21/02/2026
Ibrahim Masari Solidarity Organization IMSO
Advancing the Renewed Hope Agenda through the office of H.E Ibrahim Masari, S.A Political Matters
21/02/2026
16/02/2026
Maitaimakama Shugaban Kasa kan harkokin Siyasa, Ibrahim Masari Ya Raka Shugaba Tinubu Ziyara Ta Kwana Daya Domin Kaddamar Da Manyan Ayyuka a
Yola, Jihar Adamawa.
Mai Girma, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Al’amuran Siyasa da sauran Ayyukan yau da kullum, yabi sahun Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) a wata ziyarar aiki ta kwana guda zuwa birnin Yola na Jihar Adamawa.
A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya kaddamar da muhimman ayyuka da dama wadanda Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri ya aiwatar. Wadannan ayyuka, sunshafi sassa daban-daban da s**a hada da samar da ababen more rayuwa, kyautata ayyukan gwamnati, an tsara su ne domin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar Jihar Adamawa.
Taron ya samu halartar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaron Kasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, da gwamnoni, manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi, shugabannin siyasa, da sauran manyan baki.
Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwamnatin Jihar Adamawa bisa jajircewarta wajen kawo sauye-sauyen ci gaba, sannan ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin tarayya na karfafa hadin gwiwa da gwamnatin jihohi domin ciyar da tsarin "Renewed Hope Agenda" (Sabuwar Akidar Fatan Alheri) gaba.
Haka kuma Alh Ibrahim Masari ya nanata kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da kwanciyar hankali a fagen Siyasa, hadin kan kasa, da shugabanci na kowa-da-kowa a matsayin muhimman ginshikan samar da ci gaba mai dorewa a fadin Najeriya.
16 ga Fabrairu, 2026
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)
15/02/2026
Muna alfahari da maraba da ku zuwa wannan dandali da aka ware domin bayyana harkokin siyasa da rawar da Mai Girma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Harkokin Siyasa da Sauransu ke takawa.
A karkashin jagorancin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu (GCFR), Nijeriya na tafiya kan sabuwar turbar sauyi ta Ajandar Renewed Hope. Alhaji Ibrahim Kabir Masari na daga cikin manyan ginshiƙan wannan manufa, inda yake aiki tukuru wajen ƙarfafa jam’iyyar APC, haɗa kai tsakanin fadar shugaban ƙasa, jam’iyya da talakawa, da kuma tallafa wa manufofin da ke kawo ci gaban tattalin arziki, tsaro da jin daɗin al’umma.
An bude wannan shafi ne domin ya zama cibiyar bayanai, inda za a rika wallafa sabbin labarai kan ayyukan Alhaji Ibrahim Masari, bayanai kan muhimman harkokin APC a matakin ƙasa, da kuma yadda Ajandar Renewed Hope ke shafar rayuwar ’yan Nijeriya kai tsaye.
Muna gayyatar ’yan jam’iyya, ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa da duk masu goyon bayan ci-gaba da su biyo mu, tare da haɗa kai wajen gina Nijeriya mai wadata, adalci da ci-gaba.
Mungode:
Founder: Hon. Jamilu Mukhtar Kankara
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)
14/02/2026
We are proud to welcome you to the official platform dedicated to highlighting the political activities and strategic contributions of H.E Ibrahim Kabir Masari, Senior Special Assistant to the President on Political and Other Matters.
Our Mission: Under the visionary leadership of President Bola Ahmed Tinubu (GCFR), Nigeria is on a transformative journey through the Renewed Hope Agenda. H.E Masari stands as a key pillar in this mission, working tirelessly to:
Strengthen the APC: Ensuring our party remains a united, formidable force for national progress.
Political Synergy: Building bridges between the Presidency, the party, and the grassroots to ensure no Nigerian is left behind.
Deliver Renewed Hope: Supporting the implementation of policies that drive economic growth, national security, and social investment.
Why This Page?
Governance is a collective responsibility. This organization serves as a hub for:
- Real-time updates on H.E. Masari’s official engagements.
- Insights into APC national activities and strategic milestones.
- Deep-dives into how the Renewed Hope Agenda is changing lives across the Federation.
We invite all party faithful, patriotic Nigerians, and supporters of progress to join us as we document the journey toward a more prosperous Nigeria.
Follow us, share our updates, and let’s build together!
Founder: Hon. Jamilu Mukhtar Kankara
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Katsina
820101
