalci da jajircewa wajen yi wa jama’a aiki. Ka sanya shi cikin bayinKa nagari masu tsoronKa a fili da ɓoye.
Ya Allah, Ka haɗa zukatan mu, Ka sanya wannan shugabanci idan an same shi ya zama sanadin cigaba, zaman lafiya da haɗin kai. Ka ba shi lafiya, natsuwa, da ƙwarin gwiwar cika alkawuran da ya ɗauka.
Muna kira ga mutane muzo mu rungumi zaɓin Allah hannu bibbiyu domin hakan shine zai tabbatar mana da nasara
Mu a madadin APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU, muna miƙa cikakken goyon bayanmu ga Hon. Kabir Faruk. Muna tabbatar masa da cewa matasa suna tare da shi domin ganin ya yi nasara a wannan tafiya. Za mu tsaya tsayin daka wajen tallafa masa da addu’a, shawarwari da kuma aiki tukuru domin cigaban yankinmu.
Wannan dama ce ta gina al’umma, dama ce ta nuna nagarta, dama ce ta kawo sauyi mai ma’ana.
Allah Ya taimake mu baki ɗaya.
Allah Ya albarkaci Matazu.
Allah Ya albarkaci Jihar Katsina.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullah.
✍️SECRETARY APC YOUTH POLITICAL AWARENESS FORUM MATAZU

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 27/04/2026


Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu,
Mu, a madadin APC Youth Political Awareness Forum Matazu, muna miƙa wannan saƙo na jan hankali gare ku, masu ruwa da tsaki kuma masu alhakin sasanci a cikin jam’iyya.
Muna roƙonku da ku ji tsoron Allah (SWT), ku yi adalci, ku kuma guji son zuciya a dukkanin matakan zaɓen ‘yan takara. domin dukkan ku amana ce da Mai Girma Gwamna ya baku, Lallai amanar da aka ɗora muku babba ce, kuma nauyin talakawa yana kan kafaɗunku.
Ku zaɓo mana ‘yan takarar da suke da nagarta, mutunci, da karɓuwa a wurin jama’a—waɗanda ba za su jefa mu cikin wahalar tallata su ba, sai dai su zama abin alfahari ga jam’iyya da al’umma baki ɗaya.
Ku sani cewa:
Gwamna ya sanya ido akan ku,
Talakawa sun zuba ido suna jiran adalcinku.
Tarihi zai rubuta duk abin da kuka aikata.
Kuma Allah (SWT) yana kallonku a kowane lokaci.
Idan kuka yi son zuciya ko kuka fifita anfani na kanku, to lallai kun cutar da kanku da kuma al’ummar da kuke wakilta. Kuma ku sani cewa, sakamakon hakan ba zai tsaya a duniya kaɗai ba—Allah Mai adalci ba zai bar zalunci ba tare da sakamako ba.
Muna kira gare ku da ku tsaya tsayin daka wajen yin abin da ya dace, domin cigaban jam’iyya da kuma walwalar talakawa.
Allah ya shiryar da mu baki ɗaya, ya ba mu ikon yin abin da ya dace. Wannan tana a matsayin nasiha a garemu baki ɗaya, muna kyautata maku zato 100% domin tabbas akwai da ran zakuyi abinda ya dace, Allah ya shiga lamurran ku ya qara haɗa mana kawunan ku domin zaƙulo mana ayyukan alkhairi a Matazu dama ƙasa baki ɗaya.
Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 10/04/2026


A yau Juma’a, 10-04-2026 Mai Girma Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu, Hon. Shamsudeen Muhammad Sayaya (Ruwa Baba, Sarkin Yakin Matazu na II), ya jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa garin Malumfashi domin jajanta wa iyalan marigayi jami’in ɗan sanda, Suleman, wanda ya rasa ransa sakamakon harin ‘yan bindiga. Wannan ziyara ta nuna alhini da tausayi ga iyalan mamacin tare da nuna goyon baya a wannan lokaci na jimami.
A yayin ziyarar, shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana matuƙar alhininsa kan wannan rashi mai raɗaɗi, yana mai cewa rasuwar marigayin babban gibi ne ba ga iyalansa kaɗai ba, har ma ga al’umma baki ɗaya, ganin irin gudummawar da yake bayarwa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalai da abokan arzikin mamacin, tare da addu’ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan ƙaddara.
Mun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki, cikin ikonSa da rahamarSa mara iyaka, Ya jikanci marigayi Suleman, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya bai wa iyalansa, ‘yan uwansa, da dukkan al’ummar da wannan rashi ya shafa haƙuri, juriyar zuciya, da imani mai ƙarfi wajen jure wannan babban rashi. Amin Ya Rabbal Alamin.
✍️ Secretary Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Photos from Apc Youth Political Awareness Forum Matazu's post 10/04/2026

.
yau jumu'a 10-04-2026 an gudanar da wani muhimmin taro a garin Matazu, hedikwatar ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina, domin ƙaddamar da rabon motoci ga mutanen garin Sayaya da s**a rasa motocinsu sakamakon harin da ‘yan bindiga s**a kai musu a baya. Wannan tallafi ya samu ne ta hannun ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Musawa da Matazu, wanda ya samar da motocin domin rage raɗaɗin asarar da waɗanda abin ya shafa s**a yi.
A jawabinsa yayin taron, shugaban ƙaramar hukumar Matazu ya bayyana cewa wannan mataki babban abin alheri ne da zai taimaka wajen dawo da martaba da kuma farfaɗo da harkokin rayuwar al’ummar Sayaya. Ya ce hare-haren ‘yan bindiga sun jawo asara mai yawa ga jama’a, musamman waɗanda aka ƙone wa motocinsu, saboda motocin su ne hanyar samun abinci da gudanar da sana’o’insu.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yaba matuƙa da ƙoƙarin ɗan majalisar Tarayyar, yana mai cewa wannan ya nuna kulawa da tausayi ga al’ummar da yake wakilta. Haka kuma, ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni da shugabanni da su riƙa tallafawa al’umma musamman a lokutan da suke cikin ƙunci.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a dukkan yankunan ƙaramar hukumar Matazu.
A ƙarshe, waɗanda s**a amfana da motocin sun nuna matuƙar farin ciki tare da godiya ga ɗan majalisar da shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan gagarumin taimako, suna masu addu’ar Allah ya saka musu da alheri.
✍️ Secretary Apc Youth Political Awareness Forum Matazu

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Matazu
Katsina
020